Real Madrid na zawarcin Rodri, Bayern na neman Stones

Asalin hoton, Getty Images
Ficewar Pep Guardiola daga Manchester City ta bude kofa ga ɗan wasan tsakiyar Spain Rodri mai shekara 29 ya koma Real Madrid a wannan bazarar. (Marca)
Bayern Munich na tunanin zawarcin ɗan wasan bayan Ingila John Stones mai shekara 31 a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Mail)
Atletico Madrid na nazarin yiwuwar zawarcin ɗan wasan Manchester City ɗan ƙasar Portugal Bernardo Silva, mai shekara 31, da kuma ɗan wasan bayan Chelsea ɗan ƙasar Spain, Marc Cucurella, mai shekara 27. (Sky Sports)
Inter Miami na dab da ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Manchester United Casemiro ɗan ƙasar Brazil, mai shekara 34, zai bar ƙungiyar a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Athletic)
Golan Liverpool, Alisson mai shekara 33, yana son ya koma Juventus a bazara ko da kuwa ƙungiyar ta Serie A ta gaza samun gurbi a gasar zakarun Turai ta baɗi. (Gazzetta)
Barcelona ta amince da yarjejeniyar fatar baki da ɗan wasan gaban Ingila Marcus Rashford mai shekara 28, yayin da take neman mayar da zaman aron da ya ke yi zuwa na dindindin, amma har yanzu ba su amince da kuɗin siyan ɗan wasan da Manchester United ba. (Sport)
Liverpool ta nuna sha'awa kan ɗan wasan gaban Hoffenheim, Bazoumana Toure, mai shekara 20, amma ta na fuskantar hamayya daga Manchester United da Aston Villa da Newcastle waɗanda suma suna zawarcin ɗan wasan na Ivory Coast. (TeamTalk)
Manchester United na sanya ido kan ɗan wasan bayan Borussia Dortmund Julian Ryerson, mai shekara 28, inda ta ayyana ɗan wasan na Norway a matsayin wanda zai maye gurbin Noussair Mazraoui. (Sky Sports Germany)
Manchester United za ta iya cin gajiyar rigimar Spygate da Southampton ke fuskanta ta hanyar zawarcin ɗan wasan tsakiyar Ireland mai shekara 22 Shea Charles. (Mirror)
Liverpool na iya yunƙurin ɗauko ɗan wasan Norway Antonio Nusa, mai shekara 21, idan har ta kasa cimma yarjejeniya kan abokin wasansa na RB Leipzig Yan Diomande. (Football Insider)
Fenerbahce ta fito a matsayin mai fafutukar siyan ɗan wasan gaban Masar Mohamed Salah mai shekara 33 daga Liverpool a bazarar nan. (Caught Offside)
Chelsea na duba yiwuwar zawarcin ɗan wasan Bayer Leverkusen Edmond Tapsoba, mai shekara 27, inda ɗan wasan na Burkina Faso ya taɓa yin aiki a ƙarƙashin koci mai jiran gado Xabi Alonso. (Teamtalk)
Da wuya Borussia Dortmund ta dawo da ɗan wasan gaban Manchester United Jadon Sancho ɗan ƙasar Ingila mai shekara 26, wanda ke zaman aro a Aston Villa. (Bild)











