Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Atletico Madrid na harin Salah, Arsenal na zawarcin Bissaka
Tottenham na shirin gwada ƙudurin Bournemouth kan tayin fam miliyan 85da ta yi mata domin ɗaukar ɗan wasan gaba na Faransa, Eli Junior Kroupi, duk da cewa ƙungiyar ta Cherries ta dage da cewa matashin mai shekara 20 ba na sayarwa ba ne.(Talksport)
Atletico Madrid na neman maye gurbin Antoine Griezmann da tsohon shahararen dan wasan Liverpool, Mohamed Salah, mai shekara 33, wanda a halin yanzu yake tare da tawagar Masar a gasar Kofin Duniya.(Fichajes )
Arsenal ta sa ɗan wasan West Ham da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Aaron Wan-Bissaka, mai shekara 28, a cikin jerin 'yan wasan da take zawarci domin maye gurbin Ben White, idan ɗan wasan na Ingila ya bar ƙungiyar a wannan bazarar.(Teamtalk)
Liverpool ta bi sahun Chelsea da Manchester United a zawarcin ɗan wasan West Ham da Netherlands, Crysencio Summerville, mai shekara 24. (Caught Offside)
Daya daga cikin muhimman ayyukan farko da Andoni Iraola zai fara yi a matsayin kocin Liverpool shi ne dakile sha'awar da ake nuna wa matashin ɗan wasan tsakiya na ƙasar Mexico, Gilberto Mora, mai shekara 17, daga Manchester United da kuma wasu ƙungiyoyin Turai. Mora na buga wa Club Tijuana wasa a gasar cikin gida ta Mexico.(Teamtalk)
Chelsea na shirin bai wa matashin ɗan wasan Ingila na ƙasa da shekara 19, Jesse Derry, mai shekara 19, sabon kwantiragi domin dakile sha'awar da Bayern Munich ke nuna masa (Football Insider)
Wolves na zawarcin ɗan wasan Hajduk Split Niko Sigur, mai shekara 22 bayan ya taka wa ƙasar Croatia leda a gasar Kofin Duniya.(Sky Sports)
Watakila dan wasan Sifaniya, Dani Carvajal, mai shekara 34, ya koma Deportivo La Coruna, ƙungiyar da ta koma matakin babbar gasa, bayan ya raba gari da Real Madrid. (Fichajes - in Spanish)