Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin dattawa ne suka mamaye siyasar Najeriya?
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Duk da cewa matasa su ne mafi rinjayen al'umma a Najeriya, har yanzu dattawan da suka haura shekaru 45 a duniya kuma suka daɗe suna taka rawa a harkokin mulkin ƙasar ke ci gaba da riƙe manyan muƙaman siyasa.
Yawancin waɗanda suka daɗe ana damawa da su sun riƙe muƙamai ne tun suna matasa, amma yanzu ana ganin sun ƙi ba matasa dama. A shekarar 2018, matasa sun yi ta fafutukar ganin an samar da dokar "Not Too Young To Run" da za ta ba matasan damar riƙe manyan muƙaman siyasa.
Sai dai ana ci gaba da muhawara kan adadin shekarun da ya kamata a ƙayyade na matasa, inda wasu ke ganin duk mutumin da ya zarta shekaru 35 ya wuce shekarun da za a kira shi da" matashi" yayin da wasu ke cewa shekaru 40.
Wasu daga cikin dattawan da aka daɗe ana damawa su sun yi gwamnoni, ministoci, sanatoci na tsawon shekaru, lamarin da ya sa ake ganin tsarin da ake tafiya a kai ya taƙaita damar sabbin jini shiga harkokin shugabanci.
Wannan ya sa ake ci gaba da tambayar ko siyasar Najeriya na bai wa matasa damar hawa manyan madafun iko, ko kuwa dattawan ne za su ci gaba da jan zarensu a shekaru masu zuwa, idan aka yi la'akari da waɗanda suke kai yanzu?
Shekarun Tinubu da mataimakinsa Shettima
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, na da shekaru 74 a duniya. An haife shi ne a ranar 29 ga Maris, 1952.
Kafin hawansa kujerar shugaban ƙasa a shekarar 2023, Tinubu ya yi gwamnan Jihar Legas daga 1999 zuwa 2007, inda daga bisani ya zama Sanata kuma ya kasance ɗaya daga cikin fitattun masu tasiri a siyasar Najeriya tsawon shekaru.
Mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima, kuwa an haife shi a ranar 2 ga Satumba, 1966. A yanzu yana da shekaru 59 a duniya.
Kafin zama mataimakin shugaban ƙasa, Shettima ya yi gwamnan jihar Borno na wa'adi biyu tsakanin 2011 da 2019, sannan ya wakilci Borno ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.
Duk da cewa shekarunsa ba su kai na shugaban ƙasar ba, shi ma ya shafe shekaru ana damawa da shi a siyasar Najeriya.
Tinubu ya girmi duk gwamnonin Najeriya
Gwamnan jihar da ya fi ƙarancin shekaru a Najeriya a halin yanzu shi ne Usman Ahmed Ododo na Jihar Kogi, mai shekaru 48 a duniya.
A gefe guda kuma, gwamnonin da suka fi kowa shekaru su ne Bala Mohammed da Hope Uzodimma, waɗanda dukkansu ke da shekaru 67.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, yana da shekaru 74 a duniya, wanda ya sa ya fi kowane gwamna mai ci a yanzu shekaru. Tinubu ya girmi gwamnan da ya fi ƙarancin shekaru da shekara 26, sannan ya girmi gwamnonin da suka fi kowa shekaru da shekara bakwai.
Haka kuma akwai gwamnoni da dama da shekarunsu ke tsakanin shekaru 50 zuwa sama, ciki har da Seyi Makinde, Hyacinth Alia da Ahmadu Umaru Fintiri.
Wannan na nuna cewa shugabancin jihohin Najeriya na hannun gogaggun 'yan siyasa masu shekaru ne fiye da matasa.
Dattawan da ke jan ragamar Majalisar Tarayya
Idan aka duba manyan shugabannin Majalisar Tarayya ta 10, za a ga cewa mafi yawansu na da shekaru 60 zuwa sama.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, an haife shi ne a ranar 9 ga Disamba, 1952, wanda ke nufin yana da shekaru 73 a duniya. Kafin ya zama shugaban majalisar dattawa, ya taɓa zama gwamnan Akwa Ibom, ya kuma riƙe muƙamin minista da kuma Sanata.
A ɓangaren Majalisar Wakilai kuwa, kakakinta, Tajudeen Abbas, an haife shi a ranar 1 ga Oktoba, 1965, kuma yana da shekaru 60. Tun daga shekarar 2011 yake wakiltar mazaɓar Zaria a majalisar, kafin ya zama kakakin majalisar a 2023.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Michael Opeyemi Bamidele, an haife shi a ranar 29 ga Yuli, 1963. Yana da shekaru 62 a duniya kuma ya shafe shekaru da dama a harkokin siyasa da aikin lauya kafin ya zama ɗaya daga cikin manyan jagororin majalisar.
Haka kuma shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Julius Ihonvbere, an haife shi a ranar 25 ga Yuni, 1956, kuma yana da shekaru 70. Farfesa ne a fannin kimiyyar siyasa wanda ya daɗe yana taka rawa a gwamnati da siyasa.
Shekarun ƴan siyasar da ke takarar shugaban ƙasa
Idan aka duba fitattun 'yan siyasar da ake hasashen za su fafata a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa, mafi yawansu suna tsakanin masu shekaru 60 zuwa 80.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya daɗe yana neman shugabancin ƙasa, an haife shi a ranar 25 ga Nuwamba, 1946. A halin yanzu yana da shekaru 79 a duniya.
A hukumance, Atiku wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar adawa ta ADC a zaɓen 2027, ya girmi shugaba mai ci Bola Tinubu, kuma yana daga cikin fitattun 'yan siyasar da suka fi kowa shekaru a sahun masu neman shugabanci.
Shi kuwa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC a zaɓen 2027, an haife shi a ranar 19 ga Yuli, 1961. Yana da shekaru 64 a duniya kuma yana daga cikin 'yan siyasar da matasa da dama ke kallo a matsayin wanda zai iya ba su dama, duk da cewa shi ma ya shafe shekaru masu yawa a harkokin siyasa da kasuwanci.
A ɓangaren ƙananan jam'iyyu kuwa, tsohon gwamnan Cross River, Donald Duke, shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PRP, an haife shi a ranar 30 ga Satumba, 1961. Yana da shekaru 65 a duniya.
Gwamnan jihar Oyo mai ci a yanzu, Seyi Makinde, ya fito takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APM. Bayan taron gangami na jam'iyyar, mambobin APM sun amince da shi a matsayin ɗan takararsu na shugaban ƙasa don tunkarar zaɓen 2027.
Yana da shekaru 58 a duniya. An haife shi ne a ranar 25 ga watan Disamba, 1967.
Ita kuwa jam'iyyar PDP da ke fuskantar rikicin shugabanci a ɓangarori daban-daban, ɓangaren Turaki ya amince da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a matsayin ɗan takararsu, yayin da ɓangaren da ke samun goyon bayan ministan Abuja Nyesom Wike ya amince da Sanata Sandy Onor.
Jonathan tsohon shugaban Najeriya ne daga 2010 zuwa 2015. Yana da shekaru 68.
Shekarun Gwamnonin Najeriya
A yadda alƙaluma suka nuna a watan Maris 2026, Gwamna mafi ƙarancin shekaru shi ne Usman Ahmed Ododo na jihar Kogi mai shekaru 48. Gwamnonin da suka fi kowa shekaru su ne Bala Mohammed na jihar Bauchi mai shekaru 67 da Hope Uzodinma na jihar Imo shi ma mai shekaru 67.
Ga jerin gwamnoni da shekarunsu.
Abia: Alex Otti – 61
Adamawa: Ahmadu Umaru Fintiri – 58
Akwa Ibom: Umo Eno – 62
Anambra: Charles Soludo – 65
Bayelsa: Douye Diri – 66
Benue: Hyacinth Alia – 60
Borno: Babagana Zulum – 56
Cross River: Bassey Otu – 66
Delta: Sheriff Oborevwori – 62
Ebonyi: Francis Nwifuru – 51
Edo: Monday Okpebholo – 55
Ekiti: Biodun Oyebanji – 58
Enugu: Peter Mbah – 54
Gombe: Muhammad Inuwa Yahaya – 64
Jigawa: Umar Namadi – 63
Kaduna: Uba Sani – 55
Kano: Abba Kabir Yusuf – 63
Katsina: Dikko Umaru Radda – 56
Kebbi: Nasir Idris – 60
Kwara: AbdulRahman AbdulRazaq – 66
Lagos: Babajide Sanwo-Olu – 60
Nasarawa: Abdullahi Sule – 66
Niger: Mohammed Umar Bago – 52
Ogun: Dapo Abiodun – 66
Ondo: Lucky Aiyedatiwa – 61
Osun: Ademola Adeleke – 66
Oyo: Seyi Makinde – 58
Plateau: Caleb Mutfwang – 61
Rivers: Siminalayi Fubara – 51
Sokoto: Ahmad Aliyu – 56
Taraba: Agbu Kefas – 55
Yobe: Mai Mala Buni – 58
Zamfara: Dauda Lawal – 60
Ƴan siyasar Najeriya da suka daɗe suna jan zare tun daga 1999
Tun daga lokacin da Najeriya ta koma mulkin dimokuraɗiyya a ranar 29 ga Mayu wato a Jamhuriya ta Huɗu a 1999, akwai wasu ƴansiyasa da suke kan ƙadamin mulki har zuwa yanzu ba a daina yi da su ba.
Jamhuriya ta Huɗu ta ƙyanƙyashe ƴansiyasa da dama, wasu sabon yanka ne, wasu kuma jamhuriyar ta gaje su ne daga Jamhuriya ta Biyu da ta Uku.
Sai dai wasu sun yi fice na ɗan lokaci kafin su ɓace daga fagen siyasar. Yayin da wasu kuma suka kasance ana ci gaba da damawa a ɓangarori daban-daban na siyasa da mulki, kuma har yanzu ana damawa da su.
Sai dai yawanci sun kasance suna sauya jam'iyya ko ɓangare ko dai a siyasar ko a harkar mulki.
Yayin da ƙasar ke tunkarar wani sabon zaɓe, ga wasu daga cikin fitattun ƴan siyasar da suka kasance ana damawa da su tun daga 1999, kuma har yanzu ba su gajiya ba.
Bayan kusan shekaru 27 da fara Jamhuriya ta Huɗu, waɗannan mutane har yanzu suna daga cikin fitattun sunayen siyasar Najeriya. Wasu na mulki, wasu na adawa, wasu kuma suna taka rawa a bayan fage.