'Mun haɗa kuɗin fansa sama da miliyan 150 amma ba a sako ƴan'uwanmu ba'

Wasu mutane da dakarun sojin Najeriya suka ceto a jihar Borno

Asalin hoton, @HQNigerianArmy

Bayanan hoto, Wasu mutane da dakarun sojin Najeriya suka ceto a jihar Borno
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Kimanin wata biyar kenan bayan da ƴan bindiga suka dira a ƙauyen Woro na jihar Kwara, inda suka yi wa mutane ɗaya daga cikin kisan gilla mafi muni da aka gani a baya-bayan nan a Najeriya.

Ɓarnar da ƴan bindigar suka yi ta ƙazanta, lamarin da ya janyo hankalin ɗaukacin al'ummar Najeriya da ma masu sanya ido kan harkar tsaro a ƙasashen ƙetare.

Ƴan bindiga sama da 100 ne ɗauke da makamai suka kai harin a ƙauyuka biyu – Woro da Nuku – suka yi kashe-kashe, suka ƙona gidaje sannan suka tafi da wasu.

Mazauna yankin sun ce yanbindigar sun kashe mutum fiye da ɗari biyu da sittin, kuma suka yi awon gaba da mutum dari da saba'in da shida, baya ga kona gidaje fiye da talatin.

"Sun kashe yarana biyu, sun sace matata da yarana uku," in ji Umar Salihu, mai sarautar gargajiya na yankin.

Sai dai yayin da lokaci ke tafiya, kowace daƙiƙar agogo da ta wulga, tamkar ƙarin raɗaɗi ne a zukatan iyalan waɗanda aka tafi da nasu, kasancewar ba su san halin da suke ciki ba a inda suke cikin daji tare da mahara.

Abin ma ya fi zafi ganin cewa har an ceto wasu da aka sace daga baya a jihar Oyo mai maƙwaftaka, inda a yanzu mutunen Woro ke ganin tamkar hukumomi sun yi watsi da su.

xxx

Asalin hoton, Reuters

A kan haka ne ƙungiyoyin ci gaban al'ummar yankin suka ƙara ƙaimi wajen kiraye-kirayen da suke yi game da ceto mutanensu da ƴanbindigar suka sace tun a ranar 3 ga watan Fabrairun 2026.

Mutanen yankin sun gudanar da zanga-zangar lumana domin jaddada rokon a taimaka a kuɓutar da mutanen da aka sace, kamar yadda aka yi ƙoƙarin kubutar da malamai da ƴan makarantan da aka sace daga baya a jihar Oyo.

Sun ce mutanen da aka sace sun ƙunshi mata da yara ƙanana yayin da wasu matan ke ɗauke da ɗanyen goyo.

Alhaji Abdul Ibrahim, wani wanda aka sace mutum talatin da biyar, kuma aka kashe goma daga cikin danginsa ya shaida wa BBC cewa "Mun haɗa kuɗi miliyan 155 mun kai wa ƴanbindigar, amman ba su amsa kuɗin ba, sun ce sun yi masu kaɗan sai komawa muka yi da su."

"Babu abin da za mu iya yi wanda ya wuce mu kai kukan mu ga gwamnatin tarayya da ta jihar Kwara domin su taimake mu, saboda ba mu da labarinsu tun bayan sace su sau biyu muka yi magana da su," in ji shi.

Sai dai biyan kuɗin fansa domin karɓo wanda ake garkuwa da shi laifi ne a dokokin Najeriya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ibrahim ya ce ƴanbingar sun shaida masu cewa idan har gwamanti ba ta yi abin da ya dace ba za su auri wasu daga cikin ƴan mata masu kyau daga cikin wadanda suka sacen, "Sun yi barazanar kashe sauran bayan sun zaɓi waɗanda suke so."

Alhaji Sulaiman Bukata, Dan Sadaukin Kaiama, daya daga cikin shugabanni al'umma, ya ce har zanga-zangar lumana suka gudanar kwanan nan kan wannan batu.

"Ba a kula da mutanenmu ba, saboda bayan sace su ne aka ɗauke na Oyo, amman gashi har an ceto su, amman ba wani ƙoƙari da gwamnati ta yi kan mutanenmu."

Al'ummar yankin sun yi kira ga hukumomin gwamnati da masu zaman kansu da su taimaka su kai masu ɗauki domin ganin an kuɓutar da mutanensu.

Honarabul Sa'idu Baba Ahmed, mai wakiltar yankin a majalisar dokokin jihar ta Kwara, ya shaida wa BBC cewa ya damu matuƙa saboda jinkirin kubutar da wadanda aka sacen.

"Idan mun tuntuɓi gwamnati suna fada mana suna aiki a kai, sai dai har yanzu shiru babu wani labari, saboda haka muna roƙon gwamnatin tarayy da ta ji tausayin yara ƙanana da mata masu ciki da goyo.

xxx

Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin hare-haren yanbindiga kuma matsalar hare-haren ta fara ƙamari a jihar Kwara da ke tsakiyar Najeriya.

Ƙungiyoyin ƴanbindigar sun fi ƙarfi a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, baya ga mayakan Boko Haram da Iswap da suka addabi yankin arewa maso gabashi.

Akwai ƙungiyoyin mahara sama da 100 da suke aika-aikar, kamar kai hare-hare da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa da sauransu.

Masana sun ce ƙungiyoyin suna ƙara samun ƙarfi ne saboda talauci da rashin aikin yi, sannan sun fara ne da satar shanu da ƙananan rikice-rikice, kafin ayyukansu suka ta'azzara tare da faɗaɗa.

Abin da ya faru a Woro

'Yan bindiga fiye da 100 ɗauke da makamai, kuma sanye da kayan soji ne suka shiga ƙauyukan Woro da Nuku, waɗanda akasari Musulmi ne a ciki, da ke jihar Kwara kan babura - domin ɗaukar fansa.

''Sun zo da yawan su da sunan yaɗa addini, sai kuma daga bisani suka zaɓi kashe mutanenmu'', kamar yadda Abdalla Umar Usman, wani tsohon malami kuma mazaunin Woro ya shaida wa BBC, yana bayyana yadda aka kai harin, wanda ya yi sanadiyyar kashe mutum aƙalla 75.

An kai harin ne da yammaci kafin rana ta faɗi a ranar Talata, a yayin da mutanen ƙauyukan, waɗanda akasari manoma ne ke komawa gidajensu daga gonakin su inda suke noman doya da masara da kuma gero.

Mayaƙan sun tafi kai tsaye gidan wani basarake Umar Bio Salihu, saboda tun a baya sun aika masa wasiƙu suna neman izinin zuwa yin wa'azi kan abin da ake gani tsattsauran ra'ayin addinin Musulunci ne, sai dai al'ummar kauyukan sun ƙi amincewa.

Salihu ba ya gidansa na Woro a wannan lokacin, saboda haka sai suka ƙona gidansa tare da kashe ƴaƴansa biyu.

''An kashe yaran basaraken biyu, waɗanda ɗalibai ne da ke koyon aikin likitanci a gaban gidansu kafin a cinna wa gidan wuta,'' In ji Usman.

Daga nan sai ƴan bindigar suka ci gaba da kashe mutane har cikin dare.

''Sun kashe kowa. Lamarin ya yi muni,'' in ji Mohammed Dauda.

Ƙungiyar kare haƙƙin biladama ta Amnesty International ta ce an gano gawarwaki da hannayensu da ƙafafunsu a ɗaure, wasu an yanka maƙogwaronsu, wasu kuma an harbe su.

Da ƴan bindigar suka tafi da safiya, sun tafi da mata da yara 38, ciki har da sauran iyalin basaraken ƙauyen.

''Sun kashe ƴaƴana biyu, kuma sun yi garkuwa da matata da ƴarana uku,'' a cewar Salihu.

Ƴan bindigar na so mazauna ƙauyen su barranta daga gwamnatin Najeriya da kundin tsarin mulkinta, a maimakon hakan su bi koyarwarsu, a yunƙurinsu na kafa tasu gwamnatin a yankin.

Wannan ya ''saɓa wa koyarwar Qur'ani,'' in ji Salihu.