Ga alama ta fara ƙarewa Mourinho - Masu sharhi

Asalin hoton, Reuters
Masana harkar ƙwallon ƙafa na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan yadda abubuwa ke taɓarɓarewa Jose Mourinho a Tottenham.
Da farko Mourinho ya fara kakar ta bana da ƙafar dama inda har ma ya ɗare kan teburin Premier, amma daga baya lamura suka dagule.
A yanzu an doke Tottenham wasanni uku a jere, kuma wasanni uku kawai kungiyar ta lashe a cikin 12.
Halin da Mourinho ya samu kansa a yanzu ba shi da bambanci da wanda tsohon mai horar da yan wasan Mauricio Pochettino ya samu kansa a ƙungiyar, wanda yasa aka sallame shi aka kuma maye gurbinsa da Mourinho.
Tarihi ya nuna cewa Mourinho bai taba rashin nasarori a gida ba kamar zuwansa Tottenham.
Masana na ganin jinyar da Harry Kane ya riƙa zuwa duk da ƙwallayen da yake ci a lokacin da yake ƙalau ta taimaka wurin ja bayan da ƙungiyar ta samu, amma kuma ba zai zama dalilin da zai sa Tottenham ta lalace haka ba.

Asalin hoton, PA Media
Bugu da ƙari rashin Harry Kane ɗin ya shafi hazaƙar Son Heung-min, lura da yadda suka fahimci juna tare da riƙa taimakawa juna wurin cin ƙwallaye.
To amma kuma dawo da tsohon dan wasan gaban ƙungiyar Gareth Bale da Mourinho ya yi har yanzu bai yi wani tasiri ba, musamman a irin wannan lokaci da ƙungiyar ke fuskantar rashin nasara gida da waje.
Duk da haka Jose Mourinho ya kai Tottenham wasan ƙarshe a kofin Carabao, kuma zai buga wasan kusa da na ƙarshe a kofin ƙalubale na FA da kulob din Everton, to amma dole ne ya lalubo inda matsalar ƙungiyar take da ta haifar mata da koma baya a gasar Premier.
Idan har kuma aka cigaba da tafiya a haka, ko kuma Mourinho ya kasa doke West Brom a gida ranar Lahadi mai zuwa, to kuwa abinda zai iya biyo baya ba lalle ne ya zo masa da mamaki ba.











