Najeriya za ta nemi diyya kan kasuwanci da dukiyoyin ‘yan ƙasarta a Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Bayo Onanuga/X
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta nemi a biya diyya kan dukiyoyi da kasuwancin ‘yan ƙasarta da suka bari a Afirka ta Kudu yayin da ake dawo da su gida sakamakon hare-haren nuna kyamar baƙi.
Muƙaddashin babban jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu, Alexander Ajayi ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da ya yi da Gidan talabijin na Channels inda ya ce gwamnati ta fara tattara bayanai kan dukiyoyin da ‘yan kasar suka bari, domin tuntubar gwamnatin Afirka ta Kudu kan yadda za a biya diyya.
Ya ce an buƙaci ‘yan Najeriyan da ke dawowa su rubuta cikakken bayanin kadarorinsu da suka hada da kasuwanci da motoci da sauran dukiyoyi, yana mai cewa shirin ba zai tsaya ga dawo da su gida kawai ba, gwamnati na kuma da ƙudurin kare jarin ‘yan kasarta.
A gefe guda kuma, wasu karin ‘yan Najeriya 271 sun isa filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas, bayan kwaso su daga Afirka ta Kudu, inda suka gargaɗi sauran ‘yan kasa da su guji zuwa can, suna mai cewa yanayin tsaro ya ƙara taɓarɓarewa sakamakon hare-haren nuna kyamar baƙi.
A jiya ne dai wasu ‘yan Afirka ta Kudu suka gudanar da zanga-zangar kyamar baki bayan cikar wa’adin da aka ba ‘yan kasashen waje da ba su da takaddar zama a ƙasar su fice, lamarin da ya ƙara tayar da hankula a kasar.
















