WHO na nazarin yiwuwar amfani da allurar rigakafin Ebola a DR Congo
Hukumar lafiya ta duniya ta ce tana duba yiwuwar samar da allurar rigafi da maganin magance cutar Ebola domin taimakawa wajen shawo kan matsalar bazuwar cutar a Janhuriyyar Dimokradiyyar Kongo.
A yanzu dai babu wata allurar rigakafin cutar da aka amince da ita a hukumance.
Kwamitin bada agajin gaggawa na hukumar ya ce yana duba yiwuwar amfani da allurar rigakafi ta Ervebo da kuma allurar rigakafin da jami'ar Oxford ke ƙoƙarin samarwa nan da watanni uku masu zuwa.
Anyi amannar cewa cutar ta kashe mutane dari da talatin da tara daga cikin dari shida da suka kamu.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya kenan Tedros Ghebreyesus yake cewa muna tsammanin adadin wadanda suka kamu da wadanda suka mutu zai ci gaba da ƙaruwa idan aka yi la'akari da yadda cutar ta bazu kafin a gano barkewar cutar.