Babu sansanin ƴan ta'adda a Kudu maso Yammacin Najeriya - Sojoji

Asalin hoton, Olufemi Olatunbosun Oluyede/Facebook
Hedikwatar Tsaron Najeriya ta ce babu wata tabbatacciyar hujja da ke nuna cewa ’yan ta’adda sun kafa sansani na dindindin a yankin Kudu maso Yammacin ƙasar, duk da harin da aka kai a wasu makarantu a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo.
Babban hafsan tsaron ƙasa, Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya fitar a jiya ranar 19 ga Mayun 2026.
Janar Oluyede ya bayyana harin da aka kai makarantar Baptist da Community Grammar da kuma L.A. a matsayin mummunan aiki mara imani da ya girgiza zuƙatan ’yan Najeriya.
Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda abin ya shafa da gwamnatin jihar Oyo, tare da tabbatar da cewa rundunar sojin Najeriya za ta yi duk mai yiwuwa domin ceto mutanen da aka sace cikin aminci ba tare da wani sharaɗi ba.
Sanarwar ta ce a baya sojoji sun gudanar da manyan ayyukan kawar da masu aikata laifi a dajin Old Oyo National Park, inda suka lalata ƙarfin masu aikata miyagun laifuka a yankin.
Hedikwatar tsaron ta jaddada cewa binciken bayanan sirri da ake yi yanzu bai nuna akwai wata tsayayyar ƙungiyar ta’addanci da ta kafa sansani a dazukan yankin Kudu maso Yamma ba.
















