KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi a kan Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya na ranar 28/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar da Abdullahi Bello Diginza

  1. Ukraine na zargin Isra'ila da sayen ''hatsin sata'' daga yankunanta da Rasha ta mamaye

    Ukraine ta gayyaci jakadan Isra'ila a ƙasar, bayan da Kyiv ta zargi Isra'ilar da sayen abin da ta kira hatsin sata daga yankunan Ukraine da Rasha ta mamaye.

    Ministan harkokin wajen Ukraine Andrii Sybiha ya ce irin wannan sayayya na kawo cikas ga alaƙa mai kyau da ke tsakanin ƙasashen biyu.

    Ya ce jirgin ruwan dakon kaya na biyu ya isa Haifa, bayan na farkon ya kai hatsi yakin.

    Ministan harkokin wajen Isra'ila Gideon Sa'ar ya ce za a gudanar da bincike kan lamarin.

    Sai dai kuma ya yi gargaɗin cewa zargi ba shaida bane, inda ya ja hankalinsu kan gudanar da hulɗar diflomasiyya ta intanet ko kafafen yaɗa labarai.

  2. Dukkan jagororin Iran masu tsattsauran ra'ayi ne - Rubio

    Marco Rubio

    Asalin hoton, Getty Images

    A wata hira da ya yi da kafar talibijin ta Fox News, Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya yi ƙarin bayani game da halin da ake ciki a Iran, da kuma tsaikon da Amurka ke samu wajen cimma yarjejeniya da gwamnatin ƙasar.

    A tattauwnawar ta sa, Rubio ya bayyana jagororin Iran da cewa ‘’ Dukkaninsu masu tsatsauran ra’ayi ne, Amma akwai masu tsatsauran ra’ayin da sun san cewa dole za su tafiyar da alamuran kasa kuma dole su tabbatar tattalin arzikin kasar na tafiya yadda ya kamata. Sai dai addini ne abin da suka fi mayar da hankali kai''.

    Sai dai a cewarsa ‘abin takaici, ana iya cewa masu tsatsauran ra’ayi waɗanda ba sa ma duniya fatan alkhairi ne ke rike da wuyar kasar’’.

    Rubio ya kuma ce masu tsautsauran ra’ayin addinin ba wai kawai dakarun juyin juya halin Iran bane, har ma da shugaban Iran ɗin da majalisar sa.

    Ya kuma kara da cewa mutane kamar Fira ministan kasar da Shugaban ƙasar da Shugaban majalisa duk masu tsatsauran ra’ayi ne, amma kuma sun san cewa dole ne ƙasar ta samu tattalin arziki mai inganci, kuma dole ne yan ƙasar su ci abinci.

  3. Ƙungiyar ISIS ta ɗauki alhakin harin da ya hallaka mutum aƙalla 30 a jihar Adamawa

    dan bindiga

    Wasu ƴan bindiga sun kashe aƙalla mutane ashirin da tara a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun shiga wani filin wasan ƙwallon ƙafa ne inda jama’a ke taruwa, kana suka buɗe wuta kan mai uwa-da-wabi.

    Ofishin gwamnan jihar ya ce maharan sun shafe sa’o’i da dama suna harbin jama'a da ƙona gidaje, da babura da wuraren ibada.

    A shekarun baya-bayan nan, yankin ya sha fama da hare-hare daga kungiyoyin ‘yan daba na cikin gida da kuma masu alaka da ISIS.

    Wata sanarwa da kungiyar ta ISIS ta wallafa a shafinta, ta dauki alhakin kai harin.

    Rahotanni na cewa an tura jami’an soji da ƴan sanda zuwa yankin domin daƙile yiwuwar sake kai wani harin.

  4. Ana tuhumar mutumin da ya yi harbi a taron cin abinci da yunƙurin kashe Trump

    Cole Thomas

    Asalin hoton, SOCIALMEDIA

    Mutumin nan da ake tuhuma da yunƙurin kashe shugaban Amurka Donald Trump a wajen wata liyafar cin abincin dare ta masu aiko da rahotanni daga fadar White House ya gurfana a gaban kotu.

    Ana zargin Cole Thomas mai shekara 31 a duniya da kutsawa cikin taron a ranar Asabar, ɗauke da bindigogi da wukake.

    Taron, wanda aka gudanar a otal din Washington Hilton, ya samu halartar shugaban ƙasar da manyan jami’an gwamnatinsa.

    Wakilin BBC ya ce bayanan kotu sun nuna cewa mutumin ya kama ɗaki ne a Otal ɗin bayan ya taso tun daga birnin Los Angeles a jirgin ƙasa a makon da ya gabata.

    Ana sa ran wanda ake zargin zai sake gurfana a gaban kotu ranar Alhamis domin sauraron batun tsare shi.

    Yana iya fuskantar daurin rai da rai idan aka same shi da laifi.

  5. Ana ci gaba da aikin ceto bayan jiragen ƙasa biyu sun yi taho mu gama a Indonesia

    kokarin ceto mutane a cikin jirgi

    Asalin hoton, Kompas.com/Nurpini

    Masu aikin ceto a Indonesia na can na ta ƙokarin ceto waɗanda ke da sauran numfashi, bayan wani mummunan hatsarin jiragen kasa a kusa da babban birnin kasar, Jakarta.

    Adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa goma sha hudu, yayin da aƙalla mutane tamanin suka jikkata lokacin da jiragen suka yi taho mu gama a kusa da tashar Bekasi Timur.

    Hatsarin ya auku ne lokacin da wani jirgin ƙasa da ya yo tafiya mai nisa ya sauka daga layinsa, kana ya yi karo da wani jirgin kasa na fasinja da ke tsaye, bayan wata mota kirar tasi ta toshe masa hanya.

    Tsarin sufurin jiragen kasa da na motocin bas dai na cike da cikas a Indonesia, abun da ke yawan haifar da haɗurra.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bibiyarmu a shafinmu na BBC hausa kai tsaye barkanmu da safiyar yau Talata.

    Kamar dai yadda aka saba wannan shafi ne da zai kawo muku labarai na abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, da Najeriya da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance tare da mu, kuma za ku bibiye mu a shafukan mu na sada zumunta kamar Facebook, X, Instagram da kuma YouTube domin kallon bidiyo da tafka muhawara.