KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da kawo muku muhimman bayanan dangane da wainar da ake toyawa a Najeriya da sassan duniya na 22/05/2026

  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • wata mata
  • Ungozoma
  • BBC reporter
  • Wakilai
  • Nafiu Gombe
  • Fati Halidou
  • xxx
  • Zanga-zanga
  • Atiku Abubakar

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR da Nabeela Mukhtar Uba

  1. Ministocin ƙungiyar tsaro ta NATO na taro kan yaƙin Iran

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    A ranar Juma'ar nan ne ministocin harkokin wajen ƙungiyar tsaro ta NATO ke taro a ƙasar Sweden a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar takun saƙa a cikin ƙawancen sakamakon da yaƙin Amurka da Iran da kuma tasirinsa a duniya.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya shaida wa BBC cewa za a tattauna batun rage yawan sojojin Amurka a Turai.

    Ya ƙara da cewa shugaba Trump ya ji taƙaicin ƙasashen NATO saboda rashin goyon bayansu.

    Tun da farko, Mista Trump ya sanar da cewa zai tura dakaru dubu biyar zuwa Poland, makonni kadan bayan da Washington ta ce ta janye dubban sojoji daga Jamus.

    Ana kuma sa ran ministocin za su tattauna kan ci gaba da goyon bayan Ukraine a yakin da take yi da Rasha

  2. Ɗan majalisar jihar Kano mai wakiltar gwamna ya koma wurin Kwankwaso

    Rabi'u Musa Kwankwaso

    Asalin hoton, Kwankwaso/X

    Ɗan majalisar dokokin jihar Kano da ke wakiltar ƙaramar hukumar Gwale, wadda ita ce ƙaramar hukumar gwamnan Kano, Abdulmajid Isa Umar Mai Rigar Fata ya fice daga jam'iyyar APC zuwa ta NDC.

    A ranar Alhamis ne dai tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso wanda shi ne jagoran jam'iyyar NDC ya karɓi ɗan majalisar.

    Mai Riga ya sanar da sauya sheƙara tasa ne bayan gaza samun takarar yin tazarce a kujerar tasa a lokacin zaɓen fidda gwani da jam'iyyar APC ta gudanar, bisa zargin "rashin gaskiya da adalci".

    Ana dai ganin nan ba da jimawa ba za a yi ta samun masu sauya sheƙa sakamakon abubuwan da suka faru a jam'iyyu na zaɓen cikin gida.

    Da ma dai wata kotu a Abuja ta dakatar da wa'adin da hukumar zaɓe ta saka wa jam'iyyu dangane da ranakun rufe rijistar ƴaƴan jam'iyyu, wanda ake yi wa kallon shi ma zai ƙara bai wa ƴan siyasa damar ci gaba da sauya sheƙa.

  3. Da gaske Tinubu ya ce zai dakatar da shari'ar Musulunci a Najeriya?

    Tinubu

    Asalin hoton, Tinubu/Facebook

    Fadar shugaban Nijeriya ta musanta wani labari da ta ce na jabu ne, da ya yi zargin cewa Shugaba Bola Tinubu na yunƙurin yi wa tsarin mulkin Nijeriya gyaran fuska domin sauya sunan ƙasar da kuma rusa dokar shari'ar Musulunci.

    Ta ce labarin wanda aka wallafa ba tare da ambatar majiyarsa ba, wani ɓangare ne na "maƙarƙashiyar wasu ƴan siyasa da idonsu ya rufe a ƙoƙarinsu na haddasa ƙiyayya da janyo rikicin siyasa da tunzuri" gabanin babban zaɓen 2027.

    Labarin dai ya bayyana ne a shafukan sada zumunta a makonnin da suka gabata kuma ya sake bayyana a baya-baya nan.

  4. Cuba barazana ce ga tsaron Amurka - Marco Rubio

    Marco Rubio

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana cewa, Cuba barazana ce ga tsaron ƙasar Amurka, kuma ya yi gargaɗin cewa abu ne mai wuya a iya warware rikicin da ke tsakanin ƙasasehn biyu cikin lumana.

    Jami'an Cuba dai sun sha zargin Washington da ƙoƙarin nemo hujjar ɗaukar matakin soji a kan tsibirin.

    A ranar Laraba, Washington ta tuhumi tsohon shugaban Cuba Raul Castro da kisan kai sakamakon wani hari da aka kai shekara talatin da suka wuce.

    Amurka ta girke jiragen ruwan yaki a yankin Caribbean, kuma ta kwashe watanni da dama ta na killace tsibirin.

  5. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barka da safiyar ranar Juma'a da fatan kun wayi gari lafiya. Kamar kowace rana mun dawo domin ci gaba a inda muka tsaya a shafinmu na kai tsaye da ke kawo muku wainar da ake toyawa dangane da yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da ƙasar Iran.

    Har wayau, shafin yana kuma kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sauran sassan duniya.