Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 02/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Kotu ta tabbatar da David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar ADC

    A yau Alhamis, wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta tabbatar da shugabancin jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark.

    Kotun ta yi watsi da ƙarar da ɗan majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar, bisa rashin hujjoji masu gamsarwa.

    Da yake yanke hukunci, mai shari’a Musa Liman ya amince da buƙatun farko da jam’iyyar ADC da tsohon shugabanta Ralph Nwosu da Mark da sakataren jam’iyyar na ƙasa Rauf Aregbesola suka gabatar.

    Alƙalin kotun ya ce kotun ba ta da hurumin sauraren ƙarar saboda lamari ne da ya shafi harkokin cikin gida na jam’iyyar siyasa.

    Alƙali Liman ya kuma yanke hukuncin cewa Abejide ba shi da hurumin shari'a na shigar da ƙarar, bayan ya kasa nuna yadda aka take masa haƙƙoƙinsa sakamakon fitowar shugabannin jam'iyyar ADC na yanzu.

    Dangane da halascin bayyanar Mark da Aregbesola a matsayin shugabannin jam'iyyar, alƙali Liman ya ce sauyin shugabancin da aka samu daga Nwosu zuwa Mark bai saɓa wa kundin tsarin mulkin ADC ba.

    Daga bisani, mai shari'a Liman ya yanke hukuncin cewa Abejide ya biya kowanne daga cikin waɗanda ake ƙara kuɗin da ya kai Naira miliyan 2.

    Har ila yau, ya umurci lauyan Abejide da ya biya Naira miliyan 10 a matsayin kuɗaɗen shari'a, bisa tanade-tanaden Dokar zaɓe ta shekarar 2026.

  2. Indiya ta nemi WhatsApp ya jinkirta ƙaddamar da tsarin amfani da sunaye a manhajar

    Indiya ta nemi WhatsApp ya dakatar da fitar da wani sabon tsari wanda zai bai wa masu amfani da manhajar damar yin amfani da sunaye na musamman yayin da suka mu'amula da juna, tana mai cewa hakan na iya ƙara yawan zamba ta intanet ta hanyar leken asiri.

    Ana sa ran wannan tsarin - wanda zai bai wa mutane damar yin hira ba tare da bayyana lambobin wayarsu ba - zai fara aiki ga masu amfani da WhatsApp biliyan uku a faɗin duniya a cikin ƴan watanni masu zuwa.

    A cikin wata sanarwa dav ta fitar, WhatsApp ta ce wannan tsarin bai fara aiki ba halin yanzu kuma ta ɗauki wasu matakan tsaro, ciki har da adana sunayen wasu manyan mutane da ke amfani da manhajar domin daƙile matsalar kwaikwayon mutane da zamba ta intanet.

    Yayin da ta ke da masu amfani da WhatsApp sama da miliyan 850, Indiya ita ce babbar kasuwar manhajar, wadda ta ke mallakar kamfanin Meta da Mark Zuckerberg ke jagoranta.

    Wannan matakin na daya daga cikin a cikin jerin matakan da hukumomin Indiya suka ɗauka don kula da yadda kamfanonin fasaha na duniya ke gudanar da ayyukansu a kasar.

  3. Iran ta yi alla-wadai da barazanar da Isra'ila ta yi wa Khamenei.

    Wakilin Iran na dindindin a Majalisar ɗinkin duniya ya yi alla-wadai da barazanar da gwamnatin Isra'ila ta yi wa Iran a fili, a cikin wata wasika da ya aika wa Sakatare-Janar da kuma Shugaban Kwamitin Tsaro na majalisar ɗinkin duniya.

    A cikin wannan wasiƙar, Amir Saeed Iravani ya bayyana barazanar da Ministan Tsaron Isra'ila Israel Katz ya yi wa Mojtaba Khamenei a matsayin "shaida bayyananniya ta ta'addancin da gwamnati ke aiwatarwa da kuma keta dokokin Majalisar ɗinkin duniya a fili."

    Har ila yau, Mista Iravani ya rubuta cewa, furucin Mista Katz na cewa an yi niyyar kashe Mojtaba Khamenei wani ɓangare ne na "tsarin da Isra'ila ke bi na kashe manyan jami'an Iran, kuma shirun da kwamitin tsaro ya yi ya ƙara bai wa Isra'ila karfin gwiwar ci gaba da aikata laifukanta."

    Tun da farko dai, ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi ya yi martani kan kalaman ministan tsaron na Isra'ila, inda ya bayyana cewa duk wani barazana ga al'ummar Iran da shugabanninta za ta fuskanci "martani cikin gaggawa kuma mai ƙarfi," a matsayin.

    Ya ƙara da cewa shugaban Amurka ya yi alƙawarin taka wa Isra'ila birki, kuma ya ce idan Isra'ila ta kauce daga wannan tsari, Iran za ta ɗauki matakin mayar da martani.

  4. Firaministan Pakistan da tawagar gwamnatin India za su halarci jana'izar Ali Khamenei.

    Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ya sanar da cewa, Firaminista Shahbaz Sharif zai tafi Tehran domin halartar jana'izar tsohon jagoran addinin Iran, Ali Khamenei.

    Taher Andarabi ya shaida wa manema labarai cewa, Mista Sharif zai tafi Iran daga Türkiye daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Yuli kuma birnin Tehran ne zai zama wurin farko da zai fara zuwa.

    Ana ganin Pakistan a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu shiga tsakani a tattaunawar da ke gudana tsakanin Iran da Amurka.

    Har ila yau, India ta sanar da cewa Syed Atta Hasnain, Gwamnan jihar Bihar, da Pabitra Margarita, mataimakin ministan harkokin waje, za su wakilci ƙasar a wurin jana'izar.

    Ma'aikatar harkokin hajen India ta bayyana cewa tawagar za ta ziyarci Iran a ranar Juma'a, 3 ga watan Yuli.

    Za a fara jana'izar Ali Khamenei ne a ranar Asabar a Tehran, sannan ta kammala a ranar 8 ga watan Yuli inda za a binne shi a garinsu na Mashhad.

  5. Zanen 'Adire' zai maye gurbin Khaki a matsayin sabon tufafin NYSC - Minister

    Ministan ma'aikatar kula da ci gaban matasa ta Najeriya, Ayodele Olawande, ya tabbatar da cewa ɗaya daga cikin sauye-sauyen da aka amince da su a shirin hidimar ƙasa (NYSC) shi ne maye gurbin tufafin da maus hidimar ƙasa ke sanyawa na yau da kullum da zani na'in 'adire'.

    Yayin da yake magana a wani shiri na gidan talabijin ɗin Channels a ranar Alhamis, ministan ya bayyana cewa manufar wannan sauyi ita ce inganta masana'antu na cikin gida da kuma tabbatar da cewa kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa sun amfani tattalin arzikin Najeriya.

    Da yake amsa tambaya kan ko za a samar da sabbin kayan a cikin gida, Olawande ya ce: "Adire ne. Ana samar da Adire a Najeriya. Muna da su a jihar Ogun, muna da su a jihar Kwara, kuma muna da masaƙu. Ya kamata mu mayar da kuɗaɗenmu cikin ƙasar nan."

    Ministan ya kuma bayyana cewa, a ƙarƙashin tsarin sake fasalin shirin, za a ƙara tura masu hidimar ƙasa ta yadda zai yi daidai da fannonin da su ke da ƙwarewa a kai.

    Ya bayyana cewa za a tura waɗanda suka kammala karatun digiri a fannin ilimi zuwa makarantu, saɓannin yadda ake yi a baya inda ba a lakari da abin da matasan suka karanta a matakin digiri ba.

    Olawande ya kuma yi watsi da rahotannin da ke nuna cewa za a ƙori sojoji daga shirin na NYSC, yana mai bayyana irin waɗannan bayanai a matsayin rashin fahimta.

    Ya bayyana cewa yayin da farar hula zai jagoranci ayyukan hukumar da ke gudanar da tsarin, sojoji za su ci gaba da taka rawa a shirin, musamman wajen tabbatar da tsaron masu yi wa ƙasa hidima.

  6. Trump ya ce tattaunawa da Iran na tafiya yadda ya kamata.

    Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a ranar Laraba cewa al'amura na tafiya yadda ya kamata a tattaunawar da ake yi da Iran, kuma an samu matuƙar ci gaba a tarukan da aka yi a Qatar a cikin kwanakin nan.

    "Tsarin wargaza shirin nukiliyar Iran yana tafiya yadda ya kamata. Sun gudanar da tarurruka masu kyau," in ji Mista Trump ga manema labarai kafin ya tafi North Dakota.

    Iran ta ci gaba da jaddada yanayin zaman lafiya na shirin nukiliyarta.

    Donald Trump ya kuma ce: "Mun matsa musu matuƙa... amma muna da kyakkyawar fahimta da juna."

    Ana gudanar da tattaunawar da ba na kai-tsaye ba tsakanin Iran da Amurka a yau a Doha, wanda Qatar da Pakistan ke shiga tsakani.

  7. 'An ƙona gomman mutane da ransu a rikicin jihar Neja'

    Ƴan sanda sun bayyana cewa, an kashe aƘalla mutum 18 a jihar Neja, dake yankin Arewa ta tsakiyar Najeriya, sakamakon jerin hare-haren da ke da nasaba da dogon rikici tsakanin manoma da makiyaya.

    Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya ce jami’ai sun samu rahoto daga yankin Katako na ƙaramar hukumar Rafi cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Godoro a daren ranar Litinin.

    Ya ce an harbe wani matashi mai shekara 25 har lahira, lamarin da ya sa mambobin ƙungiyar sa-kai ta yankin suka tare hanya tare da kashe wani mutum mai shekaru 28 a matsayin ramuwar gayya.

    Ƴan sanda sun ce a wani lamari na daban a ranar Talata da daddare, an kona mutane 15 har lahira a wani gida mai ɗakuna biyu a Angwan-Baago kusa da ƙauyen Godoro, yayin da aka kashe wani mutum a wani wuri na daban, wanda ya kawo adadin mace-macen da aka tabbatar ya kai aƙalla 18.

    Duk da haka, majiyoyin yankin sun ce jimillar waɗanda suka mutu na iya kai wa 48 bayan jerin hare-hare da ramuwar gayya.

    Wani mazaunin yankin, Hamza Maisaje Kwana, ya ce "Ko da yake ba za mu iya tabbatar da ainihin adadin waɗanda abin ya shafa ba, kiyasinmu ya nuna cewa an kashe mutane 43," in ji shi.

    Ƴansakai ƙungiya ce wadda galibi ta kunshi Hausawa manoma a arewacin Najeriya.

    An kafa su ne a yankin don kare al'ummomi daga Ƴan fashin daji.

    Duk da haka, an kuma zarge su da aikata kisan kai da cin zarafi ga makiyaya Fulani ba bisa ƙa'ida ba.

    A na su ɓangaren kuma wasu Fulani makiyaya sun kafa nasu ƙungiyoyin.

    Tashe-tashen hankula makamantan wannan sun ja hankalin ƙasashen duniya a cikin ƴan shekarun nan, inda al'ummomi daban-daban ke zargin juna da kai hare-hare.

    An kashe dubban mutane a cikin shekaru da dama na rikice-rikicen ƙabila da addini masu sarƙaƙiya, galibi sun samo asali ne daga taƙaddama kan amfani da filaye tsakanin al'ummomin da galibi ke noma da kuma ƙungiyoyin makiyaya.

  8. Wani babban jami'in gwamnatin China zai halarci jana'izar Ali Khamenei.

    Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar China ta sanar a ranar Alhamis cewa, babban jakadan ƙasar He Wei, zai je Tehran domin halartar jana'izar tsohon shugaban Iran, Ali Khamenei.

    Shi ne mataimakin shugaban kwamitin dindindin na majalisar wakilan Jama'ar ƙasa, wato babbar majalisar dokoki ta ƙasar China.

    An kashe Ali Khamenei tare da wasu daga cikin ƴan uwansa a ranar farko ta harin da Amurka da Isra'ila suka kai kan Iran a ranar 21 ga watan Maris, 2026.

    An tsara gudanar da jana'izar Khamenei ne cikin kwanaki biyar.

    Dangane da shirye-shiryen da aka sanar, za a fara gudanar da jana'izar ne a ranar Asabar, 4 ga watan Yuli a birnin Tehran, sannan zai kammala a ranar 8 ga watan Yuli tare da binne Ali Khamenei a birnin Mashhad.

  9. Amurka da dawo da jigilar daloli zuwa Iraƙi

    Jaridar New York Times ta ruwaito a ranar Alhamis, cewa Amurka ta ci gaba jigilar daloli zuwa Iraki bayan dakatar da ayyukanta na watanni da dama.

    Jaridar dia ta alaƙanta bayanan da wasu mataimakan firaministan Iraƙi guda biyu.

    "An sake komawa aikin jigilar dalar Amurka zuwa Iraƙi," in ji Haider al-Abboudi, ɗaya daga cikin masu magana da yawun Firaministan Iraki, yayin da yake zantawa da jaridar.

    A cewar wannan rahoto, Mudhar Muhammad Saleh, mai bai wa Firaministan Iraƙi shawara kan harkokin kuɗi, shi ma ya tabbatar da hakan.

    A watan Afrilu, Amurka ta dakatar da jigilar kuɗin da suka kai dala miliyan 500 zuwa ƙasar,

    sannan ta dakatar da wasu daga cikin ayyukan haɗin gwiwar tsaro da ta ke yi da Baghdad.

    Manufar wannan mataki ita ce matsa wa gwamnatin Iraƙi lamba domin ta hana ayyukan ƙungiyoyin mayaƙa da Iran ke marawa baya a ƙasar.

  10. An yi wa karnuka aƙalla 400 kisan gilla

    Mazauna garin Hossana, a yankin Tsakiyar Habasha, sun ba da rahoton cewa an kashe ɗaruruwan karnuka bayan jerin hare-haren cizon kare da suka yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane a yankin.

    Mazauna da jami'ai sun ce kisan ya fara ne bayan mutuwar wasu yara uku sakamakon matsalolin da suka shafi cutar haukar karnuka.

    A cewar shaidun gani da ido, wakilan unguwa sun umurci mazauna yankin da su kashe karnukansu ba tare da la'akari da matsayinsu na rigakafi ba.

    An ruwaito cewa an tilasta wa masu gidaje su shake dabbobinsu da igiya ko kuma su lakaɗa musu duka har sai sun mutu.

    Waɗanda suka ƙi bin umarnin sun fuskanci tarar da ta kai dalar amurka 300.

    Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC ba tare da an ambaci sunansa ba cewa kisan ya fara ne bayan da wasu ƴan'uwa biyu suka mutu sakamakon cizon karnuka. "Duk da cewa an yi allurar riga-kafi, wakilan unguwa sun fara aikin kashe dukkan karnuka ba tare da la'akari da yanayin lafiyarsu ba, ko an yi musu allurar riga-kafi ko a'a.

    Wani shaida mai suna Alaazar Kebede, wanda likitan dabbobi ne, ya shaida wa BBC cewa, "Duk da cewa an riga an yi allurar rigakafi, wakilan unguwa sun fara yaƙin neman kawar da duk karnukan yankin. An umurci masu karnukan da su kashe dabbobinsu, kuma an kama waɗanda suka ƙi yin hakan. Muna hasashen cewa an kashe karnuka tsakanin 400 zuwa 450 a cikin 'kan kwanaki kaɗan."

    "Alaazar ya ƙara da cewa, "Mutane suna jan karnuka suna kashe su ta munanan hanyoyi. Wannan rashin ɗa'a ne kuma ba a yarda da shi ba a addinance, da al'adance, da kuma a fuskar doka.''

    Bidiyo ya nuna yadda masu karnukan ke ta sharɓa kuka yayin da ake kashe karnukansu.

  11. BBC ta gano wani mai safarar mutane da aka yanke wa hukunci a Faransa yana zaune a Birtaniya

    Wani bincike na BBC ya gano wani mai safarar mutane da aka yanke wa hukunci, wanda a da aka yi wa laƙabi da "ubangidan" sansanonin ƴan ci-rani na Faransa, yana zaune a Leicestershire kuma ana kyautata zaton yana neman mafaka yayin da yake aiki ba bisa ƙa'ida ba.

    An yanke wa Twana Jamal hukuncin ɗaurin shekara biyar a gidan yari a Faransa a shekarar 2016, inda hukumomi suka bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu safarar mutane da aka taba kamawa.

    Masu gabatar da ƙara sun ce ɗan Iraƙin, mai shekara 36 a lokacin, ya samu har zuwa £100,000 a mako guda saboda jigilar bakin haure ba bisa ƙa'ida ba zuwa ƙasashen Turai.

    Bayan samun wasu bayanai a kansa a cikin wannan shekarar, mun gano Jamal a ƙauyen Blaby kuma mun samu shaida yana aiki, yana tuƙa mota ba tare da lasisi ba kuma da alama yana amfani da sunan ƙarya.

    Kasancewar Jamal a Burtaniya ta haifar da damuwa sosai game da ko hukumomin kan iyaka da ke akwai suna da tasiri wajen gano masu neman mafaka waɗanda suka aikata manyan laifuka a ƙasashen waje.

  12. Aƙalla mutum 18 sun mutu bayan harin da Rasha ta ƙai babban birnin Ukraine

    Jami'ai sun ce dakarun Rasha sun kai wani mummunan harin makami mai linzami a babban birnin Ukraine Kyiv cikin dare, inda suka kashe aƙalla mutum 18.

    An kwashe mutane da dama daga gidajensu yayin da hare-haren suka girgiza gine-gine a faɗin birnin, sa'o'i bayan da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi gargaɗin cewa Rasha na shirin kai wani babban hari.

    Rahotanni na cewa yara na cikin akasarin waɗanda suka mutu, in ji Tymur Tkachenko, shugaban gwamnatin soji ta Kyiv.

    "Maƙiyan mu suna sake kai hari kan ungwannin mutane da gangan suna kashe fararen hula," in ji shi da sanyin safiyar Alhamis.

    Ma'aikatar Tsaro ta Rasha ta yi iƙirarin cewa ta kai hari kan cibiyoyin makamashi ne saboda hare-haren da Ukraine ta kai kwanan nan.

  13. Assalamu Alaikum!

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda muke kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.