An jinkirta aikin kwashe ƴan Ghana daga Afirka ta Kudu

Asalin hoton, GHANA HIGH COMMISSION IN SOUTH AFRICA
Ma'aikatar harkokin waje ta Ghana ta jinkirta tashin jirgin da aka tsara kwashe ƴan ƙasar da ke Afirka ta Kudu sakamakon ƙaruwar zanga-zangar ƙyamar baƙin haure a Afirka ta Kudun.
A wata sanarwa, ministan harkokin wajen Ghana Sam Okudzeto Ablakwa ya ce an ɗage shirin da wasu kwanaki saboda wasu dalilai.
Hakan na zuwa ne sakamakon wasu rahotanni daga kafafen yaɗa labarai a Afirka ta Kudu da ke cewa ɗan Ghana guda aka gani ya je inda jirgin zai kwashi ƴan ƙasar.
Ma'aikatar harkokin wajen Ghana ta ce 800 cikin jama'arta sun nuna sha'awar komawa gida, an samu ƙari ke nan daga 300 da aka samu a farkon makonnan.
Ta ƙara da cewa an jinkirta tashin jirgin ne saboda adadin mutanen da aka samu sun ƙaru.
Ma'aikatar ta kuma ce buƙatar a bi wasu ƙa'idoji na shari'a har da tantance fasinjoji na daga cikin dalilan da suka janyo tsaikon.
Sai dai babu ƙarin bayani kan mutum nawa ne cikin 800 ɗin za su fice daga Afirka ta Kudu kaancewar kafafen yaɗa labaran ƙasar na ruwaito cewa babu fasinjoji a filin jirgin saman.
Ana fargabar cewa zanga-zangar baya-bayan nan a sassan Afirka ta Kudu na iya janyo dawowar rikicin ƙyamar baƙi.
A 2019, aƙalla mutum 12 aka kashe sannan a 2008, baƙi 62 ne suka mutu a hare-haren da aka kai kan baƙi a sassan ƙasar.


















