Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Abdullahi Bello
Mutum huɗu sun mutu a harin ƴan bindiga a ƙauyen Gorau da ke Sokoto
Asalin hoton, Getty Images
A Najeriya, rundunar ’yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwar mutum huɗu sakamakon harin da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Gorau, da ke Ƙaramar Hukumar Goronyo.
Maharan sun kai harin ne ’yan kwanaki bayan da gwamnatin jihar ta tallafa wa iyalan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin kwale-kwale, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 60.
DSP Ahmad Rufa’i, kakakin ’yan sandan jihar Sokoto, ya tabbatar wa BBC faruwar harin, inda ya ce rundunar na ɗaukar matakan da suka dace.
Tinubu da gwamnoni sun kafa kwamitin lalubo hanyoyin rage tsadar sufuri
Asalin hoton, Ebenezer Adeniyan/FB
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya amince da kafa kwamitin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi domin aiwatar da matakan rage tsadar sufuri a faɗin ƙasar.
Tinubu ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da ƙungiyar gwamnonin Najeriya, inda ya ce gwamnonin sun ɗauki matakin rage kuɗin sufuri a jihohinsu, musamman ta hanyar amfani da motocin CNG da na lantarki.
A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya ce gwamnatin tarayya ma na zuba jari mai yawa wajen sauya tsarin makamashin sufuri, ciki har da shirin shugaban ƙasa na CNG, inda aka sauya motocin sama da 120,000 daga amfani da man fetur zuwa CNG.
Tinubu ya ce akwai kuma wasu kayan sauya motocin sama da 100,000 da ake shirin kammalawa, yayin da ake ci gaba da faɗaɗa cibiyoyin sauya motocin da wuraren da ake samun CNG a faɗin ƙasar.
Shugaban ya ce ya kuma bayar da umarnin ƙara samar da wasu tashoshin CNG 500 a faɗin ƙasar, baya ga 500 da aka riga aka ba da umarnin samarwa a farkon shekarar.
“Muna fatan daga ranar 1 ga Oktoba, ’yan Najeriya su fara cin moriyar wannan tanadi ta hanyar samun sauƙin kuɗin sufuri,” in ji Tinubu.
Tinubu ya ce gwamnati ta tarayya da jihohi sun amince da fara aiwatar da matakan nan take, domin tabbatar da cewa an samu raguwar kuɗin man fetur domin samun sauƙin kuɗin sufuri.
“Mun amince cewa idan man fetur ya yi arha, kuɗin sufuri ma ya kamata ya ragu,” in ji shi.
Ba mu fatan yin wata tattaunawa da Iran – Trump
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasarsa ba ta neman yin wata ganawa ko yin wata tattaunawa da Iran.
Trump ya bayyana hakan ne a fadar White House yayin da yake amsa tambayoyin ƴan jarida, bayan ya sanya hannu kan wata doka ta sauya sunan tafkin Ontario da ke tsakanin Amurka da Kanada zuwa “Tafkin Amurka”.
Trump ya ce: “Ba mu da wani abu da yawa da za mu ce game da Iran yanzu. Ba ma son yin magana da su, kuma ba ma son ganawa ko yin shawarwari da su.”
Ya kuma sake jaddada cewa Mashigar Hormuz a buɗe take, inda ya ce Amurka na barin jiragen ruwa da dama su ratsa mashigar.
Ya ce a kullum ana fitar da miliyoyin ganga na mai ta Mashigar Hormuz, kuma sauran ƙasashe sun san hakan.
Trump ya ƙara da cewa a wasu lokuta ana jin harbe-harbe a yankin, amma ya ce Amurka ta cire dukkan nakiyoyin da aka sanya a Mashigar Hormuz.
Ya ce Amurka na amfani da rundunar sararin samaniyarta, wato “Space Force”, wajen sa ido sosai kan yankin Tekun Fasha da kuma Mashigar Hormuz.
Ƴan sanda a Zambia sun ce sun kama jagoran adawa Brian Mundubile
Asalin hoton, Getty Images
Ƴan sanda a Zambia sun ce suna tsare da jagoran adawa, Brian Mundubile, wanda ya zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a wannan watan, bisa zargin cin amanar ƙasa.
An kama Mista Mundubile da abokin takararsa, Makebi Zulu, a safiyar ranar Alhamis, bayan da Shugaba Hakainde Hichilema ya matsa wa Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Lusaka lamba kan ta miƙa su ga jami'an tsaro.
Tun da farko, mutanen biyu sun nemi mafaka a ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya bayan jami'an tsaro sun kashe wani tsohon minista tare da kama wasu 'yan siyasa da dama a wani samame.
Mista Mundubile ya musanta zargin gwamnatin cewa jam'iyyarsa na shirin tayar da bore.
'Iran ta zartar da hukuncin kisa ga mutane sama da 500 a 2026'
Asalin hoton, Getty Images
Wata ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama da ke Norway ta ce Iran ta zartar da hukuncin kisa kan sama da mutane 500 tun farkon shekarar 2026.
Ƙungiyar Iran Human Rights ta ce aƙalla mutane 511 aka zartar da hukuncin kisa a Iran zuwa yanzu a shekarar nan, ciki har da aƙalla mutane 29 da aka ce suna da alaƙa da zanga-zangar adawa da gwamnati da aka gudanar a watan Janairu.
Daraktan ƙungiyar, Mahmood Amiry-Moghaddam, ya ce yayin da hankalin duniya ya karkata ga rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran, da kuma sake buɗe Mashigar Hormuz, ya bai wa gwamnatin Iran ƙarin damar ci gaba da zartar da hukuncin kisa.
Ƙungiyar ta kuma ce aƙalla mata 16 na cikin waɗanda aka kashe, yayin da wasu daga cikin waɗanda aka zartar wa hukuncin ke da alaƙa da ƙungiyoyin adawa da aka haramta.
Shugaban Hukumar kwallon Ƙafa ta Najeriya Ibrahim Gusau ya yi murabus
Shugaban Hukumar Kwallon Ƙafa ta Najeriya, NFF, Ibrahim Gusau ya yi murabus daga muƙamisa.
Gusau ya shaida haka ne a yau Alhamis a shedikwatar Hukumar Kwallon Kafa ta kasar a wani taron manema labarai.
An ta suka kan yadda tawagogin Najeriya na mata da maza suka gaza ƙoƙari a 'yan shekarun bayan nan, ciki har da gaza samun gurbi a gasar kofin duniya.
Rahotanni sun ce hukumomin Najeriya na bincike kan hukumar ta NFF game da yadda ta kashe wasu kuɗaɗe naira 17bn don biyan albashi da sauran hidimar ‘yan wasa.
A bangaren wasannin cikin gida kuma an yi zargin cewa alkalan wasa ba su samu kudadensu ba tun daga mako na 25 zuwa mako na 38, da dai sauran wasu korafe-korafe.
Sojojin Nepal na ci gaba da neman mutanen da suka yi ɓatan-dabo
Asalin hoton, Getty Images
Daruruwan sojojin Nepal da ma’aikatan agaji na ci gaba da aikin bincike a tsaunukan arewacin ƙasar, domin nemo mutanen da har yanzu ba a san inda suke ba, bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a yankin jiya.
Ana hasashen cewa mutane akalla dubu daya da dari uku ne suka bace a Nepal da kuma a tsallaken iyaka a yankin Tibet.
Fiye da mutum 350 ne aka tabbatar sun mutu zuwa yanzu, da dama daga cikinsu masu yawon buɗe ido ne da kuma masu aikin ibada.
Masana kimiyya na ganin cewa wata babbar ƙanƙara ce ta fado cikin koguna, lamarin da ya haddasa ambaliyar mai muni.
Jirage masu saukar ungulu na kai kayan agajin gaggawa zuwa gundumomin da ambaliyar ta fi shafa.
Wakilin BBC ya ce ambaliyar ta shafe manyan tituna da dama, wanda ya sa jami'an tsaro amfani da jirage wajen ceton mutane.
Sojojin Isra’ila sun ce sun kakkaɓo jirgin leƙen asirin Hezbollah a Lebanon
Sojojin Isra’ila sun ce sun kakkaɓo wani jirgi mara matuƙi na ƙungiyar Hezbollah a kudancin Lebanon.
Kakakin sojojin Isra’ila ya wallafa a shafin X cewa a daren jiya wasu jirage marasa matuƙi biyu sun kai hari kan dakarun Isra’ila da ke wani yanki da ke Ali al-Taher.
A cewar kakakin, sojojin Isra’ila sun kakkaɓo ɗaya daga cikin jiragen, yayin da ba a san halin da ɗayan yake ciki ba.
Isra’ila ta ce ba za ta bari Hezbollah ta “kai hare-hare kan sojojin rundunar tsaron Isra’ila” da ke yankin ba.
Meta zai taƙaita yadda matasan Amurka ke amfani da Facebook da Instagram
Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin Meta, wanda ya mallaki shafukan Facebook da Instagram, ya amince da ɗaukar matakan da za su takaita yadda matasa a Amurka ke amfani da shafukan a wani ɓangare na yarjejeniyar sulhu ta dala miliyan dubu 18 da ya kulla da wasu jihohin ƙasar da suka zarge shi da cutar da yara.
Wani alƙali a jihar California ya amince da yarjejeniyar, yana mai cewa za ta taimaka wajen magance illolin da ake dangantawa da kafafen sada zumunta.
Kodayake kamfanin na Meta ya musanta aikata wani laifi, amma ya ce zai ƙaddamar da tsauraran matakan tantance shekaru tare da sanya wa'adin ga tsawon lokacin da matasa za su riƙa amfani da shafukansa a kullum.
Meta ya kuma ce zai biya kashi ɗaya bisa uku na kuɗin sulhun ne kawai idan sauran manyan kafafen sada zumunta, ciki har da YouTube da TikTok, sun amince da irin waɗannan takunkumai.
Matakin na zuwa ne gabanin bahasin da shugaban kamfanin na Meta, Mark Zuckerberg, zai bayar kan batun. Tun da farko dai jihohin da suka shigar da ƙarar sun nemi a biya su diyya ta kusan dala miliyan dubu 200.
Trump ya tura yarjejeniyar nukiliya tsakanin Amurka da Saudiyya zuwa majalisa
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Donald Trump ta miƙa yarjejeniyar nukiliya ta lumana da Saudiyya ga majalisar dokokin Amurka domin nazari.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, za a bai wa Saudiyya damar tace uranium a matsayin wani ɓangare na shirinta na samar da makamashin nukiliya na farar hula. Sai dai wani jami’in gwamnatin Amurka ya shaida wa jaridar The Hill, wadda ke bibiyar harkokin majalisar dokokin Amurka, cewa har yanzu akwai wani sharaɗi da Trump ya ƙara bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar.
A cewar jami’in, matsayin Shugaba Trump bai sauya ba, kuma ba za a fara aiwatar da yarjejeniyar ba sai Saudiyya ta shiga Yarjejeniyar Abraham (Abraham Accords) tare da ƙulla dangantakar diflomasiyya da Isra’ila.
Yarjejeniyar ta kuma ƙara haifar da damuwa kan yiwuwar saurin ƙaruwar gasar mallakar makamashin nukiliya a Gabas ta Tsakiya.
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da Amurka ta sha bayyanawa a cikin shekarar da ta gabata cewa ɗaya daga cikin manyan manufofinta na kai hare-haren soji kan Iran shi ne hana ƙasar mallakar makaman nukiliya, tare da daƙile yiwuwar gasar makaman nukiliya a Gabas ta Tsakiya.
’Yansanda sun gayyaci VeryDarkMan kan zargin ba masu garkuwa bayanan matafiya
Asalin hoton, VDM Facebook
Rundunar ƴansandan Najeriya ta ƙalubalanci Vincent Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan (VDM), da ya gabatar da hujjojin da ke tabbatar da zargin da ya yi cewa wasu jami’an ’yansanda a shingayen bincike suna taimakon ƴanbindiga ta hanyar raba bayanan matafiya ga masu garkuwa da mutane.
VDM ya yi zargin cewa wasu jami’an ’yansanda da ke aiki a shingayen bincike a manyan hanyoyin ƙasa suna lura da matafiya masu hannu da shuni, sannan su bai wa masu garkuwa da mutane bayanansu da inda suke tafiya, lamarin da ke taimakawa wajen sace mutane domin neman kuɗin fansa.
Rundunar ta bayyana buƙatar shaidar ne a cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, CSP Ani Iniedu, ya sanya wa hannu, bayan kalaman da aka danganta wa VDM a taron ƙungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), wanda aka yi a birnin Fatakwal.
Rundunar ’yansandan ta ce ta ɗauki zargin da muhimmanci, wanda hakan ya sa ta ce tana neman gamsassun hujjoji, domin a cewarta ba za ta rumgume hannu tana kallo ana aiwatar da abubuwan da za su ɓata sunan hukumar da ke da alhakin kare miliyoyin ’yan ƙasar ba.
A cewar rundunar, zarge-zargen irin wannan girman suna buƙatar sahihan shaidu, inda ta jaddada cewa jami’an da aka tura shingayen bincike da sauran wurare a faɗin ƙasar an ba su umarnin hana aikata laifuka, gano masu aikata laifuka da kuma kare al’umma ne.
’Yan sandan sun kuma bayyana irin haɗarin da jami’ansu ke fuskanta, inda suka ce jami’an sukan yi arangama da irin waɗannan miyagu da ake zarginsu da haɗa baki da su, sannan ta nanata an sha yi wa jami’an ’yansanda da dama kwanton ɓauna, an kai musu hare-hare tare da kashe wasu daga cikinsu.
Rundunar ta ce: “Idan aka gano wani jami’i ya ci amanar aikinsa, zai fuskanci cikakken hukuncin ladabtarwa. Amma bai kamata a hukunta ko a yi Allah-wadai da wata hukuma baki ɗaya bisa wata sanarwa da aka yi a bainar jama’a ba tare da shaida ba.”
Daga bisani, rundunar ta gayyaci Otse da ya gabatar da duk wata shaida da yake da ita, ciki har da bayanan da ke goyon bayan zarginsa cewa jami’an shingayen bincike suna gano masu hannu da shuni tare da sanar da masu garkuwa da mutane inda suke.
Yadda mutanen Geidam ke zaman gida bayan harin ƴanbindiga
Asalin hoton, UGC
Rahotanni sun nuna cewa ƴanbindiga sun ƙaddamar da hare-hare a garin Geidam da ke jihar Yobe, lamarin da ya mutanen garin su koma gida suna zaman kulle.
Mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa a daren Laraba ne maharan suka kutsa garin, inda daga baya sojoji suka kai ɗauki, tare da yin musayar wuta da mayaƙan da ake kyautata zaton ƴan Boko Haram ne.
Asalin hoton, UGC
Asalin hoton, UGC
'Batun mashigar Hormuz ya fi na nukiliyar Iran muhimmanci a yanzu'
Asalin hoton, Reuters
Batun nukiliyar Iran ya zama abu na biyu mafi muhimmancin a yanzu a cewar daraktan hukumar makamashin nukiliya ta duniya (IAEA), Rafael Grossi.
Ya ce har sai an fayyace halin da ake ciki a game da mashigar Hormuz da sauran batutuwan da ke da alaƙa da shi kafin a koma batun nukiliya.
A wata hira da jaridar Argentina ta La Nación, Grossi ya ce an dakatar da tattaunawar da ake yi kan shirin nukiliyar Iran ne domin batun da ya fi shi muhimmanci.
Ya ce: “Har sai an fayyace babban batu na mashigar Hormuz da sauran batutuwan da suka shafi lamarin, batun nukiliyar ya zama na biyu.”
Grossi ya kuma bayyana cewa halin da fayil ɗin nukiliyar Iran ke ciki a yanzu ya samu tasiri daga sauye-sauyen da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma yaƙe-yaƙe.
’Yan Najeriya 67 sun koma gida daga Afirka ta Kudu
Asalin hoton, National Commission for Refugees, Migrants and Internally Displaced Persons (NCFRMI)
Hukumomin Najeriya sun ce ’yan ƙasar 67 sun koma gida daga Afirka ta Kudu a ƙarƙashin wani shirin mayar da ’yan ƙasa da wasu ’yan kasuwar Najeriya ke ɗaukar nauyin sa.
Mutanen sun isa filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a yammacin Laraba, a cikin jirgin kamfanin South African Airways, inda ta ce jami’an hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) da hukumar kula da ’yan gudun hijira, ’yan ci-rani da masu gudun Hijira a cikin gida (NCFRMI) ne suka tarbe su.
A cewar NCFRMI, waɗanda suka dawo sun ƙunshi manyan mutum 30, yara 36 da jariri guda ɗaya. Mai kula da shiyyar Kudu maso Yamma na hukumar, Alex Oturu, ya shaida wa BBC cewa wasu ’yan kasuwar Najeriya ne suka ɗauki nauyin aikin, ƙarƙashin jagorancin Ikem Ume-Ezeoke.
Ya ce kowa daga cikin waɗanda suka koma ya samu tallafin naira 50,000 ($32; £24), yayin da NEMA ta taimaka musu wajen ci gaba da tafiya zuwa garuruwansu a sassa daban-daban na Najeriya.
Wannan sabon aikin ya zo ne gabanin ranar ƙarshe ta 30 ga Satumba da wasu ƙungiyoyin da ke adawa da baƙin haure a Afirka ta Kudu suka sanya, inda suka yi kira ga ’yan ci-ranin da ba su da takardun izinin zama su bar ƙasar.
EFCC za ta ba wanda ya fallasa kuɗin sata da aka ɓoye a ƙasar waje kashi 5
Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK
Hukumar EFCC ta ce mutanen da suka bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gano dukiyar da aka wawure daga Najeriya tare da ɓoyewa a ƙasashen waje, na iya samun lada har zuwa kashi 5 cikin 100 na asalin dukiyar da aka ƙwato.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya yi kira ga mutanen da ke da sahihan bayanai kan inda aka boye kuɗaɗe da kadarorin Najeriya a ƙasashen waje da su fito su bayar da bayanan.
Ya yi wannan kiran ne yayin wani taro kan laifukan tattalin arziki da aka gudanar a Cambridge, Ingila, ina ya ce a ƙarƙashin tsarin ladar, mai fallasa bayanai (whistleblower) wanda bayanansa suka kai ga samun nasarar ƙwato dukiya, na iya samun lada tsakanin kashi 2.5 zuwa 5 cikin 100 na ƙimar dukiyar da aka ƙwato.
Da yake magana a taron, Olukoyede ya ce ya kamata a ƙara matakan kariya ga mutanen da ke bayar da bayanan da ke taimakawa wajen tona asirin laifukan kuɗi, inda ya nanata cewa kariyar na da muhimmanci, musamman a ƙasar da wasu masu bayar da bayanai ke fargabar ramuwar gayya bayan fallasa mutanen da ke da alaƙa da siyasa ko kuma masu tasiri a ƙasar.
Najeriya ta ƙaddamar da manufar kare masu fallasa bayanai ta gwamnatin tarayya a shekarar 2016, wadda ta tanadi lada ga mutanen da suka taimaka wajen fallasa almundahana, ɓoye ko karkatar da kuɗaɗen gwamnati da kadarorinta. Sai dai, duk da alkawarin bayar da lada, an taɓa nuna damuwa cewa wasu masu fallasa bayanai sun shafe lokaci suna jiran biyan kuɗaɗen da aka yi musu alkawari. Haka kuma, babu wata takamaiman doka da ke ba su cikakkiyar kariya.
Sai dai sabuwar sanarwar EFCC kan ladar ta haifar da tambayoyi kan ko hukumomi za su iya tabbatar da sirri, kariya da kuma biyan ladan kamar yadda aka yi alƙawari.
Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da dala biliyan 1 domin tallafa wa marasa ƙarfi
Asalin hoton, Federal Ministry of Information and National Orientation, Nigeria
Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da shirin HOPE-SP na dala biliyan 1 domin agaza wa marasa ƙarfi a ƙasar, inda ta ce shirin zai sauya yanayin tallafin da ake yi zuwa na ɓullo da hanyoyin dogaro da kai.
Shirin mai suna Household Prosperity and Economic Social Protection Project (HOPE-SP), an ƙiyasta zai ci dala biliyan 1, a wani mataki da ke nuna sauyin tsarin tallafin jinƙai daga bayar da tallafi na ɗan lokaci zuwa samar da hanyoyi da gwamnatin ta ce masu ɗorewa da za su taimaka wa jama’a su fita daga talauci.
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ce ta ƙaddamar da shirin a ranar Laraba, 26 ga Agusta, 2026, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ta yaba wa ministan harkokin jinƙai da rage talauci, Dr. Bernard Doro, da tawagarsa bisa ƙoƙarin da suke yi.
An tsara sauye-sauyen ne domin inganta yadda ake gano da tantance gidajen da ke cikin buƙata, da kuma tabbatar da cewa tallafi ya isa ga waɗanda suka fi cancanta. Haka kuma, za su ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin shirye-shiryen jinƙai da na rage talauci, tare da samar da tallafin gaggawa yayin fuskantar matsaloli da kuma ƙara gaskiya da riƙon amana.
Ministan ya ce ɗaya daga cikin muhimman abubuwan shirin shi ne One Humanitarian, One Poverty Response System (OHOPRS), wanda zai haɗa shirye-shiryen agaji, zamantakewa da rage talauci cikin tsari guda na ƙasa.
"Tsarin zai yi amfani da rajista guda, hanyoyin isar da tallafi na zamani, ingantaccen tsarin kuɗaɗe da bayanan sirri na zamani domin yanke shawara cikin gaggawa."
Babban Sakatare na Ma’aikatar, Olubunmi Olusanya, ya ce sauye-sauyen za su ƙarfafa haɗin gwiwa da riƙon amana, yana mai jaddada cewa babban ma’aunin nasara shi ne ganin sauyi na zahiri a rayuwar ‘yan Najeriya masu buƙata. Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, da sauran masu ruwa da tsaki, ciki har da Ministan Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi da Tattalin Arziki, Abubakar Bagudu, da abokan hulɗar kamar Tarayyar Turai da Bankin Duniya, sun yaba da ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na ƙarfafa tsarin ayyukan jin jinƙai a Najeriya.
Aƙalla mutum 177 sun mutu, sama da 800 sun ɓace a ambaliyar Nepal
Asalin hoton, Reuters
Rundunar sojin Nepal ta tura jami'ai kusan 2,000 domin taimaka wa aikin nemo mutanen da suka ɓace bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a arewacin ƙasar.
Wakiliyar BBC ta ce har yanzu tituna da hanyoyin sadarwa a toshe suke.
Rahotanni sun ce fiye da mutum 160 sun mutu a sakamakon ambaliyar, yayin da sama da 'yan yawon buɗe ido 600 ke cikin waɗanda har zuwa yanzu ba a san inda suke ba.
Sannan a iyakar da ke yankin Tibet na China kuwa, kafafen yaɗa labaran China sun ce mutum uku sun mutu, yayin da ake neman sama da wasu 500 da suka ɓace.
Hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa mai ƙarfi ya rika kwarara cikin yankunan da jama'a ke zaune, yayin da mutane ke gujewa zuwa saman tuddai domin tsira da rayukansu. Ambaliyar ta lalata ƙauyuka gaba ɗaya, tare da rusa hanyoyi, da gadoji da tashoshin samar da wutar lantarki.
Wanda ake zargi da harin 11 ga Satumba a Amurka, Khalid Sheikh zai bayyana a gaban kotu
Asalin hoton, HO/AFP via Getty Images
Bayanan hoto, Wannan hoto ne da aka ɗauka na Khalid Sheikh Mohammed a shekarar 2003 bayan an kama shi
Kafafen yaɗa labarai na Amurka sun ce wani alƙalin kotun soji ya yanke hukuncin cewa Khalid Sheikh Mohammed, wanda ake zargin shi ne jagoran shirya hare-haren 11 ga Satumba (9/11), zai gurfana a gaban kotu a watan Yunin shekarar 2028, fiye da shekara 25 bayan harin.
An kama Khalid Sheikh Mohammed a shekarar 2003, kuma tun daga shekarar 2006 ake tsare da shi a sansanin sojin ruwan Amurka da ke Guantanamo Bay a Cuba.
Ana zarginsa da tsara harin ta hanyar amfani da jiragen saman fasinja da aka yi garkuwa da su wajen kai hare-hare kan cibiyar kasuwanci ta duniya da kuma hedkwatar tsaron Amurka ta Pentagon a shekarar 2001.
Harin na 11 ga Satumba shi ne mafi muni da aka taɓa kai wa a ƙasar Amurka, inda ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 3,000.
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.