Abubuwa da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwa da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 04 ga watan Agustan 2026.

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • xxx
  • xxx
  • Bola Tinubu
  • Senator Gaya
  • xxx
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Usman Minjibir

  1. Fursunoni da yawa sun tsere daga gidan yari a Libya

    a

    'Yan sanda a Libya sun ce adadi mai yawa na fursunoni sun fasa wani gidan yari a wani gari da ke yamma da Tripoli, babban birnin ƙasar.

    Garin Sorman ya kuma fuskanci gwabza faɗa tsakanin mayaƙa masu riƙe da makamai da kuma jami'an tsaro, kamar yadda garin Zawiyya mai maƙwabtaka shi ma ya yi fama.

    'Yan sanda ba su bayyana yawan mutanen da suka kuɓuce daga gidan yarin Sorman ba.

    Suna dai gudanar da bincike a kan lamarin sannan sun ce an kafa wani kwamiti don tantance waɗanda lamarin ya shafa.

    Rikice-rikice a garuruwan biyu sun haddasa mutuwar aƙalla mutum uku, wasu kuma sun ji raunuka.

    Ba a iya fayyacewa ba zuwa yanzu, abin da ya haddasa lamarin.

  2. Paul Biya ya yi wa manyan hafsoshin sojin Kamaru garambawul

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Kamaru mai dogon zamani, Paul Biya ya yi wa manyan hafsoshin sojin ƙasar garambawul yayin da ake samun ƙaruwar raɗe-raɗi game da yanayin lafiyarsa da kuma inda yake.

    An yi sauye-sauyen ne ta hanyar dikirin shugaban ƙasa kafin a ba da sanarwa a gidan rediyon Kamaru. Tsawon wata biyu kenan, ba a ga dattijon mai shekara 93 a bainar jama'a ba.

    Gwamnatin Kamaru ta ce ya tafi Turai ne wani hutu na ƙashin kai, amma ba ta yi cikakken bayani ba, illa dai yana nan a raye kuma zai dawo nan ba da daɗewa ba.

    Shugaban mafi tsufa a duniya ya bar Kamaru ne ranar 7 ga watan Yuni don abin da aka bayyana da gajeriyar ziyara a Turai, sai dai yanzu ta zama tafiya mafi daɗewa a ƙetare da aka sani, tun bayan hawansa mulki a 1982.

    Jam'iyya mai mulki ta Kamaru ta yi wani taro da ba ta saba yi ba tsakanin manyan ƙusoshinta a watan jiya, daidai lokacin da suka ta ƙaru a kan rashin ganin shugaban ƙasar tsawon lokaci.

  3. Tinubu ya ƙara wa ƙananan sojoji albashi da kashi 80

    a

    Asalin hoton, Bayo

    Shugaban Najeriya Bola Ahemd Tinubu ya amince da ƙarin albashi da ya kai kashi 30 zuwa 80 ga dakarun sojojin Najeriya.

    Karin albashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Satumbar 2026, kamar yadda wata sanarwar daga fadar shugaban ƙasar ta bayyana.

    Sanarwar ta ce sojojin Najeriya aƙalla 250,000 ne ake tsammanin za su amfana da wannan sabon ƙarin albashi.

    Ƙarƙashin sabuwar sanarwar jami'an da suke daga matsayin kanar zuwa birgediya janar da manjo janar da laftanar janar da janar duka za su samu ƙarin kashi 30 ne cikin 100.

    Tun daga matsayi na ɗaya da ake kira laftanar na biyu da laftanar da manjo da zuwa laftarnar kanar za su samu ƙarin kashi 80 cikin 100 na ƙarin albashin.

    Yanzu ƙunshin albashin sojojin na shekara zai tashi daga naira biliyan 660 zuwa naira biliyan 924.

    Shigaba Tinubu yace an ɗauki matakin ne saboda cika alƙawarin gwamnatinsa na "kyautata rayuwar sojoji da suke yaƙi da matsalolin Najeriya irinsu ɓarayin daji, da masu satar mutane domin neman kuɗin fansa da 'yan ta'adda da suke a faɗin ƙasar".

  4. Ana samun ci gaba kan tattaunawar sake buɗe mashigar Hormuz – Rubio

    ,

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Sakataren harkokin wajen Amurka yace tattaunawa tsakanin Iran da Oman kan jiragen da suka maƙale a mashigar Hormuz, amma har yaznu ba kai game da cimma matsaya ba.

    “Ana samun ci gaba a tattaunawar da ake yi, amma gaskiya ba a kai ga ƙarshe ba. Amma muna fatan ganin hakan a kusa,” Marco Rubio ya bayyanawa maneman labarai.

    Tun da fari, sakataren baitin malin Amurka ya ce ana tattaunawa da Iran kuma ana sa ran za a cimma matsaya nan da gobe a sake buɗe mashigar Hurmoz.

    Jami’na Amurka suna ta nuna kwarin giwa kan wannan tattaunawa, a daidai lokacin da Iran da Oma suke tattaunawa kan nyadda za a riƙa tafiyar da mashigar idan an sake buɗe ta, sai dai Ita Iran tana ta musanta batun tattaunawarta da Amurkan.

    A gefe ɗaya kuma Qatar tace koƙarin da ake ta yi na masu shiga tsakiya don kawo ƙarshen rikicin Iran da Amurka na ci gaba – sai dai har yanzu ba a shirya wata tattaunawa ba ta kai tsaye tsakanin ɓangarorin biyu ba.

  5. Majalisar dokokin Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomi uku

    Kakakin majalisar dokokin Kano Ismail Falgore

    Asalin hoton, Sir Topshadow

    Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomi uku na tsawon watanni uku bisa zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati da amfani da ofis ba bisa ƙa'ida ba.

    Ciyamomin da aka dakatar su ne Bello Abdullahi Gadanya na Bagwai, Alhassan Salisu na Bebeji da Abubakar Mustapha na Rogo.

    Matakin ya biyo bayan amincewa da rahoton Kwamitin Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu na Majalisar, wanda shugabansa, Aliyu Muhammad, ya gabatar a zaman majalisar da kakakin majalisar, Ismail Falgore, ya jagoranta.

    Rahoton kwamitin ya ce an samu zargin karkatar da kuɗaɗen ayyukan raya ƙasa a Ƙaramar Hukumar Bagwai.

    A Bebeji kuwa, kwamitin ya ce ya gano zarge-zargen amfani da ofis ba bisa ƙa'ida ba, take dokokin bayar da kwangila da aiwatar da su, sayar da filayen gwamnati ba bisa ƙa'ida ba da karkatar da kuɗaɗen jama'a.

    Rahoton ya kuma zargi shugaban ƙaramar hukumar Bebeji da tilasta wa 'yan kwangila tura kuɗaɗen kwangilarsu zuwa wasu asusun banki da ake zargin shi ne ya zaɓa.

    A Rogo kuma, kwamitin ya ce shugaban ƙaramar hukumar na fuskantar zargin yin karan tsaye ga manufofin gwamnati, amfani da ofis ba bisa ƙa'ida ba da kuma karkatar da kuɗaɗen da aka ware domin ayyukan gina hanyoyin karkara da samar da wutar lantarki a al'ummomin Unguwar Dawa da Hausawa Fulani.

    Kwamitin ya ba da shawarar dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin har sai an kammala cikakken bincike, yana mai kafa hujja da sashe na 128 da 129 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999.

  6. Yaƙin Iran ya haɓaka ribar manyan kamfanonin man fetur

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gaggan kamfanonin man fetur sun ba da rahoton cin ribar da ba su taɓa samu ba daidai lokacin da yaƙin Iran ya cilla farashin mai sama.

    Kamfanin Saudi Aramco wanda ya fi samar da man fetur a duniya ya ba da rahoton samun ƙarin ribar kashi 44 a rubu'i na biyu na wannan shekara duk da rufe Mashigar Hormuz da Iran ta yi da kuma hare-haren mayaƙan Houthi a kan jiragen ruwan Saudiyya a Tekun Maliya.

    Su ma manyan kamfanonin makamashi na Ƙasashen Yamma su biyar BP da Chevron da ExxonMobil da Shell da kuma Total Energies sun wallafa zunzurutun ribar kusan dala biliyan 47.

    Farashin man fetur ya riƙa faɗuwa yana tashi tun bayan ɓarkewar yaƙin, in ji wakiliyar BBC, inda gangar ɗanyen mai nau'in brent ta kai sama da dala 120, kafin farashin ya sauka, a kan alƙawarin tattaunawa.

    Shugaba Trump ya soki lamirin kamfanonin man da ya zarga da cin ƙazamar riba a dalilin yaƙi kuma ya nemi su sauko da farashi saboda jama'a.

  7. Babu wani shirin tattaunawa kai tsaye tsakanin Amurka da Iran - Qatar

    Ƙasar Qatar ta bayyana cewa masu sasanci na ci gaba da ƙoƙarin nemo mafita ta diflomasiyya ga saɓanin da ke tsakanin Iran da Amurka, sai dai ta ce babu wani shiri a yanzu na tattaunawa kai tsaye tsakanin ɓangarorin biyu.

    Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar, Majid Al-Ansari, ya ce masu shiga tsakani na ci gaba da tuntubar dukkan ɓangarorin da abin ya shafa domin rage tsamin dangantaka.

    Qatar, tare da Pakistan, na daga cikin ƙasashen da ke taka rawa wajen shiga tsakani tsakanin Iran da Amurka yayin da ake ƙoƙarin rage tashin hankali da buɗe ƙofar tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu.

  8. Gwamna Uba Sani ya ba mijin malamar Islamiyyar da aka ƙona a Kaduna kyautar gida

    Uba Sani

    Asalin hoton, Kaduna Govt

    Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bai wa Malam Usman Aliyu, mijin marigayiya Ummulkhairi malamar Islamiyyar da aka ƙona kyautar gida domin taimaka masa ya sake gina rayuwarsa bayan wannan ibtila'i.

    An ƙona matar ne a wani hari da wasu matasa suka kai mata bayan zarginta da satar yara a Maraban Jos da ke jihar.

    Gwamnan ya miƙa masa takardun gidan ne a lokacin da ya kai masa ziyarar godiya tare da rakiyar Sheikh Haliru Maraya.

    Gwamnan ya ce tun bayan aukuwar lamarin, ya kai ziyara ga iyalan marigayiyar domin jajanta musu tare da tabbatar musu cewa gwamnatin jihar ba za ta tsaya ga kalaman ta'aziyya kawai ba.

    Ya ce baya ga samar musu da gida da tallafin kuɗi, gwamnati ta kuma ɗauki nauyin karatun ‘ya’yansu domin tabbatar da kyakkyawar makomarsu.

  9. Zaftarewar ƙasa ta hallaka mutum 14 a yankin Amhara na Habasha

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana ci gaba da aikin ceto a yankin Amhara da ke arewacin ƙasar Habasha bayan wata zaftarewar ƙasa da ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ta kashe mutane 14 tare da jikkata wasu bakwai.

    Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar jiya a wani wurin ibada na sufi, inda ɗaruruwan masu ibada suka taru domin wani biki na addini.

    Rahotanni sun ce har yanzu ba a san adadin mutanen da suka maƙale ƙarƙashin ɓaraguzan ƙasa ba, yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da lalube domin gano waɗanda abin ya rutsa da su.

    Irin waɗannan zaftarewar ƙasa na ƙara yawaita a Habasha, musamman a lokacin damina da kan fara daga watan Yuni zuwa Satumba.

  10. Gasar Commonwealth: Tinubu ya jinjina wa Najeriya bayan samun lambobin yabo 24

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya taya tawagar Najeriya murnar bajintar da ta nuna a Gasar Commonwealth da aka gudanar a birnin Glasgow na ƙasar Scotland, bayan da ta lashe jimillar lambobin yabo 24.

    Tawagar ta samu lambobin zinariya 10, azurfa 7 da tagulla 7, lamarin da ya sanya Najeriya cikin ƙasashen da suka yi fice a gasar.

    A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya yaba wa 'yan wasan kan jajircewa, ƙwazo da kuma nuna ruhin kishin ƙasa da ya dace da sunan Najeriya a idon duniya.

    Shugaban ya ce nasarorin da suka samu sun nuna irin wahalar da suka sha wajen horaswa da kuma ƙudirin da suke da shi na yin zarra.

    Tinubu ya kuma yabawa shugabannin Kwamitin Olympics na Najeriya da Hukumar Kula da Wasanni ta Ƙasa saboda ci gaba da tallafa wa 'yan wasa da bunƙasa harkokin wasanni a ƙasar.

    Ya ce ƙwarewar da 'yan wasan suka samu a gasar za ta taimaka musu wajen cimma manyan nasarori a wasu gasa na duniya da za su zo nan gaba.

    Shugaban ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da saka hannun jari a fannin wasanni, da inganta cibiyoyin horaswa tare da samar da ƙarin damar da za su ba matasan Najeriya damar haskakawa a matakan nahiya da na duniya.

  11. Babu wani rashin jituwa tsakanina da Mojtaba Khamenei - Shugaban Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Iran, Massoud Pezeshkian, ya ce babu wani saɓani ko rashin jituwa tsakaninsa da jagoran addinin ƙasar, Mojtaba Khamenei, yana mai musanta jita-jitar da ke cewa dangantakarsu ta yi tsami.

    Ya kuma jaddada cewa ba shi da niyyar yin murabus daga muƙaminsa.

    Pezeshkian ya ce: "Ba zan yi murabus ba, zan tsaya daram."

    Ya kara da cewa wasu na ƙoƙarin haddasa rikici a tsakanin shugabannin ƙasar ta hanyar yaɗa labaran da ke nuna cewa jagoran addinin ƙasar na faɗin wani abu, yayin da gwamnati ke faɗin wani abu daban.

    Tun bayan da Mojtaba Khamenei ya karɓi shugabancin Iran bayan rasuwar mahaifinsa sakamakon yaƙi, an riƙa samun rahotanni marasa tabbaci da ke hasashen cewa Pezeshkian na iya yin murabus daga muƙaminsa.

    A gefe guda kuma, ana ci gaba da samun saɓanin bayanai tsakanin Iran da Amurka kan batun tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu.

    Yayin da shugaban Amurka Donald Trump ke ci gaba da cewa Amurka na tattaunawa da Iran, hukumomin Tehran suna musanta hakan, suna cewa babu wata tattaunawa da ake yi a halin yanzu.

  12. Dangantakar Iran da Iraq na cikin mafi kyawun yanayi - Araqchi

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, wanda ke ziyarar aiki a Iraq, ya bayyana cewa dangantakar ƙasashen Iran da Iraq tana cikin mafi kyawun yanayi a halin yanzu.

    A wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iraq ranar Litinin, Araqchi ya ce ziyarar da Firaministan Iraq ya kai Tehran kwanan nan ta gudana cikin yanayi mai kyau, inda ɓangarorin biyu suka yi tattaunawa mai amfani da ma'ana.

    Ya ƙara da cewa Iran da Iraq suna da haɗin gwiwa ta kusa a fannoni daban-daban da suka haɗa da siyasa, tattalin arziki, tsaro da harkokin sufuri.

    Ministan ya kuma bayyana cewa a yayin ziyararsa a birnin Najaf, ya shaida yadda aka yi shirye-shirye da tsare-tsare masu yawa domin kula waɗanda za su halarci tattakin Arba'een.

    A lokaci guda kuma Araqchi ya isa Karbala domin halartar bukukuwan Arba'een, firaministan Iraki Ali Zaidi ma ya kai ziyara birnin.

  13. An yi zanga-zangar adawa da atisayen sojin Amurka da Koriya ta Kudu a Seoul

    ....

    Asalin hoton, EPA/Shutterstock

    Wasu masu fafutukar kare muradun al’umma a birnin Seoul, babban birnin Koriya ta Kudu, sun gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Amurka ranar Talata 4 ga Agusta.

    Masu zanga-zangar, waɗanda ke cikin ƙungiyar "Korean Solidarity for Peace, Sovereignty and Reunification", sun buƙaci a dakatar da babban atisayen soji na shekara-shekara mai suna Ulchi Freedom Shield, wanda Koriya ta Kudu da Amurka ke yi domin ƙara karfafa hadin gwiwa da shirin ko-ta-kwana tsakanin sojojin kasashen biyu.

    Ana sa ran fara atisayen na bana cikin makwanni biyu masu zuwa, inda zai ɗauki tsawon kwanaki 10 ana gudanar da shi.

    Hukumomin da za su halarci atisayen sun haɗa da Rundunar Hadin Gwiwar Sojojin Koriya ta Kudu da Amurka, Rundunar Sojojin Amurka da ke Koriya ta Kudu, Rundunar Majalisar Dinkin Duniya, Babban Hafsan Sojojin Koriya ta Kudu da kuma wasu hukumomin gwamnati.

    Masu zanga-zangar sun bayyana cewa suna adawa da atisayen ne saboda sun yi imanin cewa yana iya ƙara dagula yanayin tsaro da tashin hankali a yankin Gabashin Asiya.

  14. Majalisar dokokin Kano ta amince da ƙudirin hana makarantu ƙara kuɗin makaranta barkatai

    ...

    Asalin hoton, Sanusi Bature D-Tofa

    Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da wani ƙudiri da zai ƙayyade wa makarantu masu zaman kansu ƙara kuɗin makaranta ba tare da izini da sahalewar hukuma ba, domin kare iyaye da masu kula da yara daga ƙarin kuɗaɗe barkatai.

    Ƙudirin gyaran dokar Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai ta shekarar 2026 ya tanadi cewa duk makarantar da ke son ƙara kuɗin makaranta dole ne ta fara neman amincewar hukumar da abin ya shafa.

    Rahotanni sun ce karin kuɗin da ya wuce kashi 10 cikin 100 zai buƙaci ƙarin nazari da sahalewa.

    Shugaban Majalisar, Ismail Falgore, ya ce dokar za ta taimaka wajen inganta tsarin gudanar da makarantu da kuma tabbatar da cewa ana kare muradun iyaye da ɗalibai.

    Haka kuma, dokar ta tanadi ƙirƙirar muƙamin Sakataren Zartarwa domin ƙara inganta gudanar da ayyukan hukumar.

    Majalisar ta amince da ƙudirin ne bayan zaman sauraron ra'ayoyin jama'a da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kwamitin ilimi na majalisar ya gudanar kafin gabatar da rahotonsa.

  15. Mun fasa kai wa Ukraine hari saboda ta nemi afuwa - Iran

    ....

    Asalin hoton, IRNA

    Iran ta ce ta shirya kai hari kan wurare uku a Ukraine bayan wani hari da aka kai wa jirgin kasuwancinta, amma daga baya ta dakatar da shirin bayan Ukraine ta nemi afuwa inda ta ce harin ba a yi shi da nufin tayar da rikici da Tehran ba.

    Babban mai ba wa jagoran Iran shawara kan harkokin soji, Mohsen Rezaei, ya ce bayan tattaunawar da aka yi tsakanin ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu, Ukraine ta bayyana cewa harin wani ɓangare ne na yaƙinta da Rasha, ba da niyyar kai wa ƙasar hari ba.

    Rezaei ya kuma yi iƙirarin cewa hare-haren jiragen sama marasa matuƙi da makamai masu linzami da Iran ta kai kan sansanonin Amurka sun taimaka wajen daƙile duk wani shirin farmakin da Amurka za ta iya kai wa.

    Game da mashigar Hormuz kuwa, ya ce Iran ba za ta amince da buɗe wata hanyar jiragen ruwa da ba ta ƙarƙashin ikonta ba, yana mai gargaɗin cewa za ta kai hari kan duk wani jirgin da ya bijirewa umarninta."

  16. Sojojin Najeriya 86 sun tafi aikin wanzar da zaman lafiya a Guinea-Bissau

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta tura jami'ai 86 zuwa ƙasar Guinea-Bissau domin aikin wanzar da zaman lafiya na ƙungiyar ECOWAS

    Rundunar ta ce wannan matakin na nuna ci gaba da jajircewar da Najeriya ke yi wajen tallafa wa zaman lafiya da tsaro a yankin Afirka ta Yamma.

    A wata sanarwa da rundunar sojin ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, ta ce jami'an da aka tura sun tashi daga filin jirgin saman ƙasar da ke Abuja kuma sun isa Guinea-Bissau lafiya domin fara aikinsu ƙarƙashin umarnin ECOWAS.

    Rundunar ta kuma ce Najeriya na ci gaba da kasancewa cikin ƙasashen Afirka da suka fi bayar da gudunmawa wajen ayyukan wanzar da zaman lafiya na ECOWAS da Tarayyar Afirka da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Rundunar sojin Najeriya dai ta ce wannan sabon aikin ya nuna muhimmiyar rawar da Najeriya ke takawa wajen hana rikice-rikice, gina zaman lafiya da kuma dawo da kwanciyar hankali a ƙasashen Afirka.

    An dai kafa wannan rundunar ne domin tallafa wa ɓangaren tsaro da kuma inganta yanayin siyasa a Guinea-Bissau, bayan shekaru ana fama da rikice-rikicen siyasa da juyin mulkin soja.

    Najeriya dai ta daɗe tana cikin ƙasashen da suka fi tura sojoji zuwa ayyukan ECOWAS, inda ta bayar da dakaru, kayan aiki da jagoranci a ƙasashe irin su Liberiya, Saliyo, Gambiya da kuma Guinea-Bissau.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar da suka haɗa da hare-haren 'yanbindiga, satar mutane domin neman kuɗin fansa da dai sauransu.

  17. Iran ta ƙaryata iƙirarin cewa shugaban ƙasar Pezeshkian ya yi murabus

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani babban jami'i a ofishin Shugaban Iran ya bayyana rahotannin da ke cewa shugaban ƙasar, Massoud Pezeshkian ya yi murabus a matsayin “karya tsagwaronta.”

    Mehdi Tabatabaei, mataimakin daraktan sadarwa da yaɗa bayanai na ofishin shugaban ƙasar, ya ce wasu masu tsattsauran ra'ayi ne ke yaɗa ƙarya domin kawo cikas ga haɗin kan ƙasa.

    Tun da farko, wasu kalamai da malamin addini Mohammad Bagher Kharrazi ya yi sun bazu sosai a kafafen yaɗa labarai da sada zumunta a Iran.

    Kharrazi ya yi iƙirarin cewa Mojtaba Khamenei ya ce idan Pezeshkian ya sake miƙa takardar murabus, za a amince da ita.

    Sai dai fadar shugaban ƙasar ta yi watsi da wannan iƙirari, tana mai cewa ba shi da tushe balle makama.

  18. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan sake kasancewa da ku a wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.