Wannan ce damar Iran ta ƙarshe -Trump

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Trump na Amurka ya dage kan cewa za a ci gaba da tattaunawa da Ira domin neman mafita ga rikicin da ke faruwa tsakanin kasashen biyu.
Da yake tattaunawa da manema labarai a afishinsa da ke Fadar White House a yau, Shugaban Amurkan Donald Trump ya ce wannan ce ‘damar Iran ta karshe domin sanya hannu kan yarjejeniyar’.
Ya kuma jaddada za a yi tattaunawar ne saboda Iran ta nemi hakan. Duk kuwa da cewa ta fito karara ta musanta cewa hakan bukatarta ce.
Hakan na zuwa ne lokacin da Trump ya zargi ‘yan siyasar Iran da ‘munafirci’ a shafinsa na Truth Social.
Ya rubuta cewa “Su ne suka nemi a tattauna, ko kuma kamar yadda wasu suke cewa sun roka ne; a tattauna da kuma wasu taruka nan ba da jimawa ba’’.












































