Ma'aikatar lafiyar Uganda ta tabbatar da ƙarin mutum shida da suka kamu da Ebola, a jimulla yawan mutanen da suka kamu sun kai 15.
Cikin wata sanarwa a shafin X, ma'aikatar lafiyar ta ce mutanen da suka kamu a yanzu na cikin waɗanda suka yi mu'amala da waɗanda a baya suka kamu da cutar.
An fara samun ɓullar cutar a ranar 15 ga watan Mayu sakamakon mutuwar wani ɗan Congo da aka kwantar a wani asibitin kuɗi.
Tun lokacin kuma aka yi ta samun ƙarin mutane da suka kamu da cutar ciki har da ma'aikatan lafiya.
Ma'aikatar lafiyar ta kuma ce tana sa ido kan mutum 668 da ake zargin sun kamu da cutar a wani ɓangare na ƙoƙarin da take na daƙile bazuwar cutar.
A gefe guda kuma, an sallami mutum biyu da suka warke daga cutar.
'Duniya za ta fuskanci tsananin yanayin zafi a bana'
Asalin hoton, Getty Images
Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce ya zama dole duniya ta kalli yanayin zafin da ake ciki a matsayin wata matsala ta sauyin yanayi a duniya.
Hukumar kula da yanayi ta duniya ta ce ana buƙatar a yi shirye-shirye domin tunkarar tasirin yanayin inda ake da yaƙinin za a yi tsananin zafi a watanni masu zuwa.
Yanayin na iya janyo ɗumamar yanayi a sassan duniya.
Hakan na faruwa duk shekara biyu zuwa bakwai inda na ƙarshe ya janyo 2024 ta zama shekara mafi zafi a tarihi.
Majalisar Turai ta amince a cire haraji kan kayayyakin Amurka
Kwamitin kasuwancin ƙasa da ƙasa na majalisar dokokin Turai ya amince da wata yarjejeniya don cire harajin da aka ƙaƙaba kan wasu kayayyakin Amurka.
Hakan muhimmin mataki ne aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma ta Amurka don sassauta rikicin ƙasuwanci tsakanin Amurka da yankin na Turai.
Ƙarƙashin yarjejeniyar, Brussels za ta soke duk wasu haraje-haraje kan kayayyakin Amurka yayin da a ɓangarenta Amurka za ta ƙayyade yawan harajin da za ta sa kan kayayyakin da ƙasashen Turai suke fitarwa a kan kashi 15.
Har yanzu dokar na buƙatar amincewar majalisar Turai a wani taro da za a yi nan gaba a wannan watan.
Shugaba Faye ya naɗa sabuwar majalisar ministoci
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya sanar
da sabuwar majalisar ministocin ƙasar da ta ƙunshi wasu mambobin jam'iyyar da suka yi aiki ƙarƙashin jagorancin tsohon ubangidansa kuma amininsa Ousmane Sonko.
Mista Sonko, wanda aka kora daga muƙamin firaminista
a kwanaki goma da suka gabata, bayan
shafe watanni ana takun saƙar siyasa, ya sha alwashin jam'iyyarsa ta Pastef, ba
za ta shiga cikin sabuwar gwamnati ba.
Wakilin BBC
ya ce Mista Sonko a gaban bainar jama'a
ya riƙa sukar matakan da shugaban ƙasar ke ɗauka domin magance matsalar bashin
da ƙasar ke fuskanta kafin ya kore
shi daga aiki.
Jam'iyyar Pastef
ta Mista Sonko ita ce take da rinjaye a majalisar dokokin ƙasar kuma yan
majalisar sun maida martani kan korar da aka yi wa Mista Sonko ta hanyar naɗa
shi a matsayin kakakin majalisar dokokin ƙasar, wanda wani abu ne da zai ba shi
damar ƙalubalantar shugaban na Senegal.
Sojoji sun kuɓutar da fasinjoji 23 da aka sace a babbar hanyar Kogi
Rundunar sojin Najeriya ta kuɓutar da fasinjoji 23 da wasu da ake zargin ƴanbindiga ne suka sace a kan hanyar Ayegunle zuwa Bunu a ƙaramar hukumar Kabba-Bunu da ke jihar Kogi.
Cikin wata sanarwa a shafin X, rundunar sojin ta ce an kai samamen ne sakamakon kiran gaggawa da suka samu da sanyin safiya lamarin da ya sa sojoji suka gaggauta kai ɗauki yankin.
A cewar sanarwar, maharan sun toshe babbar hanyar tare da garkuwa da matafiya da dama kafin jami'an tsaro su isa wajen.
"Duk da cewa masu garkuwar sun tsere kafin jami'an tsaro su zo, sojoji sun yi hanzarin kai farmaki kan hanyoyin da mayaƙan ke bi," in ji sanarwar.
Sojojin sun ce samamen ya sa sun gano motocin bas da motar dakon kaya da aka yasar kan titi.
Sanarwar ta ƙara da cewa akwai mutum biyu da suka mutu sai wasu biyar da suka ji rauni inda aka gaggauta kai su asibitin St Joseph da ke Kabba kuma a nan ake kula da su.
Mutum biyu sun mutu a zanga-zangar adawa da cibiyar Ebola ta Amurka a Kenya
Asalin hoton, Anadolu via Getty Images
An harbe mutum biyu a garin Nanyuki da ke tsakiyar
Kenya yayin da ake ci gaba da zanga-zanga kan shirin Amurka na buɗe cibiyar
killace masu Ebola a sansanin soji da ke kusa.
An harbi ɗaya daga cikin mutanen a wani yanki kusa
da sansanin sojin sama da ke Laikipia inda ake zanga-zangar. Ya mutu ne bayan
da abokansa suka kai shi asibitin garin.
Ɗaya mutumin kuma gawarsa sojoji suka kai asibiti.
Zuwa yanzu ba a san musabbabin mutuwarsu ba kuma
jami'ai ba su ce komai ba kan lamarin.
A ranar Litinin, ɗaruruwan masu zanga-zangar sun yi
tattaki kan titunan garin inda suka toshe tituna tare da ƙona tayoyi a gefe
guda kuma ƴan sanda sun yi ta harba haƴaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu
zanga-zangar.
Shirin na Amurka na kafa cibiyar kula da masu Ebola
a Kenya ya janyo damuwa a tsakanin al'ummar Kenya inda suke fargabar haɗarin
bazuwar cutar a ƙasar.
Likitoci daga Amurka ne za su kula da cibiyar mai
gadaje 50 kuma za a yi amfani da ita ne wajen kula da Amurkawa da suka kamu da
Ebola a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo.
Zuwa yanzu babu rahoton ɓullar cutar ta Ebola a
Kenya.
'Gwamnati ta yi watsi da yaranmu da aka sace a Borno'
Gwamnatin Najeriya na ci gaba da fuskantar matsin lamba kan gaza kuɓutar da ɗaliban makaranta 42 da aka sace a jihar Borno da har yanzu ke hannun ƴanbindiga.
Iyayen ɗaliban sun bayyana fargaba cewa kamar gwamnati ta manta da ƴaƴansu, saɓanin irin matakan da suke jin ana ɗauka a jihar Oyo na ƙoƙarin ceto ɗaliban da aka sace.
Sai dai tuni mai bai wa shugaban Najeriyar shawara kan harkokin yaɗa labarai, Abdulaziz Abdulaziz ya musanta zargin da iyayen ɗaliban jihar ta Borno suka yi.
Yaran dai sun shafe kwana 17 a hannun ƴanbindiga tun bayan sace su a garin Mussa a ƙaramar hukumar Askira Uba.
Dakta Chi Namke shugaban al'umma ne a yankin ya shaida wa BBC cewa suna cikin tashin hankali kasancewar yaran da aka sace ƙanana ne.
"Daga gwamnatin Borno, akwai kwamishinan ilimi da ya zo amma daga wajen gwamnatin tarayya ba mu ga ko mutum ɗaya ba," in ji Dakta Chi Namke.
A cewarsa, irin haka tana faruwa a wasu jihohin kuma gwamnatin tarayya tana aika tawaga domin jajanta musu.
Ambasada Ahmad Shehu, shugaban wata gamayyar ƙungiyar farar hula a yankin arewa maso gabas ya ce haƙƙin gwamnati ne ta gaggauta ceto ɗaliban.
"Da aka yi na Mussa, ya faru a jihar Oyo a lokaci ɗaya, namu ba abin da aka yi, sai wancan kuma gwamnati ta ɗauki mataki." in ji shi.
Ya ƙara da cewa "shugaban ƙasa ya buƙaci manyan jami'an tsaro da su tare a jihar Oyo domin ganin an kuɓutar da yaran da aka sace.
Fadar gwamnatin ta bakin Abdulaziz Abdulaziz dai ta danganta iƙirarin iyayen ɗaliban jihar ta Borno da shelar ƴan adawa saboda a cewarsa shugaba Bola Tinubu yana ƙoƙari ya ga an yi abin da ya dace domin kuɓutar da ɗaliban.
A yau Talata ne ƙungiyar ƙwadago ta malaman makaranta NUT za ta jagoranci zanga-zanga a sassan Najeriya domin tilasta wa gwamnati ɗaukar matakan gaggawa na ceto ɗaliban.
Isra'ila da Hezbollah na gwabza ƙazamin faɗa a Lebanon
Asalin hoton, Kawnat Haju / AFP via Getty Images
An ci gaba da gwabza ƙazamin faɗa a kudancin Lebanon duk da sanarwar da shugaba Donald Trump ya yi cewa Isra'ila da Hezbollah sun amince su daina faɗa da juna.
Rahotanni sun ce ɓangarorin biyu sun kai wa juna hare-hare.
Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya tabbatar da yarjejeniyar, amma ya yi gargaɗin cewa za a ci gaba da kai hare-hare ta sama idan ƙungiyar Hezbollah ta ci gaba da kai farmaki kan Israila.
Shugaba Trump ya ce ya tattauna da Netanyahu da wakilan Hezbollah kan shirin, bayan da Iran ta yi gargaɗin cewa matakin sojan da Isra'ila ta ɗauka a Lebanon barazana ce ga yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran a halin yanzu.
Rasha ta kai farmakin da ya halaka mutum 13 a Ukraine
Asalin hoton, AFP
Aƙalla mutum 13 ne
aka kashe a jerin hare-haren da Rasha ta kai wa wasu biranen Ukraine ta hanyar amfani da jirage
marasa matuƙa da makamai masu linzami.
Magajin garin Kyiv,
Vitali Klitschko ya ce an kashe mutane
huɗu a babban birnin ƙasar, sannan an raunata fiye da hamsin, ciki har da
yara da dama.
Wakilin BBC ya ce magajin garin Kyiv ya kuma ce an
kai wa wani asibiti hari, lamarin da ya sa wani ɓangare na ginin rugujewa.
Hukumomin birnin
Dnipro da ke gabashin ƙasar sun ce mutane tara ne suka mutu a hare-haren da
aka kai a can.
Tun farko shugaba Zelensky ya ce bayanan sirri sun nuna cewa Rasha na shirin kai wa ƙasarsa gagarumin farmaki.
Barka da Safiya
A yau ma shafin Kai Tsaye na BBC Hausa na yi muku maraba, da fatan mun wayi gari lafiya.
Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Nabeela Mukhtar Uba tare da abokin aiki Haruna Kakangi za mu kasance tare da ku.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin kallon bidiyo da ma tafka muhawara game da labaran da muka wallafa.