Amurka za ta fitar da dala miliyan 600 domin tallafin allurar riga-kafi
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka za ta fitar da kudade har dala miliyan dari shida nan ba da jimawa ba domin Ƙungiyar Gavi, wacce ke taimaka wa kasashe masu tasowa wajen samar da allurar riga-kafi.
Tunda farko Sakataren lafiyar Amurka Robert Kennedy ne ya riƙe kuɗaden bayan ya yi amannar cewa Gavi na amfani da sinadaran da aka daina amfani da su wadanda ke da haɗari ga lafiyar dan'adam.
Sai dai Gavi ta ce matakin na shi ya jefa miliyoyin yara cikin hadarin kamuwa da cututtukan da ake iya ɗauka.


















