Amurka ta cire wa kamfanin jirgin saman Iraƙi takunkumi
Asalin hoton, Getty Images
Sashen Baitul Mali na Amurka ya cire sunan kamfanin jirgin
saman Iraƙi daga cikin jerin sunayen waɗanda ya sanya wa takunkumi.
Jirgin Fly Baghdad wanda ake kira da (Iraqi Express) wanda aka sawa takunkumi saboda alaƙarsa
da dakarun juyin juya halin Iran an cire shi daga jerin sunayen da aka sawa
takunkuman.
An kuma ƙara
janye wa wasu kamfanonin jirage biyu na daban suma takunkumansu.
Har yanzu sashen
Baitil Malin Amurkan bai fitar da bayanai ba kan dalilin cire takunkumin.
Sai dai an sa
musu tankunkuman ne tun da fari a yaƙin da ake yi da ‘yan ta’adda a duniya.
An kusa cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Oman kan Mashigar Hormuz
Asalin hoton, Getty Images
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran ya ce ana ƙoƙarin ƙarƙare wata sanarwar haɗin gwiwa tsakanin Iran da Oman a kan wata sabuwar hanyar da za a fitar domin ratsawa ta Mashigar Hormuz -- matuƙar dai kamar yadda ya bayyana wasu 'yan kiɗan-ka-na-jiyo ba su yi katsalandan ba.
Shugaba Trump da wasu manyan jami'an Amurka sun yi bayani game da yiwuwar cimma wata yarjejeniya da za a amince da ita a kan wannan muhimmiyar hanyar teku.
Sai dai Esmail Baghaei ya sake nanata cewa yarjejeniyar tsakanin Iran da Oman a karan kanta, ba za ta iya samar da tabbacin tsaro a mashigar ba.
Babu kuma fayyataccen bayani ko Amurka za ta amince da duk yarjejeniyar da aka cimma idan ta bai wa hukumomin birnin Tehran ikon da mashigar.
Infantino na tattaunawa da mambobin FIFA a Rabat
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban FIFA Gianni Infantino na gudanar da tattaunawa kan ƙurar da ta turnuƙe a Moroko, yayin da yake fatan haɓaka matsayinsa bayan shirinsa na sayar da hannun jari a Gasar cin Kofin Duniya da sauran gasanni ya rushe.
An fahimci cewa taron na gudana ne ofishin FIFA na nahiyar Afirka a kusa da birnin Rabat.
An yi imani Babban Sakataren FIFA, Mattias Grafstrom wanda aka kwarmata saƙon imel ɗin da ya rubuta wa ma'aikatan hukumar yana sukar shirin a ranar talata, shi ma yana cikin masu halartar tattaunawar.
Ba a sanar taƙamaimai dalilin kiran tattaunawar ba, sai dai ana sa ran cewa Mista Infantino zai yi ƙoƙarin gyara dangantaka a yunƙurinsa na ci gaba da riƙe muƙaminsa.
Isra’ila ta kashe mutum ɗaya 11 sun jikkata a harin da ta kai Lebanon
Hukumomin Lebanon
sun ce an kashe mutum daya wasu 11 na daban sun jikkata a wani hari da Isra’ila
ta kai musu.
Kamfanin
dillancin labarai na ƙasar ya ce har da Isra’ilan ta kai ya lalata rufin wani
dakin addu’a a cikin maƙabartar birnin Tibnin da ke kudancin Lebanon.
Dakarun Isra’ila
sun sanar da cewa sun kai harin ne a matsayin ramuwa kan karya yarjejeniyar da
aka cimma ta tsagaita da Hezbollah.
Isra’ila ta ce ta kai hari ne kan wata maɓoyar
Hezbollah a kudancin Lebanon.
An gano jirgi maras matuƙi ɗauke da ababen fashewa a filin jirgin Jamus
Asalin hoton, RICO THUMSER/AFP
'Yan sanda a Jamus sun ce sun gano wani jirgi maras matuƙi ɗauke da ababen fashewa a filin jirgin sama na Leipzig.
Sun ce an kwance ɗamarar makamin bayan wani ma'aikacin ya gano shi da daddare a sashen kaya.
'Yan sanda na kuma binciken wani abu da ba a tantance ko mene ne ba, wanda ya je ya karawa wani jiragin sama a dai filin jirgin.
Jirgin saman wanda jim kaɗan da tashinsa kenan lamarin ya faru, ya samu lahani ƙanƙani amma dai ya sauka lafiya. Duk al'amuran biyu sun faru ne a kusa da inda ake ajiye jiragen kaya na Ukraine.
Rasha ta musanta hannu a jerin zirga-zirgar jirage marasa matuƙin da ba su da izinin hukuma, waɗanda aka gano cikin 'yan watannin nan a Jamus.
Taimakon da ƙasashen waje ke mana ya ragu - Zelensky
Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Zelensky ya yi ƙorafin cewa yawan makaman kare sararin samaniyar da ƙasashen waje ke bai wa Ukraine sun ragu da ninki uku a kan bara, wannan na zuwa ne, bayan hare-haren Rasha sun kashe a ƙalla mutum bakwai a Kyiv da kuma zagayen babban birnin.
Zelensky ya roƙi ƙasashe abokan ƙawancen Ukraine su ƙara samar wa ƙasarsa makaman kariya.
Wata tashar jirgin ƙasa da wata cibiyar rarrabe saƙonnin gidan waya na cikin wuraren da aka samu -- a ɗaya daga cikin jerin hare-hare mafi muni da Rasha ta kai a bana.
Hare-haren makamai masu linzami sun auka wa birnin cikin tsakiyar dare, inda aka riƙa ganin walƙiya a sararin sama, kafin kuma gobara ta tashi a unguwannin waje-waje.
A can Rasha, jiragen Ukraine marasa matuƙi ne suka far wa wani gidan ajiyar kaya, mallakar katafaren kantin Wildberries mai hada-hada ta intanet.
Ƴanbindiga sun sako mutanen Kwara da aka yi garkuwa da su bayan wata shida
Asalin hoton, Kwara State Governor
Gwamnatin jihar Kwara da ke arewa ta Tsakiyar Najeriya ta tabbatar da sako mutanen da aka yi garkuwa da su a yukan Woro da Nuku da ke ƙaramar hukumar Kiama bayan wata shida a hannun ƴanbindigar.
A watan Fabrairin wannan shekarar ne dai wasu ƴanbindiga suka kai hari ƙauyukan biyu tare da kashe fiye da mutum 75 da sace aƙalla mutum 175.
Cikin wata sanarwa da gwmanatin jihar ta fitar da tabbatar da sakin mutanen, sai dai ba ta yi ƙarin haske kan adadin wadanda aka sako ɗin ba.
Haka kuma sanarwar ba ta fayyace ko an biya kuɗin fansa kafin sakin mutanen ba.
Wani ɗan majalisar wakilai na yankin ya shaida wa BBC cewa yanzu haka mutanen da aka sako na hannun jami'an tsaro, inda suke samun kulawar likitoci, kafin sada su da iyalansu.
Harin da aka kai cikin watan Fabrairu lokacin sace mutanen, ya kasance ɗaya daga cikin munanan hare-haren da aka fi samun asarar rayuka a yankin cikin shekarun baya-bayan nan.
Hukumomi sun ɗora alhakin harin kan mayaƙa masu iƙirarin jihadi da ke cikin dazukan kusa da iyakar Najeriya da Benin.
Sakin mutanen ya zo ne makonni bayan sakin ɗalibai da malamai 44 da aka yi garkuwa da su a jihar Oyo, bayan sun shafe sama da makonni bakwai a hannun masu garkuwa da mutanen.
Najeriya na cewa tana kara ƙaimi wajen hare-haren soji kan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, amma har yanzu ƙasar fuskantar ƙalubalen tsaro da dama, da suka haɗa da hare-haren masu iƙirarin jihadi da garkuwa da mutane masu yawa.
Jirgi mara matuƙi ya jiwa wani jami'in Rasha rauni
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban wani kamfani mai ƙera jiragen Rasha marasa matuƙi ya ji rauni a fashewar wani abu cikin mota.
Vladimir Tkachuk shi ne shugaban kamfanin Uraldron wanda ke yin jirage marasa matuƙin da sojojin Rasha ke amfani da su.
An ba da rahoton cewa an garzaya da shi sashen masu tsananin jinya a asibiti.
Haka zalika, bayanai sun ce an kashe direbansa.
Harin ya faru ne a wajen birnin Yekaterinburg cikin daren jiya.
MDD ta ce fiye da mutum 800,000 ne suka koma gidajensu a kudancin Lebanon
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mutane fiye da 800,000 da rikicin baya-bayan nan tsakanin Isra'ila da Hezbollah ya raba da gidajensu ne suka koma gidajensu a Lebanon.
Hukumar jin ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce akwai mutane kimanin 360,000 ke ci gaba da tarwatsewa a faɗin ƙasar, yayin da wasu kimanin 26,000 ke samun mafaka a gine-ginen zaman gaggawa na hukuma.
Rikicin baya-bayan nan tsakanin Hezbollah da Isra'ila ya tilasta wa ɗumbin ƴan Lebanon tsere wa gidajensu.
Ƙura ta lafa tun da Isra'ila da Lebanon suka sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar da Amurka ta ɗauki nauyi a watan Yuni.
Sai dai dakarun Isra'ila na ci gaba da tabbatar da iko a mafi yawan yankin kudancin Lebanon, inda suka yi rugu-rugu da gidaje, da ƙauyukan da suka ce daga nan ne Hezbollah ke aikace-aikacenta.
NiMet ta yi gargaɗin yiwuwar ambaliya yayin da ake sa ran ruwan sama a jihohi da dama
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargaɗin yiwuwar ambaliya a wasu yankunan da ke da ƙarancin tudu yayin da ta yi hasashen samun ruwan sama da tsawa a sassa da dama na ƙasar a ranar Laraba, 5 ga Agusta 2026.
Hukumar ta shawarci mazauna yankunan da ke fuskantar barazanar ambaliya da su kasance cikin shiri tare da kauce wa bi ta hanyoyin da ruwa ya mamaye, sakamakon ruwan sama da ake sa ran zai sauka a yankuna daban-daban na ƙasar.
A yankin Arewacin Najeriya, ana sa ran tsawa da ruwan sama a jihohin Sokoto, Kebbi, Katsina, Kano, Zamfara, Gombe, Bauchi, Taraba da Adamawa. A Tsakiya kuwa, Abuja da wasu sassan Plateau da Nasarawa za su fuskanci tsawa tun da safe, yayin da za ta bazu zuwa wasu jihohi da yamma.
A Kudancin ƙasar kuma, ana sa ran gajimare da ruwan sama a wasu yankuna, musamman jihohin Ondo, Ekiti, Oyo da mafi yawan yankunan Kudu maso Gabas da Kudancin Kudu., in ji hukumar.
NiMet ta kuma buƙaci kamfanonin jiragen sama su nemi bayanan yanayi na musamman domin tabbatar da tsaro a harkokin sufurin jiragen sama.
Zakuna uku sun mutu a Japan sakamakon tsananin zafi
Asalin hoton, Tokyo Zoological Park Society
Zakuna mata uku sun mutu a wani gidan namun daji da ke Tokyo a kasar Japan, lamarin da mahukunta suka danganta da matsanancin zafi da ake fama da shi a kasar yayin bazara, bayan binciken farko ya nuna cewa sun sha fama da rashin ruwa a jiki da kuma gazawar wasu muhimman sassan jikinsu.
Zakunan, waɗanda shekarunsu suka kai tsakanin uku zuwa 15, sun mutu ne cikin mako guda a gidan namun dajin Tama Zoological Park da ke yammacin Tokyo.
"Wannan shi ne karo na farko da muka fuskanci irin wannan yanayi. Bara ma an yi zafi sosai, amma babu wani zaki da ya kamu da rashin lafiya kamar haka," in ji Miwa Kosaka, wakiliyar gidan namun dajin, a wata hira da BBC.
A shekarun baya-bayan nan, yanayin zafi a lokacin bazara a Japan na ƙara tsananta, inda wasu birane ke fuskantar kwanaki masu tsananin zafi da yanayin ya haura digiri 40 na ma'aunin Celsius.
Mahukuntan gidan namun dajin sun ce wasu daga cikin zakunan da suka kamu da rashin lafiya sun fara samun sauƙi, yayin da wasu shida kuma suna cikin ƙoshin lafiya ba tare da wata matsala ba.
An mayar da waɗanda ba su da lafiya wani wuri na musamman da aka tanada domin kulawa da su, inda aka girke na'urorin sanyaya iska da manyan fankoki domin rage tasirin zafin da ake fama da shi.
Falasɗinu na da matuƙar muhimmanci a garemu - Iran
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa Falasɗinu na da matuƙar muhimmanci a manufofin harkokin wajen ƙasarsa.
Kafofin yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa shugaban ya faɗi hakan ne yayin wata tattaunawar wayar tarho da Khalil al-Hayyah, sabon shugaban ƙungiyar Hamas.
A yayin tattaunawar, Pezeshkian ya jaddada cewa Iran za ta ci gaba da bai wa batun Falasdinu muhimmanci a manufofinta na ƙetare.
Khalil al-Hayyah ya zama sabon shugaban ofishin siyasa na Hamas bayan da ƙungiyar ta fuskanci asarar shugabanni da dama sakamakon hare-haren Isra’ila da suka biyo bayan harin 7 ga Oktoban 2023.
Tsohon shugaban Hamas, Ismail Haniyeh, ya mutu a wani hari da aka kai masa a Tehran shekaru biyu da suka gabata yayin da ya je halartar bikin rantsar da Pezeshkian a matsayin shugaban ƙasar Iran.
Hamas na ci gaba da fuskantar matsin lamba da hare-hare daga Isra’ila a rikicin da ya daɗe yana ci gaba a yankin.
Sama da ɗalibai miliyan 1.2 sun ci jarabawar WAEC ta 2026
Asalin hoton, WAEC/X
Sama da ɗalibai miliyan 1.2 daga cikin 1,950,726 da suka rubuta jarabawar kammala sakandare ta WAEC ta shekarar 2026 sun samu sakamako mai kyau inda suka samu kiredit a aƙalla darussa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.
Hukumar WAEC ta ce ɗalibai 1,200,514 ne suka samu wannan nasara, wanda ya kai kashi 61.54 cikin 100 na jimillar masu jarabawar.
Hukumar ta kuma ce ta riƙe sakamakon ɗalibai 167,486 saboda zargin satar jarabawa yayin da ba ta faɗi yawan waɗanda suka faɗi jarabawar ba.
WAEC ta sanar da fitar da sakamakon jarabawar tare da buƙatar ɗalibai su fara samar da lambar PIN da serial number ta shafinta kafin su duba sakamakonsu a shafin internet ɗinta na binciken sakamako
Hukumar ta ce ana buatar ɗalibai su yi amfani da lambar jarrabawarsu da kuma lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN) da suka yi amfani da ita wajen rajista domin tantance bayanansu.
Kusan dalibai miliyan 1.96 daga makarantu sama da 24,200 a Najeriya ne suka rubuta jarabawar da aka gudanar tsakanin 21 ga Afrilu zuwa 19 ga Yunin 2026.
'Barazanar Trump ce ta jawo jinkirin cimma yarjejeniya kan mashigar Hormuz'
Asalin hoton, Getty Images
Kafafen yaɗa labaran Iran, ciki har da kamfanin dillancin labarai na Tasnim, sun rawaito cewa wani jami’i da ya nemi a sakaya sunansa ya ce tsoma bakin Amurka da kuma barazanar Shugaban Amurka Donald Trump ne suka haddasa jinkirin cimma yarjejeniya da Oman kan mashigar Hormuz.
Jami’in ya shaida wa Sepah News cewa “Matuƙar Amurka na ci gaba da tsoma baki tare da yi wa Iran barazanar hari, ba za a cimma yarjejeniya ba,” yana mai jaddada cewa Iran ba za ta amince da wata yarjejeniya a ƙarƙashin matsin lamba ko barazana ba.
A baya, an ruwaito cewa Shugaba Donald Trump ya nuna fatan cewa za a sake buɗe mashigar Hormuz cikin gaggawa, amma a lokaci guda ya yi barazanar kai hari kan Iran idan ba a cimma matsaya ba.
Mun kai hari kan jirgin dakon man fetur na Saudiyya - Mayaƙan Houthi
Mayaƙan Houthi na Yemen, masu goyon bayan Iran, sun bayyana cewa sun kai hari kan wani jirgin dakon man fetur na Saudiyya a Tekun Bahar Maliya (Red Sea) ta hanyar amfani da makami mai linzami.
Mai magana da yawun rundunar Houthi, Yahya Saree, ya ce a cikin wata sanarwar bidiyo cewa sun yi nasarar kai hari kan jirgin man fetur na Saudiyya mai suna Wafa a arewacin Bahar Maliya kusa da gabar tekun Yanbu, inda suka harba masa makamai masu linzami da dama.
Ya ƙara da cewa wannan shi ne jirgi na takwas da suka kai wa hari tun bayan fara abin da suka kira toshe ruwa kan Saudiyya.
Sai dai Saree bai bayyana lokacin da aka kai harin ba.
Ƴansanda sun kama masu aikata laifi 13 tare da ƙwato makamai a Abia
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar 'yansandan jihar Abia ta sanar da kama mutum 13 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a wasu samame da ta gudanar a faɗin jihar, a wani yunƙuri na daƙile fashi da makami, ayyukan ƙungiyoyin asiri da kuma lalata kadarorin gwamnati.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Maureen Chinaka, ta ce jami'an rundunar sun gudanar da kamen ne bisa bayanan sirri da suka samu.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani mutum mai shekara 27 da ake zargi da safarar wani babban bututun ruwa da aka lalata, wanda aka ɓoye a cikin wata motar haya a yankin Ubakala da ke Umuahia.
Haka kuma, 'yansanda sun kama wasu da ake zargi da fashi da makami a Aba, inda suka ƙwato bindigogi, harsasai da wasu kayan da ake zargin na ƙungiyoyin asiri ne.
Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da duk waɗanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala binciken.
Ta kuma buƙaci mazauna jihar da su ci gaba da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaƙi da laifuffuka.
Farashin mai ya faɗi a kasuwar duniya saboda yiwuwar buɗe Mashigar Hormuz
Asalin hoton, Getty Images
Farashin ɗanyen mai ya faɗi a kasuwaar duniya cikin kusan makonni uku, bayan manyan jami'an gwamnatin Amurka sun bayyana cewa ana samun ci gaba a tattaunawar da ake yi da Iran kan yiwuwar sake buɗe Mashigar Hormuz.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, da Sakataren Baitulmali, Scott Bessent, sun ce ana ci gaba da tattaunawar da za ta iya bai wa jiragen ruwa damar sake zirga-zirga ta mashigar tun daga wannan makon.
Bayan wannan sanarwa, farashin gangar ɗanyen mai na Brent, wanda ake amfani da shi a matsayin ma'aunin farashin mai a kasuwannin duniya, ya ragu da kusan kashi biyar cikin ɗari, inda ya sauka zuwa ƙasa da dala 80 kan kowace ganga.
A ranar Talata kuma, farashin ɗanyen mai na West Texas Intermediate (WTI) na Amurka ya sauka da fiye da kashi biyar cikin ɗari, inda ya kai kusan dala 76 kan kowace ganga.
Tun daga 13 ga watan Yuli ake samun raguwar farashin man.
Marco Rubio ya ce an samu ci gaba a tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da Iran da kuma Oman kan yadda za a ba jiragen ruwa damar ci gaba da zirga-zirga ta Mashigar Hormuz.
PDP ba za ta iya cin zaɓen shugaban ƙasa a 2027 ba – Wike
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce jam'iyyar PDP ba ta da ƙarfin da za ta iya lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 saboda matsalolin cikin gida da ke addabarta a halin yanzu.
Wike ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce abin da PDP za ta fi mayar da hankali a kai yanzu shi ne lashe wasu kujerun jihohi da kuma sake tsara jam'iyyar domin tunkarar zaɓen shekarar 2031.
Ya ce da wahala jam'iyyar ta gudanar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa mai ƙarfi a 2027, saboda har yanzu tana fama da rikice-rikicen cikin gida.
A cewarsa, "Tun da daɗewa nake faɗa cewa PDP ba za ta iya cin zaɓen shugaban ƙasa yanzu ba. Abin da muke yi shi ne ƙoƙarin lashe wasu muƙaman jihohi da kuma shirya jam'iyyar domin zaɓen 2031."
Iran da Amurka da Oman sun kusa cimma matsaya kan sake buɗe Mashigar Hormuz
Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni sun nuna cewa Iran da Amurka tare da Oman na dab da cimma wata yarjejeniya ta wucin gadi kan sake buɗe Mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanyar safarar mai da iskar gas ta duniya.
Kamfanin Axios ya rawaito cewa, bisa yarjejeniyar da ake tattaunawa a kai, jiragen ruwa masu shiga Tekun Fasha za su bi ta hanyar da ta ratsa ruwan Iran, yayin da masu fita za su bi ta ruwan Oman tare da haɗin gwiwar Iran.
Haka kuma, a cikin kwanaki 60 na farko na aiwatar da yarjejeniyar, ba za a karɓi kuɗin haraji daga jiragen ruwa masu wucewa ba.
Rahoton ya ƙara da cewa ɓangarorin za su gudanar da aikin kawar da nakiyoyi a tsakiyar Mashigar Hormuz cikin kwanaki 30, kafin a tsara wata yarjejeniya ta dindindin kan yadda za a riƙa amfani da hanyar ruwan.
An kama wani mutum da bindiga a wurin da Trump zai kai ziyara a California
Asalin hoton, Getty Images
Jami'an tsaro a jihar California sun kama wani mutum ɗauke da bindiga a filin wasan golf mallakin shugaban Amurka Donald Trump gabanin ziyarar da shugaban zai kai wurin domin halartar wani taron tara kuɗaɗe na Jam'iyyar Republican.
Masu bincike sun ce an kama mutumin, mai suna Jeanine John Tael da shekaru 38 ne a filin wasan da ke Rancho Palos Verdes tare da bindiga da kuma haramtattun alburusai.
'Yansanda sun bayyana cewa an ga mutumin yana yawo a wurare daban-daban na filin wasan, yana ɗaukar hotuna da bidiyo tare da lura da shirye-shiryen tsaro da ake yi gabanin zuwan Trump.
An kama shi ne ranar Lahadi, kuma a yanzu yana tsare yayin da yake fuskantar zargin ɗauke da bindiga a ɓoye da kuma mallakar haramtattun alburusai.