Sojojin Najeriya, ƙarƙashin rundunar Operation HADIN KAI mai yaƙi da Boko Haram ta ce dakarunta sun kashe mayaƙan ISWAP kusan 50 a wani gumurzu da mayaƙan ƙungiyar a Buni Gari da ke jihar Yobe.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Laftanal Kanal Sani Uba ya fitar ya ce lamarin ya faru ne a daren Juma'a, lokacin da maharan suka biyo duhun dare don ƙaddamar da mummunan hari kan shalkwatar sojoji ta 27 Brigade da ke Buni Gari.
Sanarwar ta ce sojojin sun mayar da martani cikin ƙwarewa da ƙarfin makamai, lamarin da ya ba su damar fatattakar mayaƙan.
Sani Uba ya ce mayaƙan sun karkasu zuwa gida uku, inda suka riƙa far wa shalkwatar a lokuta daban-daban, da nufin mamayeta da yi wa dakarun ƙawanya, amma sojojin suka turji tare da fatattakar mayaƙan cikin ƙwarewa.
Sojojin sun ce dakarun ƙasan sun samu taimakon na sama, ta hanyar aika jirgi, da ya riƙa bin mayaƙan yana jefa musu bama-bamai, a lokacin da suke tserewa.
Sanarwar ta kuma ce sojojin sun ƙwato makamai masu yawa, nau'ika daban-daban ciki har da nakiyoyi da makaman harba gurneti.
Sai dai rundunar sojin ta ce biyu daga cikin dakarunta sun rasu a lokacin musayar wutar.