Jirgin sama buge wani mutum a Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Fiye da fasinjoji 200 aka fitar daga wani jirgin sama a Amurka bayan da ya jirgin ya bugi wani mutum da ke tafiya a kan titin jirgin kafin tashinsa.
Direban jirgin ya dakatar da shirin tashi bayan faruwar lamarin, sakamakon wutar da ta kama ɗaya daga cikin injunan jirgin.
A wani saƙon murya da aka naɗa daga ɗakin kula da tashin jiragen an ji muryar direban jirgin na cewa injin jirgi ya kama da wuta.
Kamfanin jirgin, Frontier, da ya mallaki jirgin ya ce ya kaɗu da faruwar lamarin, kuma tuni aka ƙaddamar da bincike.


