Abubuwan da za su bai wa Arsenal ƙwarin gwiwar doke PSG

    • Marubuci, Adwaidh Rajan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
  • Lokacin karatu: Minti 5

"Akwai wasu lokuta a Gasar Zakarun Turai da wani ɗan wasan kan yi abubuwan mamaki - kuma ya sake yin hakan,'' a cewar Mikel Arteta, bayan da ƙungiyarsa ta Arsenal ta doke Atletico Madrid ta kai wasan ƙarshe na farko a babbar gasar Turai cikin shekara 20.

Za ka iya tunanin cewa waɗannan kalaman na Arteta da Bukayo Saka yake, wanda ya ci ƙwallon da ta kai Arsenal wasan na ƙarshe.

To amma wannan lokacin ''na mamaki'' da Arteta ke nufi shi ne ɗan wasan baya Gabriel wanda ya zama ginshiƙi wajen tsaron bayan Arsenal.

Wani kuskuren da William Saliba ya yi, ya bai wa ɗan wasan Atletico, Giuliano Simeone damar zura, ƙwallo amma sai golan Arsenal, David Raya ya yi bajintar tare ta.

An riƙa sukar masu tsaron bayan Arsenal da rashin iya sanin ƙafar juna, da rashin aiki tare, to amma sun yi matuƙar ƙoƙari wajen kai Arsenal wasan ƙarshe a Gasar Zakarun Turai.

To sai dai har yanzu, babban gwajinsu bai zo ba, sai a ranar 30 ga watan Mayu a birnin Budapest, inda za su kara da PSG, wadda ta kai wasan ƙarshen bayan doke Bayern Munich 6-5 gida da waje.

'Arsenal na da ƴar dama a kan PSG'

Wani mutum da ya san sirrin cin Kofin Gasar shi ne Clarence Seedorf, ɗan wasa ɗaya tilo da ya ci kofin har sau uku da ƙungiyoyi daban-daban.

Tsohon ɗan wasan tsakiyar ya yi imanin cewa Arsenal ta inganta tsaron bayanta, amma yana da kyau ta ƙara a karawarta da PSG.

"Ƙungoyi irin Arsenal sun inganta tsaron bayansu a wannan kaka inda suka yi wasanni da dama ba tare da zura musu ƙwallo ba,'' kamar yadda Seedorf ya shaida wa Amazon Prime.

"Idan har zan nuna ƙungiya ɗaya da za ta iya ɗaukar kofin Zakarun Turai na bana, to Arsenal ce, musamman saboda tsaron bayan ƙungiyar, babu wata ƙungiya da za ta samu nasarori, idan har ba ta da tsaron baya mai kyau.''

Nasarar doke Atletico da ci 1-0 a ranar Talata shi ne wasa na tara cikin 14 da ƙungiyar ta buga a gasar bana ba tare da an zura mata ƙwallo ba, kuma ƙwallo biyu kawai aka ci su a zagayen wasannin sili ɗaya ƙwale, kuma 30 a duka kakar bana.

Arsenal ta samu damar zuwa wasan ƙarshe cikin sauƙi, bayan da ta doke ƙungiyoyin Bayer Leverkusen da Sporting da kuma Atletico, yayin da PSG ta samu damar bayan doke Monaco da Chelsea da Liverpool da kuma Bayern Munich.

Duk wanda ke son zuwa wasan ƙarshen dai dole ne ya doke ƙungiyoyin da ya haɗu da su, kuma Arsenal ta yi hakan cikin bajinta bayan da ta zama ta farko a teburin teburin ƙungiyoyi 32 da suka tsallaka zagaye na biyu na gasar.

Ta kuma yi wannan bajinta ne bayan doke ƙungiyoyi irin su Bayern da Atletico da kuma Inter Milan.

Wasa 14 da ta buga ba tare da an doke ta ba, shi ne mafi tsawo da ta taɓa yi a tarihin gasar, bayan zarta tarihin da ta kafa a baya na wasa 13 ba tare da an doke ta ba tsakanin watan Maris din 2005 zuwa Afrilun 2026, a lokacin tsohon kocin ƙungiyar Arsene Wenger, wanda suka kai wasan ƙarshe suka yi rashin nasara a hannun Barcelona.

To amma tsaron baya mai kyau ne ya bambanta ƙungiyar yanzu da wadda Arsene Wenger ya jagoranta.

Onuoha ya ce "Akwai manyan dalilai da za a ce Arsenal na da ƙarfin gwiwar lashe kofin bana''.

"sun san salon wasan PSG, waɗanda inda ka bari suka mamaye ka, to ka shiga matsala. Amma Arsenal na da shiri. Saboda sun shirya wa gasar Premier a wannan kaka, kuma hakan ya taimake su, don haka ina ganin za su haifar wa PSG cikas.''

Shi ma tsohon ɗan wasan tsakiyar Manchester United Owen Hargreaves ya ce ''Arsenal na da damar lashe gasar, kuma da wannan tsaron bayan nata komai zai iya faruwa''.

Tsohon ɗan wasan Liverpool Steven Gerrard ya ƙara da cewa: "Na fi kowa sanin cewa wanda ake rainawa sai ya zo ya ci wannan gasa - mu ma mun yi haka a Liverpool bayan doke AC Milan.

"Arsenal za ta kara da babbar ƙungiya mai babban koci, kuma kowane ɗan wasan ƙungiyar na kan ganiyarsa, suna haska ƙungiyar, don haka tana da dama sosai.''

'PSG na da ƙarfin kai hari amma a wasan Arsenal salon zai sauya'

Ba shakka kowa zai yarda cewa Arsenal za ta fuskanci gagarumin aiki a fafatawarta da PSG idan har tana son ɗaukar kofin karon farko

PSg, wadda ke riƙe da kofin Zakarun Turai da ta lashe a bara, ta zira ƙwalla 44 cikin wasa 16 da ta buga a gasar Turai, yayin da ta ci shida daga cikinsu a wasan kusa da ƙarshe da Bayern, wadda ita ta ci 43.

Barcelona ce kawai ta taba cin ƙwallo 45 a wasa 16 a kaka ɗaya tsakanin 1999 - 2000.

Idan aka duba wasan ƙarshe na gasar a shekarar da ta gabata, za a yaba wa PSG wajen doke abokan karawarsu cikin sauri.

Sau ɗai-ɗai ta riƙa zura wa Inter Milan ƙwallo a karawarsu takwas a baya, amma a wasan ƙarshen sai da ta zura mata ƙwallo biyar.

Arsenal ta doke PSG da ci 2-0 a filin wasa na Emirates a gasar bara a matakin zagayen farko, amma ƙungiyar ta Faransan ta rama biki da ci 3-1 gida da waje a wasan zagayen kusa da ƙarshe na gasar ta bara

A yanzu haka Arsenal na fatan rama wannan duka da PSG ta yi mata bara, idan suka haɗu a wasan ƙarshen da za a buga a filin wasa na Puskas Arena da ke ƙasar Hungary.

"Wasan na ƙarshe zai ƙayatar sosa, PSG za ta so ta riƙa kai hare-hare fiye da wasanta da PSG, amma kuma hakan zai ba ta wahala'' in ji Hargreaves.

"Abin sha'awa ne yadda mutane ke kallon Arsenal a ƴan makonnin nan, mutane na tunanin nasarori sun tinkaro ƙungiyar," kamar yadda tsohon ɗan wasan gaban Blackburn Rovers, Chris Sutton ya shaida wa BBC.

"Ƙungiyar na da ƙarfi a yanzu, Arsenal na da dama - za ka iya cewa wasa ne da komai zai iya faruwa 50/50, za ta iya cin kofin za kuma ta iya rashin nasara."

Ƙungiyar ta Arteta ba ta da matsalar zura ƙwallo, ta ci ƙwallo 67 a wasannin Premier League 35 Premier - Inda Manchester City ce kawai da ta ci ƙwallo 69 a wasa 34 ke gabanta.

Abin jira a gani dai a yanzu shi ne ko Arsenal ta Arteta za su iya cire kitse daga wuta a Budapest a karawarsu da ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Turai