Kasuwar hannun jari na hauhawa a duniya saboa yarjejeniyar Amurka da Iran
Rahotanni da ke nuna ana samun ci gaba wajen cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka sun haifar da hauhawar kasuwannin hannayen jari na duniya, tare da saukar farashin mai.
A wani lokaci, farashin ɗanyen mai samfurin Brent ya sauka ƙasa da dala dari a kowace ganga. Farashin makamashi ya rika sauyawa sosai tun bayan fara yakin.
Kamfanonin jiragen sama sun soke jirage dubu goma sha uku a duniya kawo yanzu cikin wannan wata, sakamakon tashin farashin man jiragen sama.
A cewar wakiliyar BBC, ba dukkanin wuraren da jiragen sama ke zuwa abin ya shafa ba, sai dai wasu kamfanonin jiragen sun dauki matakin harhaɗa tafiya sama da guda wuri ɗaya, tare da mayar da hankali kan hanyoyin da suka fi mahimmaci da riba.














