'Hare-haren Isra'ila sun yi ajalin aƙalla mutum 15 a Lebanon'
Kafofin yada labaran Lebanon sun ruwaito cewa aƙalla mutum 15 aka kashe a hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa a kudancin ƙasar.
Isra'ila ta shafe yinin yau tana luguden wuta ta sama a yankin Tyre, inda masu aikin ceto ke ci gaba aikin zaƙulo mutane daga gini-ginen da hare-haren Isra'ila suka rusa.
Isra'ila ta kuma kai hari a garin Sidon, kuma Isra'ila ta ce tana kai hare-haren ne kan Hesbollah. A nata bangaren Hezbollah ta ce ta kai hare-hare kan dakarun Isra'ila da suka mamaye kudancin Lebanon
Majalisar Dattawan Najeriya ta buƙaci a kamo mata tsohon shugaban NNPCL
Asalin hoton, MELEKYARI/NNPC
Kwamitin majalisar dattawa kan bibiyar kashe kuɗaɗen al'umma ya buƙaci jami'an tsaro su kamo tsohon shugaban kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL, Mele Kyari bisa zarginsa da yin kunnen uwar shegu da gayyatar da kwamitin ya masa.
Kwamitin ya buƙaci Kyari da ya bayyana gabansa ne domin amsa wasu tambayoyi a game da binciken da yake kan kuɗi kusan naira tiriliyan 210 da kwamitin ya ce ya kasa fahimtar yadda aka yi da su a zamani shugabancin Kyari a tsakanin shekarar 2017 zuwa 2023.
Asali ofishin babban mai bincike na Najeriya ne ya fara zargin ɓacewar kuɗin, amma tsohon babban jami'in kuɗaɗen kamfanin na NNPCL, Umar Isa ya musanta.
Bayan daɗewa ana tattaunawa a zaman kwamitin ne Sanata Victor Umeh mai wakiltar yankin Anambra ta Tsakiya ya buƙaci kwamitin ya sa a kamo shi, inda nan take mataimakin shugaban kwamitin Sanata Peter Nwaebonyi mai wakiltar Ebonyi ta Arewa ya mara masa baya, inda suka ce rashin amsa gayyatar na ɓata musu lokaci da aiki.
Shi ma tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole mai wakiltar Edo ta Arewa ya ce majalisar dattawa na fuskantar barazanar rasa ƙima idan ba ta yi amfani da ƙarfi ba.
Kotu ta umarci INEC ta yi wa Jam'iyyar Matasa rajista
Asalin hoton, AUDU BULAMA BUKARTI
Kotun tarayya ta umurci INEC ta yi wa jam‘iyyar Access Party da ake kira da Jam'iyyar Matasa ta su Bulama Bukarti rajista.
Wata kotun tarayya wadda da ke zamanta Abuja ce ta bayar da wannan umurnin, sannan ta umarci INEC ta ba jam'iyyar damar ƙarasa rajistarta.
Jagororin jam'iyyar Dr. Audu Bulama-Bukarti da Mevon Samuel ne suka maka INEC a kotu a masanin jam'iyyar, bayan hukumar mai zaman kanta da ƙi amincewa da ita, inda ta kafa hujja da cewa tambarin jam'iyyar ya yi kama da tambarin wata jam'iyyar.
Da yake yanke hukunci, alƙalin kotun Mai shari'a Obiora Atuegwu Egwuatu na kotu a 11 ya ce hukumar ba ta da hurumin hakan, inda ya nanata cewa hukuncin ba daidai ba ne, kuma ya saɓa da shari'a kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 y tsara da kuma sashe na 79 na kundin zaɓe na 2022.
Harin kwanton ɓauna a Kaduna ya yi sanadin mutuwar babban jami’in Sojin Najeriya
Rahotanni daga Najeriya na cewa wani mummunan harin kwanton ɓauna da ake zargin 'yan fashin daji ne suka kai wa dakarun sojin Najeriya a yankin ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna, ya yi sanadiyyar mutuwar wani babban jami'in soji da aƙalla wasu sojoji shida.
Wannan hari ya faru ne yayin da dakarun suke gudanar da sintiri na yau da kullum, wanda ke nuna ƙalubalen da jami'an tsaro ke fuskanta wajen fatattakar 'yan ta'addar da suka daɗe suna addabar al'ummar yankin arewa maso yammacin kasar nan.
A ‘yan shekarun nan, gwamnati da hukumomin tsaro na ƙoƙarin daƙile ayyukan waɗannan ƙungiyoyi, amma hare-haren na ci gaba da faruwa, musamman a yankunan karkara.
Mazauna wasu yankunan sun daɗe suna kira ga a ƙara yawan jami’an tsaro da kuma inganta dabarun yaƙi domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
Ƴanbindiga sun kai hari a makaranta tare da kashe mutum uku a Kogi
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ƴansandan Najeriya, reshen jihar Kogi ta tabbatar da harin da ƴanbindiga suka kai a wata makaranta a jihar Kogi, inda rahotanni suka nuna sun kashe mataimakin shugaban makarantar da wani dattijo mai shekara 70 da ɗalibi mai shekara shida.
A wata sanarwa da ƴansandan suka fitar a ranar Laraba, rundunar ta ce maharan waɗanda ake zargi ƴanbindiga ne sun kai hari a makarantar ne da ke garin Iluke Bunu da nufin far wa ɗalibai masu rubuta jarabawar kammala sakandare da WASSCE.
"Da misalin ƙarfe 10:00 na safe ne rundunar ta samu kirar kar ta kwana cewa an ga ƴanbindiga masu ɗimbin yawa a kan babura kusan 40 sun nufi makarantar gwamnati ta Government
Secondary School da ke garin Iluke Bunu da nufin sace ɗalibai da malaman makarantar."
Ƴansandan sun ce babu wata alamar ɗaliban sun samu nasarar sace ɗaliban makarantar.
Sai dai sanarwar ta ƴansanda ta bayyana cewa an fara bincike domin tabbatar da haƙiƙanin abin da ya faru, "sannan jami'an tsaron haɗin gwiwar sun bi bayan maharan a cikin daji domin kama maharan," in ji rundunar, sannan ta ƙara da cewa an kashe ɗaya daga cikin maharan, sannan jami'in tsaro ɗaya ya samu rauni a lokacin da suke musayar wuta.
Sai dai wata kafar watsa labarai daga jihar ta ruwaito daga wani jami'in gwamnati cewa an sace ɗalibai uku da wasu mutanen garin.
Ya za ka yi idan katin zaɓenka ya ɓace a matsayin ɗan Najeriya?
Asalin hoton, INEC
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta yi kira ga waɗanda katunan zaɓensu suka ɓata ko kuma suka lalace da su nemi a sake musu wani ko maye musu gurbin wanda ya ɓata kafin wa’adin da aka shimfiɗa gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027.
Najeriya za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da gwamnaoni da kuma na majalisun dokokin tarayya da na jihohin ƙasar a farkon shekara mai zuwa.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce samun katin zaɓe mai inganci na da matuƙar muhimmanci ga duk wanda ke son kaɗa ƙuri’a a kowane irin zaɓe.
A cewar sanarwar, hukumar ta ce ana iya yin sabon kati ko maye gurbin wanda ya ɓace ta hanyar ziyartar ofishin INEC na jiha ko na ƙaramar hukuma, ko kuma cibiyoyin rajista da aka amince da su.
Haka kuma, hukumar ta buɗe damar yin rijista ta intanet domin sauƙaƙa wa jama’a samun katin cikin sauƙi da gaggawa.
Hukumar ta kuma sanya ranar 10 ga Yulin 2026 a matsayin ranar ƙarshe da za a karɓi aikace-aikacen yin katin zaɓen.
Tawagar Qatar ta isa Tehran don tattaunawa da jami'an Iran
Tawagar manyan jami’ai daga ƙasar Qatar ta isa birnin Tehran a yau domin tattaunawa da jami’an gwamnatin Iran, kamar yadda kafafen yada labarai na Iran suka ruwaito.
Rahotanni sun ce tawagar ta je Iran ne domin tattaunawa da musayar ra’ayoyi kan huldar ƙasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin.
Jaridar gwamnati ta Iran ta bayyana cewa, a yayin wannan ziyara, za a tattauna sabbin abubuwan da suka shafi ƙoƙarin diflomasiyya na kawo ƙarshen rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran, baya ga batun dangantaka da ci gaban yankin.
Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da aka sake samun musayar wuta tsakanin Amurka da Iran, bayan da Iran ta harbo wani jirgin yaƙin Amurka.
Sa’a guda da ta wuce, shugaban Amurka Donald Trump ya ce Iran za ta ɗanɗana kuɗarta kan jan kafa a tattaunawar zaman lafiya.
A baya Iran ta bayyana cewa za ta dauki mataki kan ci gaba da tattaunawar bayan sabbin hare-haren da Amurka ta kaddamar.
Ƙudurin dokar neman ƙara yawan alƙalan kotu ya tsallake karatu na biyu a majalisa
Asalin hoton, Nigeria Senate
Ƙudurorin dokar da ke neman ƙara yawan alkalan manyan kotunan kasar sun tsallake karatu na biyu a Majalisar Dattawa domin rage cunkoso a harkar shari’a da kuma saurin yanke hukunci.
Ƙudurin ya buƙaci a ƙara yawan alƙalan Babbar Kotun Tarayya daga 70 zuwa 90, sannan a ƙara alkalai a kotun ɗaukaka ƙara daga 70 zuwa 110.
Shugaban masu rinjaye a majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele, wanda ya gabatar da kudurorin, ya ce matakin zai ƙarfafa tsarin shari’a domin fuskantar ƙaruwar shari’o’i cikin sauƙi.
Ya ƙara da cewa dimokuradiyya ba za ta bunƙasa ba idan ba a samun hukunci cikin sauri, don haka dole a samar da isassun kayan aiki da ma’aikata ga ɓangaren shari’a.
Har ila yau, ƙudurin ya kuma tanadi daidaito wajen wakilcin jihohi da Babban Birnin Tarayya a kotun ɗaukaka ƙara, tare da inganta tsarin gudanarwa da aikin kotun.
Iran za ta ɗanɗana kuɗarta kan jan ƙafa wajen tattaunawa – Trump
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ceIran za ta ɗanɗana kuɗarta kan jan ƙafa wajen tattaunawa neman sulhu.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Truth Social, Trump ya zargi Iran da jinkirta cimma yarjejeniya duk da cewa, a cewarsa, yarjejeniyar za ta yi mata amfani.
Trump ya ce “Iran sun ɗauki lokaci mai tsawo wajen tattaunawa kan yarjejeniya mai anfani a gare su, yanzu za su ɗanɗana kuɗarsu."
Wannan bayani na Trump ya zo ne bayan sabon rikici ya ɓarke tsakanin Amurka da Iran, inda suka yi musayar hare-hare biyo bayan harbo wani jirgin sojin Amurka da Iran ta yi a kusa da mashigar Hormuz.
Rahotanni sun ce Amurka ta kai hare-hare kan wasu wuraren sojin Iran a matsayin ramuwar gayya, yayin da Iran kuma ta mayar da martani ta hanyar harba makamai a kan sansanonin Amurka a wasu ƙasashen yankin.
Ƙasar Pakistan ta ƙaddamar da hare-haren sama masu muni a kan iyakarta da Afghanistan, lamarin da ya kawo ƙarshen zaman lafiya na watanni da aka samu a yankin da ke fama da rikici.
Ministan yaɗa labaran Pakistan, Attaullah Tarar, ya bayyana a ranar Laraba cewa an lalata wurare hudu a wani hari da aka yi cikin tsari, wanda ya kashe ‘yan bindiga 26.
Amma gwamnatin Taliban a Afghanistan ta ce hare-haren sun kashe mutane 13, ciki har da yara 11.
Pakistan ta daɗe tana zargin Afghanistan da bai wa ‘yan ta’adda mafaka domin kai hare-hare a cikin ƙasarta, zargin da gwamnatin Taliban ke ci gaba da musantawa.
Wannan sabon rikici shi ne na farko tun watan Fabrairu, lokacin da ƙazamin faɗa a kan iyaka ya yi sanadin mutuwar ɗaruruwan mutane.
Ƙasashen biyu sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Oktoban bara bayan makonni na rikice-rikice masu muni.
Attaullah Tarar ya ce hare-haren sun zo ne a matsayin martani ga “sabbin hare-haren ta’addanci a Pakistan,” inda aka kai farmaki kan wuraren ɓuya da horar da ‘yan bindiga, da kuma wuraren ajiye makamai a yankin iyaka.
Tun bayan ƙazamin rikicin da ya faru a karshen watan Fabrairu, an samu arangama lokaci-lokaci, yayin da shugabannin duniya ke kira ga ƙasashen biyu da su dakatar da faɗa tare da rungumar zaman lafiya.
Muna nazarin ci gaba da tattaunawa da Amurka bayan sabbin hare-hare - Iran
Asalin hoton, Tasnim news agency
Iran ta bayyana cewa za ta sake duba yiwuwar ci gaba da tattaunawa tsakanin ta da Amurka bayan sabbin hare-haren da aka ta kai.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya bayyana hakan bayan sabuwar musayar wuta tsakanin ƙasashen biyu.
Ya ce, “Harkar diflomasiyya ba ta gudana a cikin yanayi mara tasiri ba, domin ci gaba da kowace tattaunawa, dole ne a samu wani dan sarari da zai ba da damar ci gaba da aiwatar da ita.”
Baghaei ya zargi Amurka da “lalata tsarin tattaunawar ta hanyar aika sakonni masu karo da juna da sauya matsaya akai-akai, da kuma karya yarjejeniyar tsagaita wuta sau da dama.”
A safiyar ranar Laraba ne Amurka ta kai hare-haren sama a wasu wurare a kudancin Iran, a matsayin martani ga harbo jirgin yaƙinta da Iran ta yi a tekun Oman.
A gefe guda kuma, sansanin Khatam al-Anbiya ya sanar da cewa sojojin juyin juya halin Iran sun kai hari a kan sansanonin Amurka da ke kasashen Bahrain, Kuwait da Jordan.
'Rukunin farko na 'yan Najeriya da aka kwashe daga Afirka ta Kudu zai isa ƙasar ranar Alhamis'
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta ce ana sa ran rukunin farko na 'yan Najeriya da ake kwashe daga Afirka ta Kudu sakamakon hare-haren ƙyamar baƙi (xenophobia) za su isa ƙasar a safiyar ranar Alhamis.
A wata sanarwa da kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya fitar ranar Laraba, ya ce waɗanda za a kwashe za su tashi daga Afirka ta Kudu ne a daren Laraba.
Ma'aikatar ta ce kamfanin jiragen sama na Air Peace ne zai gudanar da aikin jigilar mutanen, yayin da gwamnatin tarayya ta ɗauki nauyin dukkan kuɗaɗen aikin.
Sanarwar ta tabbatar wa 'yan Najeriya cewa gwamnati, ta hannun ma'aikatu da hukumomin da abin ya shafa, ta shirya dukkan matakan karɓa da tallafa wa waɗanda za su dawo.
Ya ce bayan isowarsu za a yi musu rijista da tantancewa tare da ba su tallafin da ya dace kafin a haɗa su da iyalansu.
Tashin hankali ya ƙaru a Afirka ta Kudu bayan wata ƙungiya da ke adawa da baƙin haure marasa takardu ta buƙaci dukkan baƙi waɗanda ba su da izinin zama su fice daga ƙasar kafin ranar 30 ga Yuni.
Kasashen Ghana da Mozambique sun riga sun kwashe ɗaruruwan 'yan ƙasarsu, yayin da Malawi da Najeriya suka sanar da shirinsu na yin hakan.
Wasu jami’an gwamnatin Amurka sun ce shugaban ƙasar, Donald Trump, bai amince da buƙatar kai wa Iran harin ramuwar gayya ba sai da safiyar ranar Talata, kamar yadda ɗan jaridar Wall Street Journal, Alex Ward, ya ruwaito.
A safiyar ranar Talata, Trump ya shaida wa Jaridar Wall Street Journal cewa harbo jirgin yaƙin Apache da Iran ta yi "ba wani babban al’amari ba ne", domin matuƙan jirgin sun tsira ba tare da sun samu raunuka ba.
Sai dai rahoton ya ce daga baya shugaban ya sauya ra’ayinsa ne bayan Ministan Tsaron Amurka, Pete Hegseth, da shugaban rundunar hafsoshin tsaron ƙasa, Janar Dan Caine, sun ba shi shawarar ɗaukar matakin soja a wani taro da aka gudanar a Fadar White House.
Daga ƙarshe, Trump ya amince da kai hare-hare kan wasu wurare a Iran a matsayin martani ga harbo jirgin yaƙin Apache, a cewar jami’an Amurka.
Rahoton ya kuma ce bayan waɗannan hare-hare, rundunar juyin juya halin Iran da sojojin ƙasar sun ƙaddamar da sabbin hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka da ke yankin.
China ta buƙaci a rage tashin hankali a Gabas ta Tsakiya
Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar China ta bayyana matukar damuwa kan rikice-rikicen da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, tana mai kira ga ƙasashen da abin ya shafa da su kauce wa ƙara dagula al’amura.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Lin Jian, ya ce ya kamata dukkan ɓangarorin su nuna haƙuri da kwantar da hankali, tare da ɗaukar matakai na gaskiya domin rage tashin hankali da gujewa faɗaɗa rikicin.
Kiran na China ya zo ne bayan musayar hare-hare tsakanin Iran da Amurka, lamarin da ya ƙara tsananta damuwa a yankin baki daya.
Iran ta kai harin makamai masu linzami kan sansanonin sojin Amurka uku
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin labarai na Iran sun rawaito cewa rundunar juyin juya halin Musulunci (IRGC) ta kai hare-haren makamai masu linzami kan sansanonin sojojin Amurka guda uku da suka haɗa da Jordan da Bahrain da Kuwait.
Iran dai ta harba aƙalla makamai masu linzami guda huɗu tare da wasu jirage marasa matuƙa da dama zuwa sansanonin sojojin Amurka ɗin.
Wani jami'in Amurka ya tabbatar da harin, yayin da rahotanni suka ce an kai hare-haren ne a matsayin martani ga hare-haren da Amurka ta kai kan wasu wurare a Iran.
A cewar IRGC, hare-haren sun kasance wani ɓangare ne na wata babbar martani inda suka yi iƙirarin kai hari kan wurare guda 21 na sojojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.
Haka kuma rahotanni sun nuna cewa sojojin Jordan sun ce sun kakkabo wasu daga cikin makaman da aka harba, ba tare da rahoton asarar rayuka ko lalacewar dukiya ba.
Kafofin yada labarai na Iran sun kuma wallafa wasu bidiyo da suka ce suna nuna lokacin harin da kuma fashewar da ta biyo baya, amma har yanzu ba a tabbatar da ingancin wadannan bidiyoyin ba daga kafafen labarai masu zaman kansu.
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Aisha Babangida ce za ta sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.