Za a yi sauye-sauye a tsarin shirin NYSC
Majalisar zartarwa ta Najeriya (FEC) ta amince da yin manyan sauye-sauye a tsarin shirin bautar ƙasa na NYSC, ciki har da mayar da shugabancinsa hannun farar hula maimakon sojoji, da kuma tsawaita lokacin atisaye a sansani daga makonni uku zuwa shida.
An cimma wannan matsaya ne a taron FEC na ranar Litinin a Abuja, wanda shi ne karo na farko da aka yi cikakken bita ga shirin tun bayan kafa shi a shekarar 1973.
A ƙarƙashin sabon tsarin, farar hula za su jagoranci harkokin NYSC, yayin da sojoji za su ci gaba da bayar da tsaro ga masu yi wa ƙasa hidima.
Gwamnatin tarayya ta kuma umarci Babban Lauyan Ƙasa da Ma’aikatar kula da ci gaban matasa su gyara dokar NYSC da sauran ƙa’idoji domin bai wa sauye-sauyen cikakken tushe na doka.
Ministan kula da matasa, Ayodele Olawande, ya ce an aiwatar da wannan matakin ne domin inganta NYSC ya koma shiri da ke haɓaka ƙwarewa da samar da damar aikin yi.
Ya ƙara da cewa za a ɓullo da tsarin kiran masu yi wa ƙasa hidima da tura su bisa la’akari da tsaro, tare da mai da hankali kan koyar da shugabanci da kasuwanci da ƙwarewar zamani.