Ƴansanda sun ƙaryata rahoton sakin ɗaliban Oyo

Asalin hoton, @OyoPoliceNG/X
Rundunar ƴansanda a jihar Oyo ta musanta rahotannin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta inda ake zargin cewa ƴanbindiga suk sako ɗalibai da malaman da suka sace a ƙaramar hukumar Orire a jihar Oyo.
Rundunar ta bayyana haka a sanarwar da kakakinta, DSP Ayanlade Olayinka ya sanyawa hannu inda ta ce rahoton ƙarya ce tsagwaranta.
Cikin sanarwar, rundunar ta kuma bai wa al'ummar jihar ta Oyo tabbaci cewa ana ci gaba da ƙoƙari na ganin an kuɓutar da ɗaliban da malaman.
Rundunar ta kuma yi kira ga mazauna jihar da su guji jita-jita su kuma nemi sahihan labarai daga ƴansanda.
Lamarin hare-haren 'yan bindiga da satar mutane don neman kuɗin fansa sun fi ƙamari ne a yankin arewacin Najeriya, inda ba kasafai aka saba ganin hakan ba a kudancin ƙasar, wadda ke fama da matsaloli na tsaro.
A baya-bayan nan ita ma dai jihar ta Oyo na fuskantar matsalar tsaron daga gungun masu aikata laifi.
















