KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 02/05/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 02/05/2026

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Buɗe mashigar Hormuz ba zai daidaita al'amura nan take ba - Starmer

    Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya yi gargaɗin cewa tattalin arzikin ƙasarsa ba ''zai koma daidai ba'', ko da an sake buɗe mashigar Hormuz.

    Yayin wata hira da BBC, Mista Starmer ya ce halin da ake ciki yanzu na buƙatar sabbin salo, domin tunkarar matsalar tattalin arziki da aka riga aka samu sakamakon yaƙin.

    Da aka tambaye game da yiwuwar samun hauhawar farashi sakamkon tashin farashin man fetur, firaministan ya ce gwamnati ba za ta kya hana aukuwar hakan ba.

    ''Muna fuskantar yaƙi har guda biyu'', kamar yadda ya bayyana.

  2. Hare-haren Iran sun lalata mafi yawan cibiyoyin sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya - Rahoto

    jirgin yaki a tsakiyar ruwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani sabon rahoto da kafar yaɗa labaran CNN ta Amurka ta fitar, ya ce hare-haren ramuwar gayyar Iran sun lalata 16 cikin cibiyoyin sojin Amurka 19 da ke yankin Gabas ta Tsakiya, kamar yadda jaridar Indepenpent ta Birtaniya ta ruwaito.

    Wani mutum da CNN ta zanta da shi ya ce ''bai taɓa ganin abu irin wannan ba a baya''.

    Majiyar ta ƙara da cewa an yi amfani da sabbin fasahohin makaman yaƙi na zamani wajen ƙaddamar da hare-haren

  3. Amurka ta sayar da makaman kusan dala biliyan 9 ga ƙawayenta a Gabas ta Tsakiya

    mkm

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar tsaron Amurka ta tabbatar da sayar da makaman soji da kuɗinsu ya kai dala biliyan 8.6 ga ƙawayenta ƙasar da ke Gabas Tsakiya, da suka haɗa da Isra'ila da Qatar da Kuwait da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

    Matakin na zuwa ne yayin da ake cikin mako na uku da fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran.

    Daga cikin waɗannan makaman an sayar wa Qatar na fiye da dala biliyan 4, yayin da aka sayar wa Kuwaita na dala biliyan 2.5, sai kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da ta samu na dala miliyan 147.

  4. Iran ta zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane da take zargi da yi wa Isra'ila leƙen asiri

    Iran ta zartar da hukuncin kisa kan wasu fursunoni biyu kan zargin yi wa Isra'ila leƙen asiri.

    Ma'aikatar shari'ar ƙasar, wadda ta zartar da hukuncin, ta ce kotun kolin ƙasar ce ta tabbatar da hukuncin.

    Ma'aikatar ta ce ɗaya daga cikin mutunen an same shi da laifin haɗa kai da hukumar leƙen asirin Isra'ila Mossad, inda ya riƙa aika mata da muhimman bayanan tsaron ƙasa a lokacin yaƙin ƙasashen.

    Haka kuma ma'aikatar ta ce ɗayan kuma an same shi da laifin zirga-zirga a wurare masu muhimmanci na tsaron ƙasar.

    Inda ta ce ya riƙa aika wa wani jami'in Mossad muhimman bayanai game da wuraren ciki har da Natanz.

    Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da waɗannan zarge-zarge ba.

  5. Trump ya sanar wa Majalisar Amurka kawo ƙarshen hare-hare kan Iran

    Shugaba Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump na Amurka ya rubuta wata wasiƙa ga shugabancin majalisun dokokin Amurka da a ciki yake sake jaddada abin da ya kira ''an kawo ƙarshen hare-hare kan Iran'', wanda hakan ke nufin ba ya buƙatar amincewar majalisar kan yaƙin.

    Dokokin Amurka dai sun yi tanadin cewa dole sai majalisaun dokokin ƙasar sun amince da duk wani matakin soji da ya wuce kwana 60.

    Shugaba Trump ya ce yarjejeniyar tsagaita wuta da ake ciki a yanzu ta kawo ƙarshen hare-hare a watan da ya gabata.

    Duk da wannan yarjejeniya dai ƙasashen biyu na hana jiragen ruwa zirga-zirga a kewayen Tekun Fasha.

    Tun da farko dai Mista Trump ya ce bai ji daɗin buƙatun da Iran ta gabatar wa Pakistan na yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin ba.

  6. Amurka za ta janye dakarunta 5,000 daga Jamus

    sojojin Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta ce za ta janye sojojinta 5,00 daga Jamus sakamakon saɓanin da ke ƙaruwa tsakanin ƙasashen biyu.

    A baya-bayan nan an samu saɓa i tsakanin Shugaba Trump da shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz kan batun yaƙin Iran.

    Ma'aikatar tsaron AMurka ta ce za a kwashe sojojin ne cikin wata shida zuwa 12 masu zuwa.

    Shugaba Trump ya soki Mista Merz da sauran shugaban ƙasashen ƙungiyar Nato kan ƙin tura sojojinsu domin buɗe mashigar Hormuz.

    A ranar Litinin ne shugaban gwamnatin Jmaus ɗin ya ce shugabancin Iran na kunyata Amurka ta hanya sa wakilan Amurak su tashi takanas har Pakistan, domin tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin amma su koma ba tare da wani sakamako ba.

    A cikin wannan mako ne dai Mista Trump ya sanar da janye wasu sojojin ƙasarsa daga ƙasashen Italiya da Sifaniya saboda yaƙin na Iran

  7. Barkanmu da safiya

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiya.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.