Kasuwar 'yan ƙwallo: Makomar Mbappe, Richarlison, Haaland, Jesus, Cavani, Zouma, Witsel, da kuma Barkley

Bayan shekaru 12, Cristiano Ronaldo ya koma tsohuwar ƙungiyarsa wato Manchester United, bayan da ciniki ya faɗa tsakanin United din da Juventus.
Ronaldo ya ci wa United ƙwallaye 118 a watanni 292 kafin ya bar Old Trafford zuwa Real Madrid a 2009.
Sanarwar da Manchester United ta fitar na cewa Ronaldo mai shekaru 36 ya aminta da yarjejeniyar shekara biyu da za ta kawo masa fam miliyan 12.8.
Ciniki tsakanin United da Juventus ya faɗa ne bayan da Manchester City mai maƙwabtaka ta sanar da dakatar da cinikin da ta fara da wakilin ɗan wasan tun da farko.
Anan kuma Paris St-Germain za ta nemi sayen ɗan wasan gaban Everton Richarlison mai shekaru 24, matsawar ta cimma matsaya kan sayar da Kylian Mbappe zuwa Real Madrid in ji jaridar Sky Sports.
Kan wannan batu jaridar Star ta ruwaito cewa Everton za ta nemi fam miliyan 85 kan Richarlison.
Hakama jaridar Sun ta ambato cewa PSG za ta taya dan wasan gaban Manchester City Gabriel Jesus matsawar Mbappe ya bar ƙungiyar.
Akwai kuma rahotannin da ke cewa PSGn na duba yiyuwar taya ɗan wasan gaban Borussia Dortmund Erling Braut Haaland indai Mbappe ya tafi, a cewar Star.
Idan muka sake komawa Manchester kuwa, Sky Sports ta ruwaito cewa Manchester United ba ta da shirin sayar da Edinson Cavani duk da sayen Cristiano Ronaldo.
Jaridar Mirrow ta ambato cewa tsohon mai horar da Manchester United Sir Alex Ferguson ya taka rawa sosai wurin dawowar Ronaldo ƙungiyar a karo na biyu.
West Ham na dab da kammala sayen mai tsaron bayan Chelsea Kurt Zouma, bayan daddale cinikin kan fam miliyan 25, in ji jaridar Mirror.
Sevilla ta ce Chelsea na jan ciki wurin sayen mai tsaron bayanta Jules Kounde mai shekaru 22, in ji jaridar Football Espana.
Akwai yiyuwar Chelsea ta sayar da Ross Barkley da Danny Drinkwater don ta samu rarar kudi kafin a rufe kasuwa ranar Talata mai zuwa, kamar yadda jaridar Sun ta wallafa.
Ita kuwa Aston Villa ta nuna sha'awar sayen ɗan wasan tsakiyar Borussia Dortmund Axel Witsel mai shekaru 32, kamar yadda Tuttosport ta ce.
A ƙarshe jaridar Football London ta ruwaito cewa Arsenal na shirin sayar da matasan yan wasanta Miguel Azeez mai shekaru 18, da kuma Ryan Alebiosu mai shekaru 19 zuwa Portsmouth da Sunderland.











