Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dodannin raga – Ƴanwasan da ake sa ran za su fi zura ƙwallo a 2026
Kylian Mbappe ya kasa yin murmushi a lokacin da yake karɓar ƙyautar takalmin zinare bayan kammala gasar kofin duniya a Qatar a 2022.
Tawagar Faransa ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Argentina, duk da cewa ya ci ƙwallo uku rigis a ranar. Cin ƙwallaye ba sa tabbatar da lashe kofi, amma suna da tasiri ga wanda ya zura su a raga da yawa a kowacce gasa.
Da yake daf ake da fara gasar cin kofin duniya ta bana da za a buga a Amurka da Canada da kuma Mexico, mun yi duba na tsanaki kan siffofi da halayyar da suke zama ruwan dare ga waɗanda ke lashe takalmin zinare da kuma nazari kan ƴan wasan da ake ganin za su iya zama kan gaba wajen yawan zura ƙwallaye a raga a gasar 2026.
Yawanci ba a samun ƴan wasa masu shekaru da yawa suna lashe ƙyautar
Wani labari mara daɗin ji ga Harry Kane shi ne - A tarihi da ƙyar ne a bana idan mai shekara 30 ko fiye da haka zai lashe takalmin zare a gasar ta kofin duniya. history suggests it is unlikely the 2026 Golden Boot will be won by somebody aged 30 or above.
It has only happened once, when Davor Suker scored six goals aged 30 at France '98 as Croatia took third place in their first World Cup since gaining independence.
Suker is the exception to the rule. On average Golden Boot winners are 24.7 years old. Mbappe brought the average slightly down in 2022, the 24-year-old beating 35-year-old Lionel Messi's tally by just one goal.
The record for the youngest player to claim the Golden Boot - which 18-year-old Lamine Yamal might have eyes on - is held by Hungarian Florian Albert, who was one of six joint-winners at Chile 1962 at 20 years and eight months old.
Ba za ka iya lashe ƙyautar kai kaɗai ba sai da abokan wasan ka
Ɗan wasan da zai yi nasara yana buƙatar abubuwa biyu—kyakkyawan tsarin kai masa ƙwallaye, sannan tawagarsa ta yi nisa a gasar cin kofin duniya.
Saboda haka ba abin mamaki ba ne cewa Brazil, wacce ta lashe kofin duniya sau biyar, ta halarcin gasar bana da ƴan wasan gaba shida da suka fi yawan zura kwallaye a bana a gasar lik da suka buga a kakar nan da ta wuce.
Wanda ya fara lashe ƙyautar takalmin zinare a tawagar Brazil a gasar kofin duniya shi ne Leonidas a 1938, yayin da na ƙarshe kuma ya kasance Ronaldo a 2002.
Zura ƙwallaye da yawa a matakin wasannin cikin rukuni, yana da muhimmanci ga masu neman lashe ƙyautar, amma idan tawagarka ba ta wuce matakan zagaye na biyu ba, hakan na rage maka damar lashe kyautar matuka duk da tarin ƙwallayen da za a ci.
Hakan ya faru da Cristiano Ronaldo a Rasha 2018, inda ya ci kwallaye huɗu a fafatawar cikin rukuni, amma Portugal ta fice a zagaye ƴan 16. A gefe guda kuma, Harry Kane ya zura shida a raga a wasannin, yayin da Ingila ta kai har wasan kusa da na ƙarshe.
Yana da ƙyau ka fara da cin ƙwallaye da yawa a ƙungiyarka a kakar, kafin fara gasar kofin duniya
Thomas Müller bai taɓa zura ƙwallo ba kafin ya isa Afirka ta Kudu, domin buga wa Jamus gasar cin kofin duniya a 2010.
"Na yi sa'a kawai, na dace da lokaci mai kyau ina kan ganiya," in ji Müller bayan da ya kammala gasar da ƙyautar takalmin.
A kakar Bundesliga a 2009–10, Müller ya yi tunanin Bayern Munich za ta iya bayar da shi aro ko ma sayar da shi gaba ɗaya. Amma zuwan Louis van Gaal ya canja komai, inda nan take ya zama ɗan wasa na farko a cikin tawagar.
Ya ciƙkwallo 13 tare da bayar da 11 aka zura a raga, yana buga dukkan wasannin da Bayern ta yi a kakar da ta lashe Bundesliga, wanda ya sa ya isa gasar cin kofin duniya a 2010 a kan ganiya, bayan nasarori da ƙungiyarsa ta yi.
Labarinsa yana daga cikin irin tsakanin waɗanda ke lashe takalmin zinare. Kawai sau biyu ne a tarihi wani ɗan ƙwallo daga gasar cikin gida da ba su kare a ƴan huɗun farkon teburi ba, suka lashe ƙyautar takalmin zinare a gasar cin kofin duniya a tarihi.
Ka zama ɗan wasa mai ƙwazo a kowanne gurbin fili
Müller ya doke ƙwararrun ƴan wasa wajen lashe kyautar a 2010—amma da ɗan kankanin bambanci sosai.
Matashin ɗan ƙwallon mai shekara 20 da Diego Forlán na Uruguay sun zura kwallo guda-guda a wasan neman matsayi na uku, wanda hakan ya daidaita su da David Villa na Spain da Wesley Sneijder na Netherlands, dukkan su suna da ƙwallo biyar a raga.
Villa da Sneijder sun samu damar ƙara cin kwallo a wasan karshe a Johannesburg a 2010, domin lashe Golden Boot, amma babu wanda ya ci ƙwallo. Saboda haka aka koma amfani da ƙarin ƙididdiga domin raba musu ƙyautar.
A nan ne aka bambanta su ta hanyar adadin bayar da ƙwallao a zura a raga da kowanne ya yi, inda Müller ya samu uku, hakan ya ba shi fifiko ya lashe kyautar. takalmin zinare
Idan kuma har ƴan wasa biyu ko fiye da haka sun zura ƙwallo a raga iri ɗaya da bayarwa a zura a raga duk iri ɗaya, FIFA tana amfani da wata doka—wanda ya buga mintuna marasa yawa a gasar, shi ne ke lashe Golden Boot.
Su wa ake sa ran za su iya lashe takalmin zinare a gasar 2026?
Ba a taɓa samun wanda ya lashe ƙyautar takalmin zinare a gasar cin kofin duniya sau biyu ba—amma akwai ƴan wasa biyu da ke da wannan damar a bana da za su iya karya wannan tarihi.
Kylian Mbappé ya zura ƙwallaye huɗu a wasan share fagen shiga gasar kofin duniya, kuma kasancewar Faransa na cikin ƙasashen da ake ganin suna da ƙarfi sosai da tarin fitattun ƴan ƙwallo, akwai yuwuwar tawagar za ta kai matakin wasan ƙarshe. Wannan na nufin Mbappé zai samu damar lashe ƙyautar da zarar an ci ƙwallaye da yawa, wanda shi ne ya lashe takalmin zinare a Qatar a 2022.
Wani ɗan wasa kuma da ke neman kafa tarihi shi ne Harry Kane. Yana da shekara 32—wanda yake da tarin shekaru tsakanin waɗanda suka lashe takalmin zinare a gasar kofin duniya, amma ƙwallaye 54 da ya zura a raga a wannan kakar da ta wuce a Bayern Munic, Kane ya zama wajibi a saka shi a sawun gaba cikin ƴan takarar lashe takalmin zinare a gasar kofin duniya a bana. Idan har tawagar Ingila karkashin koci, Thomas Tuchel ta yi nisa a gasar bana, ana sa ran Kane ne zai yi musu namijin kokarin cin ƙwallaye da yawa. Ya karɓi ƙyautar a 2018 a Rasha
Lionel Messi ya lashe ƙyaututtuka da dama a rayuwarsa ta tamaula, amma har yanzu yana da wani gibi mai suna ƙyautar takalmin zinare a cikin tarihin nasarorinsa a gasar kofin duniya, duk da yana da Ballon d'Or takwas. Yana da shekara 38, kuma zai buga gasar kofin duniya a 2026 karo na shida jimilla, ita ce dama ta ƙarshe da zai iya ƙoƙarin cike wannan gibi.
A gefe guda kuma, matashin ɗan wasa, Lamine Yamal zai cika shekara 19 kafin kammala gasar. Tawagar Sifaniya ba ta wuce zagayen ƴan 16 tun bayan nasarar lashe kofin duniya a 2010, sai dai kuma tawagar da koci, Luis de la Fuente ke jan ragama ta nuna ƙarfi sosai a Euro 2024 da ta lashe a Jamus, kuma ta yi fice a wasannin share fagen shiga gasar cin kofin duniya, wanda ke nuna za ta iya yin nisa a wannan gasar.
Erling Haaland, wanda ya lashe ƙyautar takalmin zinare a Premier League a kakar da ta wuce, ya zura ƙwallo 26 a gasar lig a Manchester City. Duk da haka, damar sa ta lashe Golden Boot a duniya na iya dogara da yadda Norway za ta nisa a gasar bana. Haaland ya zura ƙwallo 16 a wasanni takwas a share fagen shiga gasar cin kofin duniya, abin da ke nuna ƙwazonsa a gaban raga.
Ɗan wasan da ya fi kowa zura ƙwallaye a raga sama da 100 tsakanin ƙungiyoyi huɗu daban-daban, kuma bayan kakar wasan da ya cimma buri a bana a gasar Saudi Arabia, Cristiano Ronaldo zai shiga wasannin bana da burin lashe takalmin zinare da ɗaukar kofin duniya da bai taɓa yi ba, duk da cewa yana da shekara 41.
Duk da cewa tarihin Portugal a gasar cin kofin duniya ba wani mai yawa ta kafa ba—inda sau ɗaya aka yi waje da ita a zagaye na biyu a 2006 - amma tana da tawaga mai karfi da inganci da ya haɗa da Bruno Fernandes ƙyaftin ɗin Manchester United, wanda ya shahara da bayar da ƙwallaye a zura a raga, kuma hakan zai ba su damar kai wa wasan karshe a bana.
A gefe guda, duk da rikice-rikicen da Real Madrid ta fuskanta musamman a kakar da aka kammala, Vinícius Júnior mai shekara 25 ya ci ƙwall0 21 tare da bayar da 14 aka zura a raga a dukkan fafatawa. Sai dai Brazil ta kare a matsayi na biyar a wasan share fagen shiga kofin duniya daga Conmebol, kuma da har yanzu tana ɗora buri kan tsofaffin ƴan wasanta, akwai yiwuwar Vinícius zai ci karo da ƙalubale wajen samun cikakkiyar damar lashe takalmin zinare a bana.
Ousmane Dembélé ɗan wasan tawagar Faransa, bai yi kokari sosai a bana ba kamar yadda ya yi a 2024–25 ba, amma duk da haka ya ci ƙwallaye 19 a dukkan karawar da ya yi wa Paris Saint-Germain. Faransa na da tarin ƙwararrun ƴan wasan gaba, amma duk da haka Dembélé yana da gurbi, sannan zai taka leda tare da Mbappe da kuma yin gogayya da shi a fatan lashe takalmin zinare.
Argentina kuwa tana da ƙarin ƴan wasa biyu da za su iya yin takara—Lautaro Martínez da Julián Álvarez. Martínez ya ci ƙwallo biyar da ta kai ya lashe ƙyautar takalmin zinare a Copa América a 2024, yayin da Álvarez ke daga cikin manyan ƴan gaba da ake nema a Turai ruwa a jallo, bayan kakar da yake taka rawar gani a Atlético Madrid.
Za a iya samun waɗanda ba a yi tsammani ba
Waɗannan su ne ƴan ƙwallon da ake ganin za su fi samun nasara kai tsaye wajen lashe ƙyautar, amma kada a yi mamaki idan wasu suka fito ba za to ba tsammani wajen takarar lashe takalmin zinare a gasar kofin duniya 2026.
Bayan da tawagar Sifaniya ta ɗauki Euro 2024, Mikel Oyarzabal, ya zura ƙwallo a kusan dukkan wasannin share fagen shiga gasar cin kofin duniya a tawagar, sau ɗaya kacal ne da bai zura ƙwallo ba a raga. Haka kuma ya ci ƙwallo 15 a La Liga a wannan kakar da ta wuce. Idan har bai samu matsala ta rauni ba, yana da damar cin ƙwallaye masu yawa musamman tare da Lamine Yamal da Nico Williams da ke ba shi damar samun zura su a raga a kai a kai.
Alexander Isak kuma na iya amfana daga hutun da ya yi, bayan fama da doguwar jinya da ya hana shi taka rawar gani a Liverpool a kakarsa ta farko a bana, wanda zai wakilci Sweden tare da Viktor Gyökeres, wanda ya yi kokari a kakar nan a Arsenal.
Raphinha shi ma ya yi fama da jinya a lokuta da yawa, amma har yanzu yana da tasiri a gurbin kai hare-hare sosai kuma ana sa ran zai taka leda a tawagar Brazil tare da Vinícius da Igor Thiago, wanda shi ma ake ganin zai iya zama ɗan takarar takalmin zinare a gasar ta kofin duniya.
Michael Olise zai shiga gasar bana ne, bayan cin ƙwallaye 22 a dukkan fafatawa a Bayern Munich a kakar da aka kammala. Duk da cewa shi ya fi shahara wajen bayar da ƙwallaye a zura a raga mai 30 a bana, sai saboda yawan damar da Faransa ke sumu a wasanninta zai iya zama cikin masu takarar ƙarbar ƙyautar takalmin zinare a bana.
A ƙarshe, akwai Romelu Lukaku—wani tsohon ɗan wasa ƙwararre daga tawagar Belgium, ya shahara wahen cin ƙwallaye da samar da damar cin ƙwallaye a wasanni da yawa, kuma mai taka leda a Napoli babu mai iya dakatar da shi idan har yana kan ganiya, domin yana da karfi ga sa jiki ga cin ƙwallaye ga samar da damar maki, suna kuma da fitattun ƴan wasa.