Atiku da Kwankwaso: Abokan tafiyar siyasa da suka raba gari

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

A daidai lokacin da ake cigaba da shirye-shiryen babban zaɓen 2027, siyasar arewacin Najeriya ta ɗauki zafi ne kan muhawarar da ake tafkawa game da Atiku Abubakar da Rabiu Musa Kwankwanso.

Magoya bayan fitattun ƴan siyasar na arewa suna ta musayar yawu ne kan wane ne ya fi girma da ƙarfi da tarin masoya da ma gogewa a siyasar, da kuma tunanin wanda ya fi girma a siyasar ƙasar.

A watannin baya ne magoya bayan ɓangarorin biyu suka fara murna bayan jagororin siyasar biyu sun dunƙule a jam'iyyar ADC domin fuskantar APC, amma sai auren ya ƙi daɗi, inda suka rabu bayan lokaci kaɗan.

Atiku Abubakar dai shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC, inda ya samu jimillar ƙuri'a 1,846,370, inda ya kayar da sauran ƴan takara biyu - Rotimi Amaechi wada ya samu jimillar ƙuri'u 504,117, sai Muhammed Hayatudden a matsayi na uku da jimillar ƙuri'u 177,120.

Shi kuma Rabiu Musa Kwankwanso shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam'iyyar NDC, ina zai mara wa Peter Obi baya domin fafatawa da jam'iyyar APC mai mulki da ADC da sauran jam'iyyu a babban zaɓen na 2027.

Amma me ya sa magoya bayan ƴansiyasar biyu suke takun-saƙa? kuma me yake haɗa su?

Shin tare suka fara siyasa?

Dangantakar siyasa tsakanin Atiku Abubakar da Rabiu Musa Kwankwaso ta daɗe, domin sun shafe sama da shekara 30 suna gwagwarmayar siyasa, lamarin da ya sa ake tunanin ya kamata su kasance makusantan juna a siyasa..

Duk da cewa a wasu lokuta sun kasance a jam'iyyu daban-daban ko kuma sun kara da juna a zaɓe, asalinsu na siyasa ya samo asali ne daga tafiya guda ƙarƙashin marigayi Shehu Musa Yar'Adua.

A zamanin mulkin soji na Janar Ibrahim Babangida ne da aka fara shirye-shiryen komawa dimokuraɗiyya ta Jamhuriya ta uku, Shehu Musa Yar'Adua ya kafa ƙungiyar siyasa ta People's Front of Nigeria, wadda ta kasance ɗaya daga cikin ƙungiyoyin siyasa mafi ƙarfi a wancan lokaci.

Atiku da Kwankwaso dukkansu sun kasance cikin fitattun mambobin wannan ƙungiya tare da wasu ƴan siyasa, waɗanda yawancinsu daga baya suka mamaye siyasar Najeriya.

A lokacin an samu cikas saboda gwamnati ta ƙi yi wa People's Front rajista a matsayin jam'iyyar siyasa, wanda hakan ya sa mambobinta da dama suka shiga jam'iyyar SDP domin shiga zaɓen 1992.

A zaɓen shekarar 1992, Kwankwaso ya lashe kujerar majalisar wakilai, inda ya zama mataimakin shugaban majalisar. A gefe guda kuma, Atiku ya fara da takarar gwamna sannan daga baya ya nemi tikitin takarar shugaban ƙasa na SDP a shekarar 1993, inda ya fafata takarar fitar da gwani, amma Abiola ya doke shi.

Zamanin fadama zuwa PDP

Bayan rushewar Jamhuriya ta uku sakamakon soke zaɓen da ya yi fice da zaɓen 12 ga Yuni, Atiku da Kwankwaso sun ci gaba da kasancewa cikin tsarin siyasar da ya samo asali daga People's Front. Daga baya suka shiga People's Democratic Movement (PDM), wata ƙungiya da ta taka muhimmiyar rawa wajen fafutukar dawo da mulkin dimokuraɗiyya.

Da aka dawo mulkin farar hula a shekarar 1999, su biyun suka kasance cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar PDP.

A zaɓen na 1999, Atiku da Kwankwanso sai suka tsaya takarar kujerar gwamna, inda Atiku lashe zaɓen gwamna jihar Adamawa, shi kuma Kwankwanso ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano.

Sai dai shi Atiku bai yi gwama ba, saboda zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na lokacin, Olusegun Obasanjo ya zaɓe shi a matsayin mataimakin shugaban ƙasa., yayin da Kwankwaso ya zama Gwamnan Jihar Kano.

Atiku ya yi shekara takwas a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, shi kuma Kwankwanso ya yi shekara huɗu a gwamna, aka kayar da shi, amma daga bisani ya zama ministan tsaro. Amma dukkansu suna PDP tare.

Fara raba-gari

Bayan kammala mulkin Obasanjo, sai ya ayyana marigayi Umaru Musa 'Yar'adua matsayin wanda yake so ya gaje shi.

Lamarin da ya sa Atiku, wanda suka daɗe ba sa ga maciji da shugaban ya fice daga PDP a karon farko, ya koma AC wato Action Congres, inda ya haɗu da shugaban ƙasar na yanzu Bola Tinubu domin tsayawa takarar shugaban ƙasa. A ACn ne ya fafata da ƙanin tsohon maigidansa na siyasa.

A lokacin shi kuma Kwakwaso yana PDP, inda ya tsayar da Ahmed Bichi takara domin fafatawa da Ibrahim Shekarau, amma Shekarau ya samu nasara.

A zaɓen 2011, Atiku Abubakar ya sake komawa PDP domin tsayawa takara, inda ya fafata da shugaban ƙasa na lokacin, Goodluck Jonathan, amma bai samu nasarar samun tikitin ba.

Shi kuma Kwankwanso sai ya sake tsayawa takarar gwamna, ida aka yi taken 'dawo-dawo', inda ya samu nasarar sake lashe zaɓen gwamnan jihar Kano a karo na biyu.

A lokacin da ake shirye-shiryen zaɓen shekarar 2015 ne, Atiku da Kwankwaso suka sake haɗuwa a jam'iyyar haɗaka da APC domin fuskantar tsohuwar jam'iyyarsu ta PDP da ɗan takararta, Jonathan.

A zaɓen fitar da ƴantakarar APC, marigayi Muhammadu Buhari ya zo na ɗaya, Kwakkwaso ya zo na biyu, sannan Atiku ya zo na uku. Amma sai suka haɗu suka mara wa Buhari baya, inda suka samu nasarar doke Jonathan.

A zaɓen 2019 ma sun sake komawa PDP, inda suka fafata zaɓen fitar da gwani a Fatakwal. A zaɓen Atiku ne ya samu nasara, inda Kwankwanso ya zo na huɗu.

A zaɓen 2023 kuma, Kwankwaso ne ya fice daga PDP, inda ya shiga jam'iyyar NNPP ya tsaya takarar shugaban ƙasa, sannan ya tsayar da ɗan takarar gwamna a Kano.

Da gaske akwai takun-saƙa?

Alwan Hassa, ɗan siyasa ne na tsagin jam'iyyar APC, wanda ya daɗe yana bibiyar siyasar Atiku da Kwankwanso da ma arewacin Najeriya, ya ce jagororin siyasar sun daɗe tare, inda ya yi iƙirarin cewa "Atiku ya taka rawa a lokacin da Kwankwao ya zama mataimakin shugaban majalisa a Jamhuriya ta uku."

"Inda aka fara samun matsala shi ne lokacin da gwamnoni suka taru suka mara wa Atiku baya domin ya yi takara, amma sai Kwankwaso ya ce ya kamata a ba Obasanjo dama ya sake tsayawa takara ko ku a ji daga gare shi. Wannan maganar ba ta yi wa Atiku daɗi ba a lokacin," in ji Alwan.

Alwan ya ƙara da cewa zaɓen fitar da gwani na APC da aka yi a 2015, "Kwankwaso ne ya zo na biyu bayan marigayi Muhammmadu Buhari, Atiku ya zo na uku. Wannan lamarin bai yi wa Atiku daɗi ba, shi kuma Kwankwaso ya yi farin ciki. Sannan ko a zaɓen 2019, ana tunanin Kwankwaso bai taimaka wa Atiku ba wajen samun ƙuri'a," in ji shi.

Za su iya zama a inuwa ɗaya?

Kabiru Sufi, masanin siyasa ne, kuma mai sharhi kan harkokin siyasa ya ce akwai abubuwa biyi muhimmai a suke tsaiko wajen zaman ƴansiyasar guda biyu a inuwa ɗaya.

"Na farko dai duk da kasancewar idan aka duba tarihi ƴan gidan siyasar gida ɗaya ne wato gidan fadama kuma ƴan taɓo ne, amma da aka shiga mulkin Obasanjo, sai su Kwankwaso da wasu ministoci irin su Nasir El-Rufai suka zama na hannun damar Obasanjo a lokacin a Atiku da Obaanjo suna takun-saƙa."

Masanin siyasar ya ƙara da cewa abu na biyu mai muhimmanci shi ne dukkan ƴan siyasar biyu yanzu burinsu ɗaya ne.

"Tun bayan da Atiku ya yi zango biyu na mataimakin shugaban ƙasa, shi kuma Kwankwaso ya yi gwamna biyu, sai ya zama dukansu buƙatarsu kusan ɗaya ce. Yanzu dukansu burinsu zama shugaban ƙasa ne, shi ya sa yake da wahala su haɗu a waje ɗaya, har gara Kwankwaso ma zai iya zama mataimakin shugaban ƙasa."

Sufi ya ƙara da cewa magoya baya na tasiri sosai a siyasar jagororinsu, "saboda kowannensu magoya bayansu ba sa fahimtar juna, har sukan jefi juna da maganganu. Su kan su jagororin sukan yi gugar zana a tsakaninsu," in ji Kabiru Sufi.