Wace ƙungiya ce za ta lashe gasar Champions League ta bana?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Gasar Champions League ta sake dawowa - wa zai lashe wannan shahararren kofin a birnin Madrid a ranar 5 ga watan Yunin shekara mai zuwa?

Ƙungiyar Paris St-Germain na da burin lashe kofin a karo na uku a jere yayin da ake fara matakin rukuni na gasar a ranar Talata.

Ƙungiyoyi biyar daga Ingila za su yi ƙoƙarin hana su nasarar, inda ake ganin Arsenal ce ke da damar ƙarasa abin da ta fara a kakar da ta gabata inda ta zo ta biyu.

Mun tambayi ƙwararru kan harkokin ƙwallon ƙafa, Julien Laurens da Guillem Balague, ra'ayinsu game da wanda zai lashe gasar, sannan muka yi nazari kan abin da alƙaluman ƙididdiga suka nuna.

Su waye ake ganin za su yi nasara?

Julien Laurens:

Idan PSG ta yi nasarar lashe kofin sau uku a jere, hakan zai zama babban abin alfahari da ban mamaki. Ba na tsammanin za su iya cimma hakan. A ganina, lashe kofin sau biyu a jere ma babban abu ne—amma sau uku a jere abu ne mai matuƙar wahala, sai dai idan kana da Cristiano Ronaldo a cikin tawagarka, alhali su ba su da shi.

Ina ganin za su yi ƙoƙari sosai har su kai ga matakin kusa da na ƙarshe (semi-final), amma ina ganin ƙalubalen lashe kofin sau uku a jere yana da wuyar gaske.

Ban gama amincewa da shirin Jose Mourinho a Real Madrid ba, don haka ina ganin Bayern Munich da Arsenal ne za su kai ga wasan ƙarshe. Wataƙila su ne ƙungiyoyin da suka fi cancantar kasancewa a wannan matakin a shekaru biyun da suka gabata, bayan PSG.

Idan ana batun wadda za ta lashe kofin, zan zaɓi Arsenal. Suna da mafi kyawun tsarin tsaron gida a Turai baki ɗaya, kuma hakan shi ne babban abin da ke ba ƙungiya damar lashe kofuna. Ina hasashen PSG za ta kai matakin ƙungiyoyi huɗu na ƙarshe, Bayern ta zo ta biyu, sannan Arsenal ta lashe kofin.

Guillem Balague:

Ganin yadda PSG ta fara kakar wasan bana cikin rashin tabbas, muna ganin irin wahalar da ke tattare da ci gaba da riƙe matsayin ƙoli. Luis Enrique na ci gaba da ingiza ƴan wasan su ci gaba da kasancewa a matakin ƙololuwa a fagen ƙwallon ƙafa kuma hakan na tattare da ƙalubale.

Kasancewar ana kallon matakin farko na gasar a matsayin lokacin gwaje-gwaje da kuma shirye-shirye don fuskantar ɓarin ƙarshe na kakar wasa, za a ga cewa an samu sauye-sauye da dama wanda hakan zai haifar da sakamako masu ban mamaki da rashin tabbas kafin a shiga muhimmin lokacin gasar daga watan Janairu zuwa gaba.

Kasancewar an riga an kafa ginshikin ƙungiyar, ina sa ran za su yi matuƙar kusa da sake lashe gasar.

Amma Barcelona sun kama hanyar komawa kan ganiya. Suna buƙatar ƙarin ɗan wasan baya da kuma dan wasan gaba (lamba tara). Wannan shi ne abin da Hansi Flick ke so domin ya kai ƙungiyar zuwa mataki na gaba, duk da cewa yana ganin tuni suna kan hanyar komawa kan matakin ƙololuwa a fagen wasa.

Arsenal ta samu sa'ar lashe wasanni akai-akai, kuma wannan yana rage matsin lambar da ke kan ƴan wasan, yana kuma ba su damar yin wasa cikin kwanciyar hankali.

Ya kamata waɗannan ƙungiyoyi uku su kai matakin kusa da na ƙarshe (semi-final) sai dai idan sun haɗu da juna kafin lokacin. Ƙungiya ta huɗu kuma—idan jadawalin wasa ya ba da damar hakan—ya kamata ta kasance Bayern Munich, Real Madrid ko Manchester City.

Wadanne ƴan wasan ne ake ganin za su haska a gasar bana?

Julien Laurens:

Na zaɓi ƴan wasa biyar da ya kamata a sanya ido a kansu a gasar Champions League ta wannan shekarar. Na farko shi ne Jude Bellingham. Wannan babban lokaci ne a gare shi, kasancewar zai taka muhimmiyar rawa a ƙungiyar Real Madrid ƙarkashin jagorancin Mourinho, musamman a matsayin mai buga lamba 10, matsayin da nake ganin ya dace da shi sosai. Bayan ya taka rawar gani a gasar cin kofin duniya, ina ganin zai ci gaba da kasancewa cikin wannan kyakkyawan yanayi. Ina sa ran zai zura ƙwallaye da yawa, kuma ya kasance mai taka muhimmiyar rawa wajen yanke hukunci kan makomar wasa.

Nico Paz, wanda ke sanye da riga mai lamba 10 a ƙungiyar Como, shi ne ginshikin duk wani motsi da suke yi da ƙwallo. Wannan shi ne karon farko da suke shiga gasar Champions League. Cesc Fabregas ne kocinsu, don haka ƙungiya ce mai ban sha'awa da kuma ƙayatarwa wajen kallo. Paz matashin ɗan wasa ne na musamman—wanda har yanzu yake ci gaba da bunƙasa—amma nan ba da jimawa ba zai zama babban ɗan wasa.

"Mr Champions League" – Khvicha Kvaratskhelia. A shekaru biyun da suka gabata, ya nuna bajinta ta musamman, musamman a kakar wasan da ta gabata a ɓangaren hagu na fili, inda yake da ikon shiga tsakiyar fili ko kuma ya ci gaba da tafiya ta gefe; yana da barazana sosai ta hanyar amfani da ƙafarsa ta dama da ta hagu, ya zura ƙwallaye masu ban sha'awa, kuma yana da ƙwarewa ta musamman wajen sarrafa ƙwallo. Ina ganin yana ɗaya daga cikin waɗanda za su iya lashe kyautar Ballon d'Or.

Ƙungiyar Lens ta dawo gasar Champions League bayan ta yi gwagwarmaya sosai da PSG a kakar bara a gasar Ligue 1, kuma ana iya cewa Ismaelo Ganiou ne ɗan wasansu mafi kyau. Shi ɗan wasan baya ne na tsakiya mai ƙarfi, matashi mai shekara 21, wanda ya ƙware wajen sarrafa ƙwallo, kuma yana da matuƙar sauri da ƙarfin jiki. Ina tsammanin zai bar ƙungiyar a ƙarshen kakar wasa domin komawa wata babbar ƙungiya a gasar Premier League.

Tun bayan barin Aston Villa zuwa Roma, Donyell Malen ya nuna bajinta ta musamman, inda yake cin aƙalla ƙwallo ɗaya a kusan kowane wasa a matsayin ɗan wasan gaba ɗaya tilo a ƙungiyar Gian Piero Gasperini. Dawowar Roma gasar Champions League abu ne mai kyau, kuma ƙungiya ce da ta sake zama mai ƙayatarwa wajen kallo. Ina ganin za mu sake ganin Malen yana taka leda a matakinsa mafi girma.

Guillem Balague:

Ɗan wasan gaba na Bayern Munich, Harry Kane, na fafutukar ganin ya lashe kyautar Ballon d'Or. Ya cancanci kasancewa cikin masu takarar, kuma ba na tsammanin zai rage ƙwazonsa tunda salon wasan Bayern ya dace da shi sosai.

Matashin ɗan wasa Lamine Yamal yana da burin samun ƙarin nasarori kuma ya sa ido kan gasar Champions League. Hansi Flick yana son ƙungiyar da ke tsare ragarta daga gaba tare da nuna ƙwazo, hakan zai ba shi damar nuna bajintarsa.

Khvicha Kvaratskhelia ya kai wani sabon mataki na ƙwarewa, kuma yayin da PSG ke ci gaba da samun nasara a gasa, zai sake ceto ƙungiyar tare da lashe manyan wasanni. Nan ba da jimawa ba zai lashe kyautar Ballon d'Or.

Ƙungiyar Shakhtar tana da dogon tarihi na mayar da ƴan wasan Brazil zuwa manyan taurarin ƴan wasa da ake sayarwa kan maƙudan kuɗaɗe a Turai, kuma matashi mai shekara 20, Kaua Elias, na iya zama kan gaba a jerin waɗannan ƴan wasan.

Bayan shekarar da ta gabata ta kasance mai cike da ƙalubale da raunuka ga Martin Odegaard, ya fara wannan kakar cikin nasara. Ɗan wasan na ƙasar Norway yana da ikon sarrafa wasanni, kuma ƙungiyarsa - wadda yanzu ke da ƙarin ƙwarin gwiwa - za ta buƙaci ya ci gaba da yin hakan. Da alama yana shirye ya ɗauki nauyin da ke tattare da shugabancin ƙungiyar.

Mene ne alƙaluma ke cewa?

A cewar kamfanin ƙididdiga ta Opta, ƙungiyar Arsenal—wadda ta zo ta biyu a kakar bara—ita ce kan gaba wajen hasashen lashe gasar Champions League (da kashi 20.4), duk da cewa Bayern Munich (wadda PSG ta doke a matakin kusa da na ƙarshe a baya) tana biye da ita (da kashi 20).

Damar da PSG ke da ita ta lashe kofin Turai karo na uku a jere ita ce kashi 7.3, wanda ya sanya ta a matsayi na huɗu, yayin da Manchester City—wadda ta lashe kofin a 2023—take a matsayi na uku tare da damar kashi 12.7.

Dukkan ƙungiyoyi biyar na gasar Premier League suna cikin jerin ƙungiyoyi 10 na farko a jerin waɗanda ake kyautatawa zaton lashe gasar, kuma an ba su damar da ta wuce kashi 50% na kai wa matakin ƙungiyoyi 16 na ƙarshe.

Dangane da tsarin matakin rukuni na gasar, Liverpool ce ta samu jadawalin wasanni mafi sauƙi a cewar ƙididdigar ƙarfin ƙungiyoyi da Opta ya yi: Stuttgart ce ke da hanyar da ta fi sauki gaba ɗaya gasar, yayin da Inter Milan ta samu yanayi mafi sauƙi a tsakanin ƙungiyoyin da ke cikin rukuni na farko.

Arsenal ma ta samu jadawalin wasanni mai sauƙi. Duk da cewa za ta fafata da Real Madrid da Bayern Munich, ƙungiyar ta Mikel Arteta ta kuma haɗu da ƙungiyoyi biyu mafi ƙarancin matsayi a gasar—wato Sabah da Slovan Bratislava.

Manchester City za ta fuskanci wasu daga cikin wasanni mafi wahala a tsakanin ƙungiyoyin Ingila, inda ƙungiyoyi biyar kacal suka samu jadawalin wasanni mafi wahala fiye da nasu. Za su fafata da manyan ƙungiyoyin Turai biyu, wato Barcelona da PSG, yayin da ƙungiyar Napoli—wadda ke matsayi na 24—za ta iya kasancewa babban ƙalubale ga ƙungiyar ta filin wasan Etihad.

A kakar wasan da ta gabata, Arsenal ta kasance a saman teburi bayan zagayen farko na gasar bayan ta samu ɗaya daga cikin jadawalin wasanni mafi sauki kamar yadda kamfanin Opta ya bayyana, yayin da Bayern Munich ta zo ta biyu duk da cewa ta fuskanci ƙungiyoyi masu matuƙar wahala.