Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Dangote zai sayar da hannun jarin matatarsa, kuma ta yaya hakan zai shafe ku?
Attajirin Afirka, Aliko Dangote, ya sanar da cewa cikin kwanaki masu zuwa zai fara sayar da hannun jari a matatar man fetur ɗinsa.
Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana hakan a wajen bikin sanya hannu kan yarjejeniyar, ranar Litinin a birnin Legas.
Ɗangote ya ce yana son amfani da kuɗin da za a samu daga wannan tsarin ne domin ƙara faɗaɗa aiki da faɗada matatar daga matakin da take ciki yanzu zuwa mafi girma.
Ya kuma ce yana son bai wa talakawan da ba su da manyan kuɗaɗe damar zama masu hannun jari a matatar.
Wannan ne ya sa aka sanya mafi ƙarancin adadin hannun jarin da mutum zai iya saya ya zama guda 10 kacal.
A karkashin tsarin sayar da hannun jari ga jama'a da ake kira da (IPO), za a fitar da hannayen jari na yau da kullum biliyan 4.1 a kasuwa kan farashin naira 525 kan kowanne hannu, kuma ana sa ran fara tayin a ranar Litinin, 14 ga Satumba.
A wata sanarwa, Rukunin Kamfanonin Dangote ya bayyana wannan IPO wato karo na farko da wani kamfani ke fitar da hannayen jarinsa ga jama'a domin su saya. a matsayin mafi girman tayin sayar da hannun jari da aka taba yi a tarihin Afirka, inda ake sa ran tara fiye da naira tiriliyan biyu kwatankwacin kimanin dala biliyan 1.5.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da farashin fetur ya kusa kaiwa naira 1,400 kan kowace lita zuwa ƙarshen watan Agusta a Najeriya.
Lamarin ya biyo bayan ƙarin da Matatar Dangote ta yi wa farashin sayar da man fetur ga dillalai. A ranar 29 ga Agusta, matatar ta ƙara farashin ta da naira 65 kan kowace lita, daga naira 1,200 zuwa naira 1,265.
Yadda ƴan Najeriya za su ci moriyar tsarin
Dangote ya ce wannan tayin sayar da hannun jari an shirya shi ne domin bai wa abin da ya kira "talakawan Najeriya da na Afirka" damar mallakar hannun jari a matatar.
Wannan na zuwa ne bayan da matatar ta fara aiki, inda a farkon lokaci ta taimaka wajen rage wasu farashin dangogin mai.
"Abin da muke ƙoƙarin yi shi ne tabbatar da cewa direbobinmu, masu girki, masu hidima, manajoji da kowa da kowa suna samun damar mallakar wani kaso a wannan matata," in ji Alhaji Aliko Dangote.
Yaya IPO ke aiki?
Lokacin da IPO ya fara ciniki a kasuwar hannayen jari, masu zuba jari za su iya sayen hannun jari a kamfanin da a baya masu zaman kansu ne kaɗai ke da ikon mallakarsa.
Mene ne amfanin hakan ga masu saye?
Masana na cewa masu sayen hannun jari za su iya amfana ta hanyoyi kamar:
- Samun riba idan darajar hannun jarin ta ƙaru.
- Samun rabon riba idan kamfanin ya raba riba.
- Sauƙin saye da sayar da hannun jari a kasuwa.
- Rage haɗarin zuba jari idan aka kwatanta da wasu hanyoyin kasuwanci.
Ko akwai haɗari?
Eh. Kamar kowane zuba jari, tsarin sanya hannun jari na IPO na tattare da wasu haɗurra, ciki har da:
- Sauye-sauyen dokoki da manufofin kamfani
- Sauyin salon gudanarwa bayan kamfanin ya shiga kasuwar hannayen jari.
- Sauka da faɗuwar hannun jari bisa yanayin kasuwa.
A cewar Hukumar Kula da Kasuwancin Gwamnati ta Najeriya (BPE), za a iyakance yawan hannun jarin da mutum ko wata hukuma za su iya saya domin mutane da yawa su samu damar shiga.
Saboda haka, idan shirin ya tafi yadda aka tsara:
- Talakawa za su samu damar zama masu hannun jari.
- Ƙarin kuɗi zai shiga matatar domin faɗaɗa ayyukanta.
- Za a iya samar da ƙarin ayyukan yi.
- Tattalin arziki da kasuwar hannayen jari ta Najeriya za su ƙara ƙarfi.
Idan samar da man fetur ya ƙaru, hakan na iya taimakawa wajen bunƙasa wadatar kayayyakin mai a cikin ƙasa.
Girman matatar Ɗangote
A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, ba Najeriya kaɗai ce ke nuna sha'awar sayen hannayen jarin ba.
A makon da ya gabata, Dangote ya kai ziyara Botswana domin yi wa masu zuba jari bayani kan shirin fitar da hannayen jarin ga jama'a.
Matatar Dangote tana yankin Ibeju-Lekki a Jihar Legas, kuma tana kan fili mai fadin kusan hekta 2,635.
A cewar Rukunin Kamfanonin Dangote, wannan cibiyar za ta kasance mafi girman matatar mai ta babban layi guda ɗaya na sarrafa danyen mai daga farko har ƙarshe, da ake kira da "Single-Train", a duniya mai ikon tace gangar danyen mai 650,000 a rana, tare da masana'antar nau'in roba da ake samarwa daga feutur da iskar gas na "Polypropylene" mai ƙarfin samar da tan 900,000 a shekara.
Idan ta fara aiki da cikakken ƙarfi, ana sa ran matatar za ta iya biyan kashi 100 cikin 100 na buƙatun Najeriya na dangogin man fetur da aka tace, tare da samun ragowar da za a fitar zuwa ƙasashen waje.
An tsara ta ne domin tace nau'o'in danyen mai iri-iri, ciki har da na ƙasashen Afirka da dama, wasu daga Gabas ta Tsakiya da kuma nau'in mai maras kauri na Amurka.
Matatar tana da tankuna 177 da ke da jimillar ƙarfin ajiya na lita biliyan 4.742.
A wata sanarwa daga Dangote, an ce an yi amfani da manyan injinan haƙo yashi mafi girma a duniya wajen cike wurin da yashi mai yawan mita kubik miliyan 65, aikin da ya kashe kusan euro miliyan 300.