Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lalurar jego: Ana tuhumar uwa da kashe ƙananan ƴaƴanta uku
- Marubuci, Madeline Halpert
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
An fara jin ta-bakin masu taimaka wa alƙali a shari'ar Lindsay Clancy, wata mata a jihar Massachusetts ta Amurka da ake tuhuma da kashe ƙananan ƴaƴanta uku a gidansu da ke wani yanki na wajen birnin Boston.
A wata shari'a da ta ɗauki hankalin jama'ar Amurka, Clancy ba ta musanta cewa ita ce ta kashe yaran nata ba, amma lauyoyinta na cewa bai kamata a ɗora mata alhaki ba saboda tana fama da matsananciyar lalurar ƙwaƙwalwa.
Ana tuhumar Clancy da laifuka uku na kisan kai mataki na farko dangane da mutuwar yaran a watan Janairun 2023.
Masu taimaka wa alƙali kuma za su iya yin la'akari da ƙananan tuhume-tuhume, ciki har da kisan kai ba da gangan ba, ko kuma su same ta ba ta da laifi saboda taɓin hankali.
Idan aka same ta da laifin kisan kai mataki na farko, za ta fuskanci hukuncin daurin rai da rai ba tare da yiwuwar samun afuwa ba.
Ga wasu daga cikin muhimman abubuwa da suka faru a wannan shari'a mai cike da raɗaɗi da ta ɗauki mako biyar.
Clancy na fama da gane-gane
Masu gabatar da ƙara suna zargin cewa a ranar 24 ga Janairun 2023, Clancy ta shake dukkan ƴaƴanta da gangan, Cora mai shekara 5, Dawson mai shekara 3, da Callan mai wata takwas, da igiyar motsa jiki a gidansu da ke Duxbury, Massachusetts, kafin ta yi tsalle dira ta taga daga hawa na biyu.
Clancy, wadda yanzu take da shekara 36, ta samu shanyewar rabin jiki sakamakon dirowar da ta yi, kuma ta halarci shari'ar ne a kan kujerar guragu.
Lauyoyin Clancy, yayin da suke kare ta, ba su taɓa ƙaryata rawar da ta taka a kisan ba.
Maimakon haka, sun gabatar da hujjoji na taɓin hankali, suna masu cewa Clancy tana fama da gane-gane da kuma ruɗani bayan ta haifi ƙaramin ɗanta.
Sun kafa hujja da jinyar matsalar ƙwaƙwalwa da take yi, wanda ita ce ta kai kanta asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa kwanaki kaɗan kafin mutuwar yaran.
A gefe guda, masu gabatar da ƙara suna cewa Clancy ta ɗauki mataki ne da gangan na kashe 'ya'yanta kuma ya kamata a ɗora mata alhakin lamarin.
Suna zargin cewa kafin yin kisan Clancy ta aiki mijinta Patrick Clancy, domin kada ya kasance a gida.
Iyalan Clancy, ciki har da tsohuwar surukarta da mijinta, sun ba da shaida game da yanayin hankalinta kafin mutuwar yaran.
Shari'ar da ta ɗauki makonni biyar ta jawo hankalin mutane a kafafen sada zumunta yayin da dubban mutane suka bi yadda ake gudanar da zaman kotun.
Daruruwan mata sun taru a wajen kotun domin nuna goyon baya ga Clancy, suna sanye da rigunan ruwan hoda masu ɗauke da jimloli kamar "Tana Buƙatar Taimako" da "A sama wa Lindsay lafiya".
'Lokaci mai matuƙar wahala': Tsohon mijin Clancy ya ba da shaida
Tsawon kwanaki biyu, tsohon mijin Clancy, Patrick, ya bayyana wa masu taimaka wa alƙali yadda matsalar ƙwaƙwalwar tsohuwar matarsa ta fara bayan haihuwa, sannan ya bayyana ranar da 'ya'yansa suka mutu da cikakkun bayanai masu tayar da hankali.
Ya shaida wa masu taimaka wa alƙali cewa "abubuwa sun lalace ne sosai" kusan wata guda kafin mutuwar yaran.
"Ta fara rage kiba sosai, kuma ta shiga matsananciyar damuwa, tana cikin wani yanayi mai matuƙar wahala," in ji shi.
Ya bayyana yadda take neman taimako daga likitoci lokaci zuwa lokaci tare da shan magunguna iri-iri, ya ƙara da cewa ya tuna tana cewa ta fara tunanin kashe kanta.
Patrick Clancy ya bayyana gani na ƙarshe da ya yi wa ɗansa Dawson yana zaune a kan kujera yana cin soyayyen naman kaza kafin ya fita domin sayo kayan abinci da magani.
Ya dawo ya tarar da ƴaƴansa a mace.
Lindsay Clancy ta fashe da kuka a kotu yayin da aka kunna muryar kiran neman ɗauki da mijinta ya yi.
An ji yana ihu yana cewa, "Ta kashe yaran," bayan ya iske ƴaƴansu a mace a ɗakin ƙasa.
Tun daga farkon shari'ar, zarge-zarge marasa tushe suka riƙa yawo a shafukan intanet a kan Patrick Clancy, ciki har da zargin cewa yana da hannu a kisan yaran nasa.
Sai dai ba a taɓa sanya shi a cikin waɗanda ake zargi ba a wurin binciken; Lindsay Clancy ta amsa cewa ita ce ta kashe ƴaƴanta, kuma lauyoyinta ba su musanta hakan ba.
Taƙaddama lalurar Clancy
Fiye da ƙwararrun 10 da suka bayar da shaida daga ɓangaren wadda ake tuhuma da kuma masu gabatar da ƙara, ciki har da wasu da suka yi musayar zafafan kalamai da lauyoyi kan lafiyar ƙwaƙwalwar Clancy.
A tsawon lokacin da ake kula da ita, an bai wa Clancy magunguna daban-daban har fiye da 12, kuma ta nemi taimako daga layin kiran wayar da ke taimaka wa masu tunanin kashe kansu da kuma sashen gaggawa.
Masu kare Clancy sun yi ta ƙoƙarin gamsar da masu taimaka wa alƙali cewa tana fama da lalurar ƙwaƙwalwa bayan haihuwa, wata cuta da ba a cika samu ba da ke iya sa mata su riƙa samun tsananin zaƙuwa ko shiga tsananin damuwa ko kuma duka biyun.
Clancy ta yi iƙirarin cewa tana yin gane-gane da kuma shiga cikin ruɗani.
Wata rana a kotu muhawara ta yi zafi a lokacin da ɗaya daga cikin masu kula da lafiya ƙwaƙwalwar Clancy, Jennifer Tufts ta bayyana cewa Clancy ba ta nuna alamun lalurar ƙwaƙwalwa ba a lokacin da take zuwa neman kulawa a wurin su.
"Babu wata alama mai ƙwari da ta nuna cewa ita ko wani daban na cikin haɗari," in ji Tufts, wadda ta kula da Clancy fiye da sau 12 cikin watanni biyar.
Amma lauyoyin da ke kare wadda ake tuhuma sun yi nuni da bayanan likita Tufts da ke nuna cewa Clancy ta nuna wasu alamu da ake iya alaƙantawa da lalurar tsananin murna.
Tufts ta musanta cewa ta yi imanin Clancy ta nuna irin wannan alama.
Yayin da lauyan kariya Kevin Reddington ya matsa mata da tambayoyi, ta amsa cewa:
"Ban damu da abin da aka rubuta ba. Na san abin da nake nufi."
Mahaifiyar Clancy ta bayar da shaida
Baya ga Patrick, tsohuwar surukar Lindsay, mahaifiyarta da 'yar'uwarta su ma sun ba da shaida, suna fada wa masu taimaka wa alkali yadda lalurar kwakwalwarta ta ci gaba da tabarbarewa bayan haihuwar ɗanta.
"Lindsay Clancy tana roƙon taimako," in ji tsohuwar surukarta Susan Clancy.
"Ba ta iya barci. Ta daina cin abinci," in ji ta.
"Ta kasance cikin tsananin damuwa da baƙin ciki."
Ta ƙara da cewa Clancy ta kasance "mahaifiya mai matuƙar kulawa" har zuwa lokacin haihuwar ƙaramin ɗanta.
Mahaifiyar Clancy, Paula Musgrove, ta ce 'yarta ta fada mata da tsohon mijinta cewa tana yin wasu tunani-tunani na cutar da yaran nata wata guda kafin mutuwarsu.
Musgrove ta ce 'yarta ta fara zama mai tsoro da zargi kuma tana cewa magungunanta suna "dagula tunaninta".
'Yar'uwar Clancy, Allison Ozga, ta shaida wa kotu cewa 'yar'uwarta tana fama da tunanin kashe kanta a kowace rana wata guda kafin ta kashe 'ya'yanta.
Mahaifiyar Lindsay Clancy, Paula Musgrove, ta gaya wa kotu cewa 'yarta ta zama mai tsoro da zargi
Alƙali ya umarci masu taimaka masa su yi watsi da shaida kan addini
Kwana biyu kafin jawaban rufe shari'a, bangaren kariyar Clancy ya nemi a soke shari'ar bayan masu gabatar da ƙara sun tambayi shaidu game da addininta.
A makon da ya gabata, masu gabatar da ƙara sun tambayi tsohuwar surukar Clancy, Susan Clancy, ko ta san cewa ana ɗaukar kisan kai a matsayin "babban zunubi" bayan sun tambaye ta ko ita mai bin akidar Katolika ce.
Sannan a wannan makon, masanin ilimin halayyar ɗan‘adam kuma mai bincike Kirk Heilbrun, wanda ya yi hira da Lindsay Clancy bayan kashe-kashen, ya shaida cewa ya tambaye ta ko ana ɗaukar kashe kai a matsayin "babban zunubi" yayin tattaunawa kan tarbiyyarta ta Katolika.
Alƙali William Sullivan ya yi watsi da bukatar tawagar lauyoyin Clancy na soke shari'ar, amma ya gaya wa masu taimaka wa alkali cewa wannan "wani fanni ne na shaida da bai dace ba gaba ɗaya".
"Za a cire shi. Ba za a yi la'akari da shi ba," in ji shi.