Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa wasu sojoji suka yi bore a Nijar?
Ga alama ƙura ta lafa a Yamai babban birnin Nijar bayan da wasu sojoji masu tawaye sun kai hari filin jirgin sama da fadar shugaban kasa.
Sojojin sun fara bore ne tun a cikin dare zuwa wayewar safiyar ranar Asabar, lamarin da ya haifar da musayar wuta da fashe-fashe na tsawon sa'o'i tare da dakatar da watsa shirye-shiryen gidan talabijin da rediyon gwamnati na dan lokaci.
Daga baya, ma'aikatar tsaron Nijar ta bayyana cewa sojoji sun kwato wuraren da aka kwace yayin harin na daren Asabar.
Sai dai majiyoyin tsaro sun ce har zuwa yammaci sojojin masu bore sun kasance a filin jirgin saman Yamai kuma yanayin ya ci gaba da kasancewa cikin rashin tabbas.
Wannan harin dai ya kasance wata sabuwar barazana ga mulkin Abdourahamane Tiani, wanda ya kwace iko a juyin mulkin shekarar 2023.
Tiani ya yi alkawarin inganta tsaro a wannan kasa ta yankin Sahel—wacce ke daya daga cikin manyan masu samar da sinadarin uranium—amma hare-haren 'yan jihadi sun ci gaba da faruwa.
A farkon shekarar nan, mayaƙa masu alaƙa da Al Qaeda da IS sun kai hare-hare kan fararen hula a filin jigin sama da kuma sansanonin soji.
Shugaba Tiani bai fito bainar jama'a ba ya yi jawabi bayan faruwar lamarin, kuma wasu na ganin duk da gwamnatinsa ta ce iƙirarin murkushe boren sojojin amma akwai barazanar tsaro a ƙasar.
Me Masana suka ce?
Masana kimiyyar siyasa a Nijar sun yi tsokaci bayan yunkurin boren da wasu sojojin kasar suka yi wanda bai yi nasara ba.
Dokta Dominic Francis, masanin kimiyyar siyasa da harkokin diflomasiyya da kuma tsaro a nahiyar Afirka, ya shaida wa BBC cewa wannan yunkuri na bore da aka yi a Nijar bai zo da mamaki ba.
Ya ce,"Ba wani abu ba ne ya kawo wannan yunkurin bore illa yadda masu mulki a Nijar ke tafiyar da mulkin su, misali rashin ba wa sojoji kulawar da ta dace."
Masanin ya ce,"Akwai sojoji da yawa da suka rasa ransu a fagen daga, ma'ana a kan aiki wajen kare kasa, kuma hakan na da nasaba da rashin isassun kayan aiki tun daga kan makamai da kula da jin dadi da walwalarsu."
Ya yi iƙirarin cewa akwai bambancin da ake nunawa a tsakanin jami'an tsaro su, inda a cewar sa "wasu suna zargin kamar ana fifita sojojin da ba su je fagen daga ba a kan wadanda ke fagen daga, to irin wadannan bambancin ka iya tunzurasu su dauki wannan mataki."
Dokta Dominic Francis, ya ce "rashin gaskiya na taka muhimmiyar rawa wajen faruwar irin wannan bore ba ma a Nijar kadai ba, har ma da wasu kasashe na Afirka."
Ya ce akwai matakan da ya kamata gwamnatin Nijar ta dauka don kare afkuwar irin wannan yunkurin bore, kamar sulhu tsakanin wadanda suka yi wannan yunkuri da kuma gwamnatin.
"Ta zauna da su ta ji me ye damuwar su har suka dauki wannan mataki, sai ta gyara," a cewar sa.
Masanin ya ce,"ya kamata a rika kyautatawa sojojin da suka gamu da wata lalura a yayin aiki ko suka mutu a kyautata wa iyalansu, sanann idan sun yi ritaya kuma a kyautata walwalarsu ta yadda ba za su zamo abin tausayi ba daga karshe."
Dakta Francis, ya ce," Idan har gwamnatocin kasashe suka yi wadannan abubuwa, to ko shakka babu za a samu saukin yunkurin irin wannan boren ba a Nijar kadai ba har ma sauran kasashen da ke Afirka."
Me hukumomin Nijar suka ce?
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yi bayani kan harbe-harben da aka kwashe tsawon dare ana ji har zuwa wayeywar gari a Yamai, babban birnin kasar inda ta ce ta murƙushe yunƙurin bore da wasu sojoji suka yi.
Lamarin ya tayar da hankulan mazauna birnin tare da jawo hankalin ƙasashen duniya.
A cikin sanarwar da ya karanta ta gidan talabijin na gwamnati, ministan tsaron Nijar, Janar Salifou Modi, ya ce kimanin ƙarfe 12:20 na dare wani rukuni na sojoji sun kutsa cikin sansanin soji na 101 da ke kusa da filin jirgin saman Diori Hamani a Yamai, inda suka yi garkuwa da wasu daga cikin abokan aikinsu.
Sai dai ya ce dakarun ƙasar sun yi gaggawar mayar da martani, inda suka dakile yunƙurin tare da dawo da doka da oda.
Wasu mazauna Yamai da BBC ta tuntuba sun ce sun ji karar harbe-harbe a kusa da filin jirgin saman Diori Hamani, fadar shugaban ƙasa da kuma wasu sansanonin soji.
Wani mazaunin birnin ya shaida wa BBC cewa: "Tun misalin ƙarfe ɗaya na dare muke jin karar harbe-harbe da kuma wasu abubuwan fashewa."
Wani mutum na biyu kuma ya ce ya ji karar harbe-harben lokacin da ya tashi sallar asuba.
Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023, inda suka hambarar da gwamnatin da aka zaɓa ta Mohamed Bazoum, Nijar ke fuskantar ƙalubalen tsaro daga ƙungiyoyin mayaƙa masu alaƙa da Al-ƙa'ida da kuma IS.
Ƙasar mai arzikin ma'adanan yureniyom da danyen man fetur ta sauya akalar manufofinta na ƙetare bayan juyin mulkin, inda ta ƙarfafa alaƙa da Rasha tare da nisantar ƙasashen yamma.
Nijar da makwabtan ta Burkina Faso da Mali sun kuma fice daga ƙungiyar Ecowas tare da kafa Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES).
A baya, shugaban ƙasar Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya zargi Faransa da hannu wajen ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta, zargin da Paris ta musanta.