Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bellingham na son ci gaba da zama a Madrid, United da Chelsea na harin Kounde
Ɗan wasan Ingila Jude Bellingham, 23, ya kammala shirin tsawaita kwantiraginsa na ci gaba da zama a Real Madrid har zuwa 2031. (AS - in Spanish)
Arsenal da Liverpool za su biya ƙarin fam miliyan 60 don jan hankalin ɗan wasa Kevin Schade, daga Brentford. (Teamtalk)
Leeds na ci gaba da tuntuɓa kan halin da Igor Paixao ke ciki a Marseille, inda ya ke cikin ƴan wasan da ƙungiyar ta Fransa ke son sallama yayin da suka fama da matsalolin kuɗi. (Football Insider)
Chelsea, da Manchester United, da Arsenal, da Liverpool da kuma Bayern Munich na sa ido kan halin da Jules Kounde ke ciki a Barcelona, yayin da dan wasan ke auna makomarsa a Barcelonan. (4-4-2.ch - in German)
Barcelona na son shiga ckin ƙugiyoyin da ke taya siyyen ɗan wasan Manchester United JJ Gabriel, inda Real Madrid da Paris St-Germain ke son ɗan wasan tare da da ƙara farashin taya shi. (Sport - in Spanish)
Newcastle ba ta zo ko kusa ba, wajen ɗaukar Joe Willock wajen sabunta kwantaraginsa duk da cewar mai horar da ƴan wasan ƙungiyar Matthias Jaissle da ke son ɗan wasan. (Newcastle Chronicle)
Kociyan Leeds Daniel Farke ya cimma sabuwar yarjejeniya da hakan zai bayar da dama gare shi na sa Ellan Road ci gaba da zama a ƙungiyar har nan da 2029. (The Athletic - subscription required)
Daraktan wasanni Bayern Munich Max Eberl ya ce ana samun fahimta a tattaunwar da suke yi da ɗan Harry Kean, wajen ganin ya rattaba hannu kan sabuwar kwantaraginsa, sai dai babau wani ƙwaƙwaran alƙawari da aka yi masa a hukumance kan haka. (Sky Sports Germany - in German)
Ɗan wasan AC Milan Fikayo Tomori, zai bar ƙungiyar a ƙarshen kakar wasannin idan kwantaraginsa ta ƙarem ba tare da samun wani tayi daga wata ƙungiya ba. (Calciomercato - in Italian)
Da alama Real Madrid za ta iya barin ɗan wasan Morocco Brahim Diaz, a matsayin ɗan wasan aro a watan Janairu, sakamakon yadda ta fifita Endrick akansa. (Marca - in Spanish)