Fitatttun ƴan Afirka da za su buga Gasar Kofin Duniya ta 2026

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 8

A karon farko tawaga 10 ce daga Afirka za ta buga gasar kofin duniya a bana da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico.

Jimilla tawaga 48 ce za ta kece raini a karon farko da aka sauyawa gasar fasali, inda Argentina ce ke rike da kofin da ta lashe a 2022 a Qatar.

Za a fara wasannin daga 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yuli.

Mohammed Abdu ya haɗa muku rahoto kan dukkan ƴan wasan da aka gayyata daga nahiyar, domin buga gasar kofin duniya 2026.

Tawagar Afirka ta Kudu

Akwai ƴan wasa da yawa da aka yi mamaki da kociya, Hugo Broos waɗanda aka gayyata a karon farko da Bafana-Bafana za ta halarci kofin duniya tun bayan wanda ta shira shekara 16 da ta wuce.

Jerin ƴan wasan Afirka ta Kudu da za su buga kofin duniya:

Masu tsaron raga: Ronwen Williams (Mamelodi Sundowns), Ricardo Goss (Siwelele), Sipho Chaine (Orlando Pirates)

Masu tsaron baya: Khuliso Mudau, Aubrey Modiba, Khulumani Ndamane

(all Mamelodi Sundowns), Olwethu Makhanya (Philadelphia Union,

USA), Bradley Cross (Kaizer Chiefs), Thabang Matuludi (Polokwane

City), Nkosinathi Sibisi, Kamogelo Sebelebele (both Orlando

Pirates), Ime Okon (Hannover 96, Germany), Samukele Kabini

(Molde FK, Norway), Mbekezeli Mbokazi (Chicago Fire, USA)

Masu buga tsakiya: Teboho Mokoena, Jayden Adams (both Mamelodi

Sundowns), Thalente Mbatha (Orlando Pirates), Sphephelo Sithole

(Tondela, Portugal)

Masu cin ƙwallaye: Oswin Appollis, Tshepang Moremi, Evidence Makgopa, Relebohile Mofokeng (all Orlando Pirates), Lyle Foster (Burnley, England), Iqraam Rayners, Themba Zwane (both Mamelodi Sundowns), Thapelo Maseko (AEL Limassol, Cyprus)

Tawagar Morocco

Sabon koci, Mohamed Ouahbi ya gayyaci Nayef Aguerd cikin tawagar Morocco, bayan da mai tsaron baya ke jinya tun daga cikin watan Maris, ya kuma ajiye mai cin ƙwallaye, Youssef En-Nesyri.

Jerin ƴan wasan tawagar Morocco da za su buga mata kofin duniya:

Masu tsaron raga: Yassine Bounou (Al Hilal), Munir Mohamedi (RS Berkane), Ahmed Tagnaouti (Royal Armed Forces)

Masu tsaron baya: Noussair Mazraoui (Manchester United), Anass Salah-Eddine (PSV Eindhoven), Youssef Belammari (Al Ahly), Nayef Aguerd (Marseille), Chadi Riad (Crystal Palace), Issa Diop (West Ham United), Redouane Halhal (KV Mechelen), Achraf Hakimi (Paris St-Germain), Zakaria El Ouahdi (Genk)

Masu buga tsakiya: Samir El Mourabet (Strasbourg), Ayyoub Bouaddi (Lille), Neil El Aynaoui (Roma), Sofyan Amrabat (Real Betis), Azzedine Ounahi (Girona), Bilal El Khannouss (Stuttgart), Ismael Saibari (PSV Eindhoven)

Masu cin ƙwallaye: Abdessamad Ezzalzouli (Real Betis), Chemsdine Talbi (Sunderland), Soufiane Rahimi (Al Ain), Ayoub El Kaabi (Olympiacos), Brahim Diaz (Real Madrid), Yassine Gessime (Strasbourg), Ayoub Amaimouni-Echghouyabe (Eintracht Frankfurt)

Tawagar Ivory Coast

Kociyan tawagar Ivory Coast, Emerse Fae ya gayyaci mai cin ƙwallaye, Ange-Yoan Bonny a karon farko da zai yi wa kasar tamaula.

Jerin ƴan wasan Ivory Coast da za su yi mata gasar kofin duniya:

Masu tsaron raga: Yahia Fofana (Rizespor), Mohamed Kone (Charleroi), Alban Lafont (Panathinaikos)

Masu tsaron baya: Emmanuel Agbadou (Wolverhampton Wanderers), Clement Akpa (AJ Auxerre), Ousmane Diomande (Sporting), Guela Doue (Racing Strasbourg), Ghislain Konan (Gil Vicente), Odilon Kossonou (Atalanta), Evan Ndicka (AS Roma), Wilfried Singo (Galatasaray)

Masu buga tsakiya: Seko Fofana (Stade Rennais), Parfait Guiagon (Charleroi), Franck Kessie (Al Ahli), Christ Oulai (Trabzonspor), Ibrahim Sangare (Nottingham Forest), Jean-Michael Seri (NK Maribor)

Masu cin ƙwallaye: Simon Adingra (AS Monaco), Ange-Yoan Bonny (Inter Milan), Amad Diallo (Manchester United), Oumar Diakite (Cercle Brugge), Yan Diomande (RB Leipzig), Evann Guessand (Aston Villa), Nicolas Pepe (Villarreal), Bazoumana Toure (Hoffenheim), Elye Wahi (Nice)

Tawagar Tunisia

Koci, Sabri Lamouchi bai gayyaci ƙyaftin Ferjani Sassi da wani fitatcen mai tsaron baya, Yassine Meriah.

Jerin ƴan wasan Tunisia da za su kara a gasar kofin duniya:

Masu tsaron raga: Sabri Ben Hessen (Etoile Sahel), Abdelmouhib Chamakh (Club Africain), Aymen Dahman (CS Sfaxien)

Masu tsaron baya: Ali Abdi (Nice), Adem Arous (Kasimpasa), Mohamed Amine Ben Hamida (Esperance), Dylan Bronn (Servette Geneva), Raed Chikhaoui (US Monastir), Moutaz Neffati (Norrkoping), Omar Rekik (NK Maribor), Montassar Talbi (Lorient), Yan Valery (Young Boys Berne)

Masu buga tsakiya: Mortadha Ben Ouanes (Kasimpasa), Anis Ben Slimane (Norwich City), Ismael Gharbi (FC Augsburg), Rani Khedira (Union Berlin), Mohamed Hadj Mahmoud (Lugano), Hannibal Mejbri (Burnley), Ellyes Skhiri (Eintracht Frankfurt)

Masu cin ƙwallaye: Elias Achouri (FC Copenhagen), Khalil Ayari (Paris St Germain), Firas Chaouat (Club Africain), Rayan Elloumi (Vancouver Whitecaps), Hazem Mastouri (Dynamo Makhachkala), Elias Saad (Hannover 96), Sebastian Tounekti (Celtic).

Tawagar Masar

Tsohon ɗan wasan Liverpool, Mohamed Salah shi ne zai ja ragamar Masar a gasar cin kofin duniya.

Jerin ƴan wasan Masar da za su buga mata gasar kofin duniya:

Masu tsaron raga: Mohamed El-Shenawy, Mostafa Shobeir (Al Ahly), El-Mahdi Soliman (Zamalek), Mohamed Alaa (El Gouna).

Masu tsaron raga: Mohamed Abdelmonem (Nice), Mohamed Hany, Yasser Ibrahim (Al Ahly), Hossam Abdelmaguid, Ahmed Fattouh (Zamalek), Tarek Alaa (ZED), Rami Rabia (Al Ain), Hamdi Fathi (Al Wakrah), Karim Hafez (Pyramids).

Masu buga tsakiya: Mohamed Salah (Liverpool), Marwan Attia, Ahmed Mostafa "Zizo", Mahmoud Hassan "Trezeguet", Emam Ashour (Al Ahly), Mostafa Abdel Raouf, Mohannad Lasheen (Pyramids), Haitham Hassan (Real Oviedo), Mahmoud Saber (ZED), Ibrahim Adel (Nordsjælland), Nabil Emad (Al-Najma).

Masu buga tsakiya: Omar Marmoush (Manchester City), Hamza Abdel Karim

(Barcelona Atletic).

Tawagar Senegal

Koci, Pape Thiaw ya ajiye mai tsaron baya Moustapha Mbow da kuma Ilay Camara, kafin daga baya ya sanar da 26 da za su wakilci kasar a gasar kofin dunuya.

Ƴan wasa na ƙwarya-ƙwarya kafin tantance 26 na tawagar Senegal:

Masu tsaron raga: Edouard Mendy, Mory Diaw, Yehvann Diouf

Masu tsaron baya: Krepin Diatta, Antoine Mendy, Kalidou Koulibaly, El Hadji Malick Diouf, Mamadou Sarr, Moussa Niakhate, Abdoulaye Seck, Ismail Jakobs

Masu buga tsakiya: Idrissa Gana Gueye, Pape Gueye, Lamine Camara, Habib Diarra, Pathe Ciss, Pape Matar Sarr, Bara Sapoko Ndiaye

Masu cin ƙwallaye: Sadio Mane, Ismaila Sarr, Iliman Ndiaye, Assane Diao, Ibrahim Mbaye, Nicolas Jackson, Bamba Dieng, Cherif Ndiaye

Tawagar Aljeria

Mai horar da tawagar Aljeria, Vladimir Petkovic ya kara gayyatar mai taka leda daga tsakiya, Nabil Bentaleb.

Jerin ƴan wasan tawagar Aljeria da za su buga mata kofin duniya:

Masu tsaron raga: Oussama Benbot (USM Alger), Melvin Masstil (Stade Nyonnaise), Luca Zidane (Granada)

Masu tsaron baya: Achraf Abada (USM Alger), Rayan Ait Nouri (Manchester City), Zinedine Belaid (JS Kabylie), Rafik Belghali (Verona), Ramy Bensebaini (Borussia Dortmund), Samir Chergui (Paris FC), Jaouen Hadjam (Young Boys Bern), Aissa Mandi (Lille), Mohamed Amine Tougai (Esperance)

Masu buga tsakiya: Houssem Aouar (Al Ittihad), Nabil Bentaleb (Lille), Hicham Boudaoui (Nice), Fares Chaibi (Eintracht Frankfurt), Ibrahim Maza (Bayer Leverkusen), Yassine Titraoui (Charleroi), Ramiz Zerrouki (FC Twente)

Masu cin ƙwallaye: Mohamed Amine Amoura (VfL Wolfsburg), Nadir Benbouali (Győri ETO), Adil Boulbina (Al-Duhail), Fares Ghedjemis (Frosinone), Amine Gouiri (Olympique de Marseille), Riyad Mahrez (Al-Ahli), Anis Hadj Moussa (Feyenoord Rotterdam).

Mai tsaron raga mai jiran ko-ta-kwana: Abdellatif Ramdane (Mouloudia Alger).

Tawagar Cape Verde

Koci, Bubista ya saka mai tsaron baya, Logan Costa cikin tawagar da za su buga wa Vape Verde gasar kofin duniya.

Jerin ƴan wasan Cape Verde da za su buga mata kofin duniya:

Masu tsaron raga: Carlos dos Santos (San Diego), Marcio Rosa (Montana 1921), Vozinha (Chaves)

Masu tsaron baya: Sidny Cabral (Benfica), Diney Borges (Al Bataeh), Logan Costa (Villarreal), Roberto Lopes (Shamrock Rovers), Steven Moreira (Columbus Crew), Wagner Pina (Trabzonspor), Kelvin Pires (SJK Seinäjoki, Finland), Stopira (Torreense)

Masu buga tsakiya: Telmo Arcanjo (Vitoria Guimaraes), Deroy Duarte (Ludogorets), Laros Duarte (Puskas Akademia), Joao Paulo Fernandes (Oțelul Galați), Jamiro Monteiro (PEC Zwolle), Kevin Pina (FK Krasnodar), Yannick Semedo (Farense)

Masu cin ƙwallaye: Gilson Benchimol (Russia), Jovane Cabral (Portugal), Dailon Livramento (Casa Pia), Ryan Mendes (Igdir), Nuno da Costa (Istanbul Basaksehir), Garry Rodrigues (Apollon Limassol), Willy Semedo (Omonia Nicosia), Helio Varela (Maccabi Tel Aviv).

Tawagar Jamhuriyar Congo

Tawagar Jamhuriyar Congo ta je buga gasar kofin duniya tare da fitatcen ɗan wasan da ke buga tsakiya Gael Kakuta da koci, Sebastien Desabre zai ja ragama.

Jerin ƴan wasan tawagar Jamhuriyar Congo da za ta buga kofin duniya:

Masu tsaron raga: Matthieu Epolo (Standard Liège), Timothy Fayulu (Noah), Lionel Mpasi (Le Havre)

Masu buga tsakiya: Dylan Batubinsika (Larisa), Rocky Bushiri (Hibernian), Gedoon Kalulu (Aris Limassol), Steve Kapuadi (Widzew Lodz), Joris Kayembe (Racing Genk), Arthur Masuaku (Racing Lens), Chancel Mbemba (Lille), Axel Tuanzebe (Burnley), Aaron Wan-Bissaka (West Ham United)

Masu buga tsakiya: Theo Bongonda (Spartak Moscow), Brian Cipenga (Castellon), Meshack Elia (Alanyaspor), Gael Kakuta (Larisa), Edo Kayembe (Watford), Nathanael Mbuku (Montpellier), Samuel Moutoussamy (Atromitos), Ngal'ayel Mukau (Lille), Charles Pickel (Espanyol), Noah Sadiki (Sunderland)

Masu cin ƙwallaye: Cedric Bakambu (Real Betis), Simon Banza (AlJazira), Fiston Mayele (Pyramids), Yoane Wissa (Newcastle United).

Tawagar Ghana

Kociyan tawagar Ghana, Carlos Queiroz ya fayyace ƴan wasan da za su wakilci kasar a gasar kofin duniya, inda aka ajiye mai tsaron baya, Alexander Djiku da mai buga tsakiya, Mohammed Kudus, sakamakon jinya.

Jerin ƴan wasan tawagar Ghana da za ta buga gasar kofin duniya:

Masu tsaron raga: Joseph Anang, Benjamin Asare, Lawrence Ati-Zigi

Masu tsaron baya: Jonas Adjetey, Derrick Luckassen, Gideon Mensah, Abdul Mumin, Jerome Opoku, Kojo Oppong Preprah, Baba Abdul Rahman, Alidu Seidu, Marvin Senaya

Masu buga tsakiya: Augustine Boakye, Abdul Fatawu Issahaku, Elisha Owusu, Thomas Partey, Kwasi Sibo, Kamal Deen Sulemana, Caleb Yirenkyi

Masu cin ƙwallaye: Prince Kwabena Adu, Jordan Ayew, Christopher Bonsu Baah, Ernest Nuamah, Antoine Semenyo, Brandon Thomas-Asante,

Inaki Williams.