Kashe kuɗaɗe a yaƙi ya janyo giɓi a kasafin kuɗin Rasha
Shugaba Putin na gabatar da jawabi a taronsa na shekara-shekara kan tattalin arzikin ƙasar a Saint Petersburg a yau, Juma'a a yayin da masu taimaka masa ke cewa Rasha na nan da ƙarfin ta, a fannin soji da kuma tattalin arziki.
Moscow dai na da giɓi sosai a kasafin kudinta, sakamakon yadda ake ta karkatar da kuɗaɗen ƙasar zuwa ga yaƙin Ukraine.
Sai dai ɗaya daga cikin masu bai wa Putin shawara Kirill Dmitriev ya shaidawa BBC cewa tattalin arzikin Rasha bai yi ƙasa ba duk da takunkuman da aka yi ta kakaba mata.