Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd na harin Hall, Atletico ba ta son sayar wa City Baena
Ɗan wasan baya na Ingila mai shekara 22, Lewis Hall, na iya barin Newcastle United a bazara mai zuwa duk da cewa rahotanni sun ce ya amince da sabon kwantiragi da ƙungiyar har zuwa shekarar 2031. An danganta Hall da yiwuwar komawa Manchester United a baya-bayan nan.
A wani labarin kuma, Manchester United na shirin bai wa ɗan wasan bayanta na Argentina mai shekara 28, Lisandro Martinez, sabon kwantiragi na tsawon lokaci. Sai dai hakan zai dogara ne kan ko zai kauce wa matsalolin rauni da kuma yadda zai taka rawar gani a kakar wasa ta 2026 zuwa 2027 a filin wasa na Old Trafford.
Rahotannin sun nuna cewa shugabannin United na kallon Martinez a matsayin muhimmin ɓangare na shirin ƙungiyar na dogon lokaci, amma suna son ganin ya samu cikakkiyar lafiya da kwanciyar hankali a wasanninsa kafin a tabbatar da sabuwar yarjejeniya.
Brighton na da kwarin gwiwar cewa za ta cimma matsaya kan sabon kwantiragi da ɗan wasan tsakiya na Sweden, Yasin Ayari, mai shekara 22, yayin da tattaunawa ke ci gaba.
Sai dai makomar ɗan wasan gefe na Japan, Kaoru Mitoma, a Brighton na cikin rashin tabbas, saboda ana sa ran ba zai tsawaita kwantiraginsa ba kafin ya kare a bazara mai zuwa, lamarin da ka iya sa ya bar ƙungiyar tun a watan Janairu.
Bayan kasa ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Faransa, Manu Kone, a lokacin cinikin bazara, Chelsea na iya sake komawa nemansa a watan Janairu. Rahotanni sun ce yarjejeniyar na iya haɗawa da musayar ɗan wasan gefe na Ingila, Jamie Gittens.
Liverpool na shirin sayen wani sabon ɗan wasan tsakiya a bazara mai zuwa, abin da zai iya rage matsayin ɗan wasan Argentina, Alexis Mac Allister, a cikin jadawalin zaɓin 'yan wasa na ƙungiyar.
Atletico Madrid ba ta da niyyar sayar da ɗan wasan tsakiya na Sifaniya, Alex Baena, duk da sha'awar da Manchester City ke nunawa a kansa.
Masu yi wa Manchester United da Tottenham Hotspur farautar 'yan wasa sun halarci wasa a Belgium domin kallon ɗan wasan gaba na Jamus daga Club Brugge, Nicolo Tresoldi, mai shekara 22.
A wani labarin kuma, tsohon ɗan wasan bayan Real Madrid kuma dan ƙasar Austria, David Alaba, mai shekara 34, na iya komawa ƙungiyar Club America ta Mexico bayan rabuwarsa da ƙungiyar Sifaniyan a lokacin bazara.