Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa ake yawan samun rikici a mahaƙar ma'adinai a Najeriya?
Al'ummar garin Randagi da kewaye a yankin karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna na cikin tashin hankali sakamkon aukuwar wani rikici da ya ɓarke tsakanin wasu bangarori na manyan masu haƙar ma'adinai.
Al'amarin ana zargin ya yi sanadin rasa rayukan mutum uku, yayin da wasu goma suka jikkata.
Wani wanda lamarin ya faru a gabansa wanda ya buƙaci BBC ta sakaya sunansa ya ce matsalar da ta haddasa tashin-tashinar ta taso ne a sakamakon takun saƙa da ake a tsakanin bangarorin biyu.
Rikicin ya faru ne tsakanin ɓangaren Auwal Dan Haza, wani mai hakar ma'adinai da ke garin Birnin Gwari, da bangaren Abubakar Yusuf, wani shugaban matasan garin na Randagi, kuma mai haƙar ma'adinai.
Inda aka zargi bangaren Auwal Dan Haza da yunkurin kwashe wasu kaya daga wurin hakar ma'adinan.
"Mun ga suna kwashe kayan Abubakar Yusuf da kuma na sauran jama'a, shi ne maza da mata da ke wurin suka fito suka nuna rashin amincewarsu kan hakan," in ji shi.
An zargi jami'an tsaro da yin harbi a wajen da ya yi sanadiyar mutuwar mutum uku tare da jikkata wasu da dama.
Ya ƙara da cewa "suna zuwa sai suka buɗe wuta kan mutanen, inda suka kashe mutum uku suka kuma raunata mutum goma," cewar wanda lamarin ya faru a gabansa.
Wasu na ganin cewa an harzuƙa jami'an tsaron ne shi ya sa suka dauki wannan mataki.
Ya ce an firgita mutane wadanda iyalansu suka rasu suna cikin damuwa matuƙa.
BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Auwal Dan Haza, amma hakan bai samu ba, saboda an kasa samun sa ta waya, kuma bai mayar da da amasr sakon da aka aika masa ta wayar ba.
Babu dai wata sanarwa daga bangaren gwamnatin jihar Kaduna ko kuma jami'an tsaron jihar kan wannan batu.
BBC ta yi kokarin tuntubar rundanar ƴansanda a jihar ta Kaduna, kan wannan batu, amma ba a samu jami'inta na hulda da jama'a, DSP Mansir Hassan ba.
‘Za a dauki mataki’
Honarabul Bashir Zubairu Usman, Ciroman Birnin Gwari, kuma mai wakiltar mazabar Birnin Gwari da Giwa a majalisar wakilai ta tarayya, ya ce lamarin ya tayar masa da hankali.
"Ba za mu bari ba sai mun tabbatar da an yi bincike, kuma dole a biya diyya na wadannan bayin Allah da aka kashe," a cewarsa.
Ɗanmajalisar ya ce jami'an tsaron na ɗaya daga cikin jagoran ɓangaren da ake zargi da fara tsokanar rikicin ne, inda ya ce babu wata doka ko ƙa'ida da ta ce a ba wani mai haƙar ma'adinai jami'an ƴansanda da sojoji domin su ba shi kariya.
"Muna fama da bala'in ƴanbindiga da Boko Haram a yankunanmu saboda haka bai dace a riƙa haka ba - za mu ɗauki duk matakin da ya kamata mu ɗauka a matsayinmu na shugabanni" cewar sa.
Yankin Birnin Gwari na cikin yankunan da ke fama da matsalar hare-haren ƴanbindiga, al'amarin da ya raba jama'a da dama da garuruwansu da ayyukan gona da kasuwanci da dai sauran harkokin yau da kullum.
Ana yawan samun rikici ko mummunan iftila'i a wajen mahaƙar ma'adinai inda hakan kan yi sanadiyyar mutuwar mutane.
Ko a watan Fabrairu an samu wani mummunan iftila'i a wata mahaƙar ma'adinai da ta yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 40 a jihar Filato da ke arewa ta Tsakiyar Najeriya.
Ana ganin cewa guba mai ƙarfi ta sinadarin da ake amfani da shi ne ke taruwa a cikin ramin ƙasa da iska ba ya samun shiga sosai, wanda ke sa ma'aikatan faɗuwa a ƙasa kafin su kammala aikin da suke.
Abin da muka sani
Wasu hotuna da BBC ta gani wadanda ba mu iya tantance sahihancinsu ba sun nuna yadda dandazon mutane ke kokarin hana wasu jerin gwanon motoci ficewa daga kauyen na Randagi.
A wani bidiyon ana jin karar harbe-harben bindiga na tashi, yayin da wata murya ke cewa “sojojin Najeriya na ta harbin mutane a garin Randagi”.
Za a iya hangen hayaki na tashi daga nesa yayin da mutane ke tserewa domin neman mafaka.
Wani bidiyon kuma ya nuna wani matashi da aka tarwatsa wa kai yana kwance a mace cikin jini, kusa da wani babur, sai kuma wani bidiyon da ya nuna mutane a asibiti da alamun raunin harbin bindiga yayin da kayan da suke sanye da su suke jike da jini.
Wadanda BBC ta zanta da su sun bayyana cewa an kashe akalla mutum uku zuwa hudu yayin da babu tabbas kan yawan wadanda aka garzaya da su asibiti.