Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Budurwar da ta rubuta Qur'ani da hannu cikin salo mai ƙayatarwa
A wata unguwa da ke birnin Herat, ƴanmata ne suka duƙufa suna aikin zane. Ga kuma abubuwan da suka zana a alluna da farantai zagaye da su, inda suka yi zane-zane masu ƙayatarwa har a kan tukwanen ƙasa da kuma faranti, inda a saman kowane zane an rubuta "Khatin Zar Gallery", sunan wurin da suke aiki ke nan.
Duk da irin tsauraran dokokin da gwamnatin Taliban ta ƙaƙaba, waɗannan ƴanmata suna yin amfani da taɓo wajen yaƙar talauci.
Jagora a cikinsu ta fita daban, sai dai ita ma ta dukufa tana aiki. A zagaye da ita ayoyin Qur'ani ne da aka zayyana su a shafukan takarda.
Manyan shafuka ne da yawa ɗauke da ayoyin na Qur'ani, yayin da ita kuma take riƙe da alƙalami a hannunta, sai kuma wasu zube a kan teburi.
An haifi Nagita Durrani kuma ta yi dukkanin karatunta ne a garin Herat. "Ni mai aikin zane-zane ce, ina kuma rubuta fassarar Qur'ani zuwa harshen Pashto," kamar yadda ta shaida wa BBC.
Durani ta zayyana ayoyin Qur'ani da yawa a manyan takardu, kuma tana shafe sa'o'i da dama a kowace rana wajen wannan aiki.
"A baya mukan kasu gungu-gungu muna rubuta ayoyin Qur'ani, to amma a yanzu ni na koma aikin rubuta fassarar Qur'ani da harshen Pashto, kuma wannan shi ne babban abin da na fi so a rayuwata," in ji ta.
Ta bayyana cewa akwai mutane da dama da ke yin rubutun zayyana a Herat, kuma wannan ne ya sanya ta ji sha'awar koyon irin wannan rubutu mai ƙayatarwa.
"Na koyi rubuta Qur'ani da hannu ne shekaru 10 da suka gabata lokacin ina da shekara 15," in ji ta.
Malamina shi ne Mir Wali Ahmad, wani sanannen marubuci a Herat, wanda ya koya mini zayyana."
Duk da cewa mafi yawan makarantu a Herat na amfani ne da manhajar karatu ta Dari, Durrani ta bayar da himma wajen koyon adabin harshen Pashto, inda hakan ya ba ta damar gudanar da aikin fassara Qur'ani zuwa harshen na Pashto.
Harkar rubutun zayyana na da daɗaɗɗen tarihi a garin, tsawon shekara 1000, inda har a wannan zamani ake da mutane da dama wadanda suka ƙware wajen harkar zayyana.
Cibiyar rubutun zayyana ta Herat ta zamo matattarar masu zane-zane, kuma tana taimaka wa masu sha'awar yin irin wannan aiki.
Nagita Durrani, 25, ta yi sa'a ta samu damar yin aikin da ta fi sha'awa a rayuwarta a ƙasar da yara mata da dama ba sa samun irin wannan dama ta cimma burinsu.
An haramta wa yara shiga manyan makarantu da jami'o'i kuma ba su da damar samun ayyukan yi.
Durani ta ce ta yi farin ciki ƙwarai da gaske da ta samu wannan dama, kuma tana fatan sauran yara mata za su samu irin wannan dama.
A yanzu haka tana horar da yara mata sama da 20 kan rubutan zayyana, kuma tana sa ran zuwa wasu larduna na Afghanistan domin koya masu, ta ce "ina fatan hakan zai yiwu."
Ta bayyana cewa ya zuwa yanzu akwai yaran da take koyarwa kan wannan sana'a, kuma akwai da dama daga cikinsu wadanda suka ƙware, har ya kai ga cewa sun halarci wata gasar zayyana a ƙasar Saudiyya.
"Mukan tura waɗannan tukwane da muke yi wa zane zuwa ƙasashe kamar Amurka da Turai ," in ji Durrani.
"Wannan ba sana'a ba ce kawai, wani abu ne daga matan Afghanistan," in ji Durrani.