Hotunan bukukuwan Gasar Kamun Kifin Argungu ta 2026

Bikin Kamun kifi
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Dubban mutane ne suka halarci bukukuwan gasar kamun kifin Argungu ta 2026 da aka shirya a jihar Kebbi.

Gasar Kamun kifin Argungu

Gasar wadda ake yi shekara-shekara an jima ba a yi ba saboda dalilai na tsaro.

bikin gasar kamun kifi

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne babban baƙon da ga buɗe gasar kamun kifin da aka gudanar a yau Asabar.

Tinubu da gwamnan Kebbi
Hannatu Musawa

Ministar al'adu da yawon buɗe idanu, Hannatu Musawa tare da ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu

Gwamnonin Gombe da Jigawa

Gwamonin Gombe da Jigawa na daga cikin gwamnonin ƙasar da dama da suka halarci bikin

gwamnan Sokoto

Gwamnan Sokoto Ahmad Aliyu ne ya ƙaddamar da gasar tseren motoci a lokacin bukukuwan

tseren motoci

Gasar tseren motoci na daga cikin wasannin da ake gudanarwa a lokacin bukukuwan gasar

Manyan saraku

Manyan sarakuna da dama ne suka halarci gasar

Kafin gasar kamun kifin ta yau an shafe tsawon kwanaki ana gudanar da wasanni daban-daban.

wasu na wasa a ruwa

Daga cikin wasannin da aka gudanar har da tseren jakuna da dawaki da kuma raƙuma

mahayin doki

Masunta masu yawa ne suka fafata a gasar kamun kifin da aka gudanar ranar Asabar

Masunta

Dubban asunta ne suka fafata gasar kamun kifin ta bana

mai kifi

Abubakar Usman daga ƙaramar hukumar Maiyama na jihar Kebbi ne ya lashe gasar kamun kfin ta bana

Kifin da ya kama na da nauyin kilogiram 59, kamar yadda alƙalan gasar suka bayyana

Kifin da aka kama ya yi zarra

Ya samu kyautar motoci biyu da kuɗi naira miliyan ɗaya, daga masu shirya gasar.

Bikin Kamun kifi
Bayanan hoto, Wasu daga cikin motocin da aka fafata da su a gasar tseren mota