Yadda aka caccaka wa mutane wuka bayan bikin murnar ɗaukar kofin Arsenal

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

An caka wa mutane shida wuka kuma an kama 24 a lokacin bukukuwan murnar lashe kofin Arsenal a arewacin London, kamar yadda ƴan sandan Metropolitan suka bayyana.

Yawancin waɗanda suka ji rauni a harin da aka kai musu da wuka ba su samu mummunan rauni ba, amma wani matashi mai shekaru a cikin 20, an garzaya da shi asibiti cikin yanayin da ke barazana ga rayuwarsa, bayan an kai masa hari a titin Hornsey Road da misalin ƙarfe 20:30 na daren Lahadi. 'Yan sanda sun ce yanzu yana murmurewa sosai.

Fiye da jami'an ƴansanda 500 ne aka tura domin tabbatar da tsaro a taron, wanda ya jawo daruruwan dubban magoya baya, domin murnar nasarar Arsenal a gasar Premier League.

Ƴansanda sun kuma ce wani jami'in su ya samu raunin yankan wuka a hannu, yayin da wani kuma aka buge shi a kai da abubuwan da aka jefa yayin bukukuwan.

Daga cikin mutum 24 da aka kama, akwai 10 da ake zargi da kai hari ga jami'an ƴan sanda, uku da ake zargi da aikata laifin cin zarafin mata ta hanyar lalata, sannan mutum ɗaya da ake zargi da aikata mummunan rauni ga wani, bayan wani hari da ya haddasa masa rauni a kai.

An bar motocin ƴansanda guda huɗu a titin Theberton, Islington da suka samu matsala da kuma wasu da aka fasa musu fitilu da wunduna.

A ranar Lahadi, Hukumar Kashe Gobara ta London (London Fire Brigade) ta yi gargaɗi ga magoya baya da kada su hau saman rufin gine-gine, bayan jami'anta sun ceto magoya baya 75 da suka makale a wurare masu tsawo.

A yammacin ranar, bayan yawancin jama'a sun koma gida, an samu aukuwar caka wa mutane wuka sau shida su daban-daban, kamar yadda ƴansandan Metropolitan suka bayyana.

An kuma ba jami'an ƴansanda ƙarin ikon tsayar da mutane da yin bincike a cikin daren domin ƙarfafa tsaro.

Kwamanda, Stuart Bell wanda ya jagoranci aikin tabbatar da tsaro na ƴansanda a yayin bikin murnar lashe kofin Premier League da Arsenal ta yi, ya ce:

"Ina so in gode wa mafi yawan dubban magoya bayan Arsenal da suka halarci ranar domin yin murna cikin aminci da kuma cikin ladabi."

"Amma mun riga mun bayyana cewa ba za a lamunci tashin hankali ko wasu laifuka ba, kuma abin takaici an samu wasu wurare da aka yi rashin ɗa'a da kuma wasu lokuta da jami'anmu suka shiga tsakani, ciki har da hare-hare kan abokan aikinmu."

Ya ƙara da cewa: "Yayin da dare ya yi, yawancin jama'a suka koma gida, an sake samun tashin hankali, ciki har da wasu abubuwan da ke da alaƙa da ƙungiyoyin masu aikata laifi."

Ya ce jami'an ƴansanda sun kai ɗauki cikin gaggawa a kowane wurin da aka samu caka wuka, kuma ana ci gaba da bincike.