A cewar majiyoyi da dama da kamfanonin dillancin labarai na Reuters da AFP suka ambata, rundunar sojin gwamnatin tarayyar Habasha tare da dakarun ƙawance sun sake ƙwace iko da filin jirgin Alula Aba Nega da ke Mekelle, babban birnin yankin Tigray a arewacin ƙasar.
Sake ƙwace filin jirgin na zama babban koma baya ga dakarun Tigray, waɗanda suka ƙwace filayen jiragen sama uku a yankin lokacin da rikici ya sake ɓarkewa a ranar 23 ga Satumba. Wannan ne ya tilasta wa kamfanin Ethiopian Airlines dakatar da zirga-zirgar jiragensa zuwa yankin.
Wasu mazauna garin sun shaida wa BBC cewa a ranar 2 ga Oktoba an ga jami'an gwamnatin Tigray da dama suna barin Mekelle, suna ɗora sojoji da kayan aiki a manyan motoci. Sai dai BBC ta ce ba ta iya tabbatar da waɗannan rahotanni da kanta ba.
Shaidu sun kuma bayyana cewa an samu yawaitar sace-sace da wawashe dukiya a cikin dare.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa majiyoyi uku sun tabbatar da karɓe ikon filin jirgin. Daga cikinsu akwai wata majiya da ke da masaniya kan abubuwan da ke faruwa a birnin, wani ma'aikacin agaji, da kuma wani mazaunin Mekelle wanda ya ce ya ji harbe-harbe a wajen tsakiyar birnin.
Mazaunin ya ƙara da cewa wasu mayaƙan rundunar Tigray Defence Force (TDF) suna barin wuraren aikinsu suna komawa gida, yayin da ake ci gaba da wawashe wasu cibiyoyin gwamnati.
Wata majiya da ke kusa da TPLF ta shaida wa Reuters cewa sojojin gwamnatin tarayya da dakarun ƙawancensu sun kewaye birnin Mekelle gaba ɗaya.
A daren Juma'a, ƙungiyar mayaƙan Tigray Peace Forces mai goyon bayan gwamnati ta wallafa a shafinta na X cewa:
"Mun karɓe cikakken iko da Filin Jirgin Alula Aba Nega na Mekelle. A halin yanzu muna ci gaba da share birnin Mekelle."
Haka kuma, kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa mayaƙan Tigray suna ta ficewa daga babban birnin yankin yayin da sojojin da ke goyon bayan gwamnati ke ci gaba da matsowa kusa da birnin.