Dokoki 7 da FIFA ta canza a Gasar Kofin Duniya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 7

Za a hana ƴan wasa a gasar Kofin Duniya ta 2026 zuwa yankin masu horarwa domin tattaunawa da kociyoyi a lokacin da mai tsaron raga ya ji rauni, kamar yadda shugaban alkalan wasa na FIFA, Pierluigi Collina, ya bayyana.

Hukumar Dokokin Kwallon Kafa ta Duniya (IFAB) kuma ta amince da bukatar sauya tsarin VAR, domin ba da damar duba kura-kuran da suka shafi keta.

Wannan tsarin da ake kira "goalkeeper tactical timeout" ya zama abin tattaunawa sosai a ƴan shekarun nan. Ana amfani da shi ne ta hanyar kociyoyi domin ba ƴan wasa sabbin umarni ko kuma ɓata lokacin abokan hamayya.

A watan Nuwamba, kocin Leeds United, Daniel Farke, ya zargi mai tsaron ragar Manchester City, Gianluigi Donnarumma, da yin kamar ya ji rauni domin "karkatar da dokoki" da kuma dakatar da wasa na ɗan lokaci.

A irin wannan yanayi, mai tsaron raga kan zauna a kasa ya nuna alamar neman a duba lafiyarsa, sai sauran ƴan wasa su garzaya wajen koci domin samun wasu umarni. Bayan koci ya gama magana, mai tsaron raga zai tashi ya ci gaba da wasa kamar babu abin da ya faru.

IFAB ta ce ta dade tana nazarin wannan matsala, amma har yanzu ba a amince da sauyin dokar ba.

An kuma bukaci gasannin ƙasashe su gwada wasu hanyoyi daban-daban a lokacin kakar 2026–27 domin gano mafita.

Gasar ƙwallon ƙafa ta mata ta Amurka (NWSL) ta riga ta fara amfani da wata dokar a matakin wucin gadi a bana.

Idan mai tsaron raga ya ji rauni, dole ne ƴan wasa na kowanne bangare su tsaya a inda suke ko kuma su taru a tsakiyar fili.

"Ba daidai ba ne dukkan ƴan wasa su taru wajen koci domin karɓar umarni yayin tamaula".

FIFA za ta yi amfani da irin wannan tsarin da aka fara gwadawa a gasar mata ta NWSL, inda za a hana ƴan wasa zuwa gefen fili, domin yin magana da kociyoyi.

Sai dai wannan mataki ba zai magance matsalar gaba ɗaya ba, domin har yanzu ana iya amfani da wannan dabara domin dakatar da yanayin wasan ko ɓata lokacin abokiyar hamayya.

Collina ya ce dukkan ƙasashe ya kamata su san cewa wannan ba halas ba ne yanzu.

Ya ce: "Mun yi taron horarwa tare da dukkan kociyoyin tawaga 48 da za su buga gasar kofin duniya, kuma mun gaya musu cewa alkalai za su kasance masu tsaurin aiwatar da doka.

"Ba za su bar ƴan wasa su je wajen benci ba lokacin da mai tsaron raga, yana kwance a ƙasa ya ji rauni ba.

"Mai tsaron raga yana da ƴancin ya ji rauni, amma ƴan wasa ba su da ƴancin barin fili su yi amfani da wannan damar a matsayin wani irin hutu ko tuntuɓar kociyoyinsu."

Sai dai ana ganin tasirin wannan doka a gasar Kofin Duniya zai iya kasancewa abin muhawara, domin za a rika yin hutun shan ruwa na mintuna uku a kowane zangon wasan, wanda zai riga ya zama damar tattaunawa ga kociyoyi.

Jami'an wasa ne za su kula da aiwatar da wannan doka, amma Collina ya ce ba za a ba wa ƴan wasa katin gargadi ko wani hukunci ba idan suka yi ƙoƙarin zuwa tattaunawa da koci.

Ya kara da cewa: "Abin mamaki ne cewa a wasu lokuta alkalin wasa da masu duba lafiyar ɗan wasa da mai tsaron raga kawai suke ragewa a cikin fili, sauran ƴan wasa duk sun fita. Wannan ba abu ne mai kyau ba."

Collina: "Ba adalci ba ne a ci ƙwallo daga wani laifin da aka yi".

Collina ya bukaci a sabunta tsarin VAR domin take iya shiga tsakani idan an samu kuskure, kafin a ci gaba da wasan.

An riga an samu wasu misalai, kamar ƙwallon da Ingila ta ci a wasan da suka tashi 1-1 da Uruguay a Wembley a watan Maris.

Cole Palmer ne ya yi bugun kusurwa, amma kafin ya bugo ƙwallon sai Adam Wharton ya tare mai tsaron raga, Jose Maria Gimenez.

Wannan ya ba da damar ƙwallon ta kai ga Harvey Barnes, wanda ya buga ƙwallon a lokacin da Fernando Muslera ke son ya fitar da ita, sai Ben White ya samu ya zura ta a raga.

A baya, tsarin VAR bai ba da damar duba irin wannan laifi da ya faru kafin a yi bugun kusurwa, amma Collina ya nemi IFAB ta amince da wannan canji.

Yanzu IFAB ta amince cewa duk wani laifi da ya faru kafin a fara wasa, idan yana da tasiri kai tsaye, za a iya duba shi a VAR.

Wannan zai shafi bugun fenariti ko hukunci da ya taso daga bugun kusurwa.

Za a fara amfani da wannan mataki a gasar Kofin Duniya, sannan a sake duba dokokin bayan gasar.

Wannan yana nufin cewa a ƙwallon Ingila, VAR za ta iya ba da shawarar a sake bugun tazara, saboda laifin da Wharton ya yi wa Gimenez.

Collina ya ce: "Muna ganin wannan ba adalci ba ne, cewa a ba da ƙwallo alhali an hana mai tsaro raga damar kare kansa."

"Muna da kwarin gwiwa cewa IFAB za ta ba da karin bayani kafin Kofin Duniya cewa VAR na iya shiga tsakani a irin waɗannan batutuwan. Mun yi imanin babu wanda zai ƙi hakan."

Wannan sabuwar doka za ta shafi laifukan da ƴan wasa masu neman cin ƙwallaye ke yi, ba na masu tsaron raga ba kamar rike ko jan riga.

Collina kuma ya bayyana sabuwar doka kan ƴan wasan da ke rufe baki da hannu ko riga yayin tattaunawa da abokin wasa.

Yanzu hakan zai iya kaiwa ga jan kati, kamar yadda wani abin da ya faru tsakanin Gianluca Prestianni na Benfica da Vinícius Júnior na Real Madrid a wasan Champions League.

Prestianni ya samu hukuncin dakatarwa daga wasanni shida daga UEFA saboda halin da aka ɗauka a matsayin na nuna wariya.

Collina ya ce: "Idan tattaunawa ta kasance ta sada zumunci, babu matsala. Amma idan ta zama ta rikici, rufe baki yana nufin kana ɓoye wani abu mai hatsari, kuma hukuncin zai iya zama jan kati."

Ya kuma ce alkalai za su kasance cikin shiri wajen lura da turereniya a cikin yankin fanareti, tare da samun bayanai kan dabarun da ƙungiyoyi ko tawagogi ke amfani da su.

Sabbin sauye-sauyen dokoki a gasar Kofin Duniya

Gasar Kofin Duniya ta wannan bazarar za ta ga yawan sauye-sauyen dokoki, musamman domin rage dabarun ɓata lokaci idan ana wasa.

Collina na fatan waɗannan sauye-sauyen za su sa lokacin ƙarin mintuna (stoppage time) ya ragu idan aka kwatanta da gasar 2022. Sai dai an tabbatar da hutun mintuna uku a kowane zangon wasa, domin shan ruwa (hydration breaks).

Sabbin dokoki:

  • Kirgen seconds na jefa kwallo (5 seconds):

Idan ɗan wasa ya yi ganganci wajen jinkirta fara wasa, za a iya ba da jefa kwallon ga abokan hamayya.

  • Kirgen seconds na bugun goal-kick (5 seconds):

Haka kuma idan aka yi amfani da wannan domin ɓata lokaci, za a iya ba da corner ga abokan hamayya.

  • Lokacin sauya ƴan wasa (10 seconds):

Dole ne wanda aka canja ya bar fili cikin daƙiƙa 10 mafi kusa. Idan ya karya dokar, wanda zai shigo ba zai iya shiga fili ba har sai bayan minti 1, kuma tawagarsa za ta ci gaba da wasa da ƴan ƙwallo 10.

  • Kula da lafiyar ɗan wasa (minti 1):

Dole ne ɗan wasan da ake kula da lafiyarsa ya zauna a waje na daƙiƙa 60. Sai dai akwai keɓantattu, kamar mai tsaron raga, ko rauni mai tsanani, ko idan abokin hamayya ya samu katin gargadi ko aka kore shi.

  • Rufe baki yayin tattaunawa tsakanin ƴan ƙwallo:

Duk ɗan wasan da ya rufe bakinsa yayin wata hatsaniya ko rashin jituwa da abokin wasa zai iya fuskantar hukuncin jan kati kai tsaye (red card).

Sauye-sauyen VAR:

  • Ana iya duba bugun kusurwa:

VAR za ta iya tabbatar da ko an ba da bugun kusurwa daidai ko akasin hakan, amma dole ne a yi hakan da sauri kafin a sake fara wasan. Amma ba ya shafi goal-kick wato bugun falan ɗaya da aka ba da kuskure ba.

  • Za a iya duba katin gargadi na biyu:

Idan ɗan wasa ya tashi zai fita daga fili, saboda katin gargaɗi na biyu, za a iya duba na biyu. Amma ba za a yi nazari kan yiwuwar katin na biyu ba kai tsaye.

Makasudi:

Wadannan sauye-sauyen duk suna da nufin rage ɓata lokaci da kuma yin wasa cikin sauri ko a samu cin ƙwallaye da yin nishadi da tabbatar da yin adalci.