Yadda halin rashin tabbas ya jefa wasu 'yan takarar APC cikin damuwa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

da alam dai har yanzu wasu daga cikin 'ya'yan jam'iyyar APC a Najeriya da suka samu nasara a zaɓukan fidda gwanin da aka yi sun fara bayyana damuwa game da rashin tabbas, da fargaba kan jinkirin da ake yi na basu takardar shaidar tsayawa jam'iyyar takara.

Wannan lamari dai ya ci gaba da jefa jam'iyyar mai mulkin Najeriya cikin kalubale.

An dai kwashe makwanni da jam'iyyar APC ta gudanar da zabukanta na fid da gwani a matakai daban-daban, to amma har yanzu korafe-korafe na bibiyar jam'iyyar kan lamarin.

Mu'awuya Yusuf Muye, da ya tsaya takarar zaben fidda gwani na kujerar majalisar wakilai ta tarayya a mazabar Lafai daAgaye a jihar Neja, karkashin inuwar jam'iyyar ta APC, na daya daga cikin masu nuna wannan damuwa inda ya shaida wa BBC cewa shi damuwarsu ita ce bai wuce ayi musu adalci ba.

Ya ce," Na riga na yi zaben fitar da gwani kuma ni na san ni na samu nasara, to amma an je an yi abin da aka ga dama aka rubuta sakamako."

" Mu 'yan jam'iyya ne, kuma mun yar da da jam'iyyarmu dama shugabanninmu, don haka muna so ayi mana adalci wajen bayar da takardar shaidar tsayawa takarar, a ba wa duk wanda ya samu nasara takardarsa." In ji shi.

A cewar Mu'awuya Yusuf, jinkirin da ake yi wajen tantance ire-iren wadannan korafe-korafen ya fara haifar da kokwanto a zukatan wasu 'yan takarar zabukan fid da gwanin na jam'iyyar APC.

Ya ce," Wasu na ganin idan ba a bayar da takardar nan ba to lokaci zai kure da wasu da aka y iwa ba daidai ba ba za su iya zuwa kotu su kai korafinsu ba."

Anata bangarem uwar jam'iyyar ta APC ta kasa ta ce jinkirin da aka samu na kokarin yi wa kowa adalci ne,

Bala Ibrahim, shi ne daraktan yada labarai na jam'iyyar APCn na kasa, ya shaida wa BBC cewa korafe-korafen da ke gaban jam'iyyar na bukatar lokaci don a gudanar da cikakken bincike kansu:

Ya ce," Wani abu da ake zargin cewa an yi yana bukatar aje a bincika a inda aka ce an yi, sannan aji ta bakin mutanen da suka yi abin, to duk wadannan na daga cikin matakan da ake bi domin tabbatar da an yi abin da ya kamata ace an yi kuma an yi wa kowa adalci."

" Ya kamata mutane su sani komai da ake yi a jam'iyya ana yin sa cikin lokaci da wa'adin da Hukumar zabe ta bayar,kuma har yanzu ba a wuce wannan lokaci ba." In ji Bala Ibrahim.

Duk da irin wannan bayani da kuma tabbaci da jam'iyyar ta APC ke ta bayarwa dai, jinkirin da take yi na nan na haifar da gajen hakuri da zarge-zarge da kuma fargabar kar a karshe jifan da aka yi gabas a ga ya fadi yamma.