Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko za a iya yi wa namiji dashen mazakutar da aka yanke?
Tun bayan bazuwar labarin wata budurwa da aka zarga da yanke gaban saurayinta a farkon makon nan, mutane da dama ke ta yin tambayoyi dangane da yiwuwar sake dasa azzakarin tare da yin aiki kamar yadda ya ke a baya.
A ranar Litinin ne dai rundunar ƴansandan jihar Kano ta ce ta kama matashiyar mai shekara 25 bisa zargin yanke mazakutar saurayinta yayin da yake barci a wani ɗakin otal da suka sauka a Kano.
Matashiyar da ake zargi da aikata wannan aikin dai ta yi amfani da wata wuƙar da ta yi tafiyayyiya da ita tun daga garin Maigatari inda ta kwashe azzakarin nasa bakiɗaya.
Hakan ne ya sa BBC ta nemi bayani daga ƙwararru dangane da yiwuwar yin dashen azzakarin, inda ta tattauna da Dakta Jibrilla Usman Atiku, ƙwararren likitan hanyoyin fitsari da al'aurar maza a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.
Me ya kamata a yi bayan yanke azzakari?
"A wasu lokuta ana iya yi wa mutum dashen azzakari ko kuma a sake haɗa azzakarin da ya yanke, amma hakan ya danganta da irin raunin da ya samu da kuma yadda aka samu kulawar likita cikin sauri," in ji Dakta Jibrilla.
Sai dai kuma likitan ya ce taimakon gaggawa da ya kamata a fara da zarar an samu matsalar yankewar azzakari shi ne alkilta shi domin ka da ya lalace.
"Za a iya yin aiki idan an kai azzakarin cikin lokacin da ake kira da "Golden Hours" ko kuma lokutan farko. Kuma za a iya sanya azzakarin a cikin ƙanƙara bayan wankewa da naɗe shi a cikin leda. Wannan zai iya hana shi ya ruɓe har na tsawon awanni 12 ko 24, kamar dai yadda ake yi wa ƙoda idan za a yi wa wani da ke nesa dashenta."
"Idan dai wannan azzakarin bai jima ba za a iya yin aiki ta hanyar mayar da jijiyoyin jinin yadda ka san ana dashen ƙoda. Ana kiran sa "micro-vascular surgery" Sai dai kuma fa babban aiki ne ba a yi a Najeriya. Ko a turai da Amurka ba a kowace cibiyar lafiya ake yi ba," in ji Dakta Jibrilla.
Ƙwararren ya kuma ƙara da cewa idan waccan hanyar ba ta samu ba to akwai wani zaɓin kuma.
"...Akwai kuma wani azzakarin mai kama da na roba wanda za a saka shi ya maye gurbin aikin kamar dai ƙafar mutum ta yanke ka ga ana saka masa wata. To haka shi ma azzakarin idan ya ɗan gutsire ne akwai saura za a iya buɗe shi a saka masa wani abu mai kama da roba amma ta musamman," in ji Dakta Jibrilla.
Gutsirewar azzakari
Dakta Jibrilla ya ce akwai bambanci tsakanin share azzakari bakiɗayansa da kuma yankewar kansa.
"Shi kan azzakari shi ne wurin da ya fi ko'ina jin taɓi a jikin azzakarin namiji. Idan aka datse shi to shi ma idan aka je asibiti da wuri ana iya ɗan matso da kan domin mutum ya samu wurin jin taɓi domin samun gamsuwa. Gamsuwar za ta ragu ba kamar ta da ba amma kuma zai iya saduwa," in ji Dakta Atiku Jibrilla.
Ko azzakarin zai yi aiki bayan dashe?
Likitan ya ce kamar yadda rauni yake warkewa a hankali shi ma haka zai koma kan aikinsa.
"Zai yi aiki a hankali kafin ya koma amma dai ba zai koma ɗari bisa ɗari ba amma dai zai iya saduwa tare da samun gamsuwa. Da ma ai shi azzakari ayyukansa biyu ne wato fitsari da kuma saduwa da iyali domin samun gamsuwa."
Yankewar ƴaƴan maraina
"Shi ai ƴaƴan maraina a nan ne ake samar da ƙwayayen spermatozoa da ke bai wa namiji damar haihuwa kuma a ciki ƙwayoyin da ke samar da sinadarin ɗanamiji da ake kira testesterone wanda ke samar da sha'awa da wasu ayyukan haihuwa da gemu da murya."
"A nan ne ake samar da kashi 90 inda kuma kashi 10 na zuwa ne daga ƙoda. Saboda haka idan ka ga namiji an datse masa ƴaƴan maraina to matsalar ita ce ba zai haihu ba. Zai iya samun sha'awa har ya yi jima'i ya kuma samu gamsuwa amma gaskiya sha'awar za ta ragu sannan kuma zai iya kasancewa cikin damuwa."
"Saboda shi wannan sinadarin na testestorane da kuke gani shi ne ke sa namji kazar-kazar har ma fara'a. To idan babu zai shiga damuwa ya daina komai har ma ta kai shi ga mutuwa."
Ko mutum zai iya rayuwa ba tare da azzakari ba?
"E mutum zai iya rayuwa mana ai ba zai mutu ba domin ba shi da azzakari. Sai dai kuma ba zai samu kwanciyar hankali ba saboda yadda rayuwar jima'i ta ce ga ɗa namiji. Irin wannan ne ake kira da mutuwa daga tsaye," in ji Dakta Jibrilla Atiku.