Shin an murƙushe ƙungiyoyi irin su al-Shabaab ne, ko kuwa sun sauya salo?

    • Marubuci, Mina al-Lami
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Monitoring
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 8

Shinkafa, taliya, sukari, man girki da wake, ba su ne kayayyakin da ake tsammanin za a gani a farfagandar ƙungiyoyin jihadi ba. Sai dai waɗannan na daga cikin kayan abincin da ƙungiyar al-Shabaab, reshen al-Qaeda a Somaliya, ta ce ta raba wa ɗaruruwan iyalai da ke cikin mawuyacin hali a watan Agusta.

Ƙungiyar ta yaɗa labarin rabon kayan abincin ne ta shafukanta na sada zumunta da gidan rediyonta.

Al-Shabaab, wadda ke iko da manyan yankunan karkara a kudanci da tsakiyar Somaliya, ta ƙara mayar da hankali wajen tallata ayyukan jin ƙai da take cewa tana gudanarwa a shekarar 2026.

"Wannan matar ta ce: Allah ya saka masa da alheri," in ji wata mata daga yankin da ta bayyana a ɗaya daga cikin bidiyon ƙungiyar.

Waɗannan matakai na cikin ƙoƙarin ƙungiyar na samun goyon bayan al'ummar yankin, da kuma nuna kanta a matsayin wadda ba ta tsaya ga ayyukan jihadi kawai ba.

Shekara 25 bayan harin 11 ga Satumba, 2001, da al-Qaeda ta kai wa Amurka, kuma shekaru 12 kenan bayan ƙungiyar IS ta ayyana abin da ta kira halifanci a Iraƙi da Syria, inda salon ayyukan ƙungiyoyin jihadi ya sauya matuƙa.

Maimakon mayar da hankali kan kai hare-hare a ƙasashen Yamma ko kafa daular Musulunci ta duniya, wasu daga cikin ƙungiyoyin, musamman waɗanda ke da alaƙa da al-Qaeda, sun fi mayar da hankali wajen ƙwace iko a ƙasashen da suke aiki. Haka kuma, suna ƙara nuna aniyar yin sassauci domin cimma wannan buri.

Wannan ya haifar da muhawara sosai a tsakanin ƙungiyoyin masu tsauraran ra'ayi na ƙin sassauci, yayin da waɗanda ke da ra'ayin mai sassauci ke ganin haɗa kai da ƙungiyoyin cikin gida, har ma da tsoffin abokan gaba, na iya zama hanyar samun iko.

Sai dai shin wannan na nuna sauyin gaske ne, ko kuwa wata sabuwar dabara ce kawai da suke amfani da ita wajen cimma tsohon burinsu na kafa ƙasa da ke aiwatar da tsattsauran fassarar shari'ar Musulunci, a cikin gida da kuma hulɗarta da sauran ƙasashen duniya?

Manyan ƙalubale

Al-Qaeda da IS ba su cimma babban burinsu na ƙwace ikon ƙasa ɗaya ko fiye da haka, sannan su gudanar da mulki bisa tsattsauran ra'ayin addinin Musulunci ba.

Ƙungiyoyin biyu sun fuskanci manyan koma-baya, an kashe shugabanninsu, sannan sun shafe shekaru suna fuskantar matsin lamba daga ƙasashen duniya. IS, wadda a baya ta taɓa ƙwace manyan yankuna a Iraki da Syria, ta rasa yankin ƙarshe da take iko da shi a shekarar 2019.

Sai dai aƙidar jihadi da ƙungiyoyin da ke yaɗa ta ba su ɓace ba.

A yanzu, nahiyar Afirka ce cibiyar ayyukan ƙungiyoyin jihadi mafi girma a duniya. Ƙungiyoyi masu ƙarfi masu alaƙa da al-Qaeda, irin su JNIM, da ke aiki a yankin Sahel na Mali, Burkina Faso da Nijar, da kuma al-Shabaab ta Somaliya, sun daɗe suna fafatawa da gwamnatocin ƙasashensu.

Ita ma IS, wadda ke da tsananin hamayya da al-Qaeda, tana da rassan da ke kai hare-hare a Najeriya, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, yankin Sahel, Mozambique da Somaliya.

Ɗaya daga cikin mutanen da ke zama abin koyi ga ƙungiyoyin jihadi, har ma suke yi wa kallon wanda suke kwaɗayin irin nasararsa ko sun amince da hakan ko a'a, shi ne sabon shugaban Syria, Ahmed al-Sharaa.

Tsohon mamba a IS, wanda daga baya ya jagoranci al-Qaeda, a baya Amurka ta ayyana shi a matsayin wanda take nema ruwa a jallo. Sai dai ya ƙwace mulki a Syria a watan Disamban 2024, lamarin da ya sa shugabannin ƙasashen Yamma suka tarbe shi.

Ahmed al-Sharaa, wanda a baya aka fi sani da sunan yaƙi Abu Mohamed al-Jawlani, shi ne ya jagoranci ƙungiyar jihadi ta Jabhat al-Nusra, wadda da farko take da alaƙa da IS, daga baya kuma ta koma ƙarƙashin al-Qaeda. Daga bisani ya jagoranci ƙungiyar Hay'at Tahrir al-Sham (HTS).

A hankali ya yanke alaƙarsa da IS da al-Qaeda, tare da nisanta kansa daga kiraye-kirayensu na jihadin duniya.

Maimakon haka, ya mayar da hankali kan Syria, inda ya kafa sansani mai ƙarfi a lardin Idlib da ke arewa maso yammacin ƙasar.

Abin ya ba mutane mamaki ganin yadda a hankali ya fara karkata wajen haɗa kai da ƙungiyoyin da ba na Islama ba, da kuma ƙulla alaƙa da ƙasashen waje.

Yayin da mayaƙan HTS suka doshi Damascus, shugabanninta sun yi ƙoƙarin kwantar da hankalin ƙasashen duniya. Har ma sun tuntubi Rasha, wadda babbar ƙawar gwamnatin Bashar al-Assad ce a lokacin, domin kawar da fargabar cewa za a kafa gwamnatin masu tsattsauran ra'ayin addini.

Wannan salon tafiyar da al'amura cikin sassauci, tare da wasu yanayin siyasar duniya da suka taimaka, ciki har da raunin da Rasha da Iran suka samu, sun taimaka masa wajen ƙwace mulki a Syria.

Sai dai abin da ya fi ba mutane mamaki shi ne yadda shugabannin duniya, ciki har da shugaban Amurka Donald Trump, suka tarbe shi hannu bibbiyu.

Shin wata dabara ce ta cimma babban buri?

Akwai ƙungiyoyi biyu musamman da ya kamata a sanya ido kan ayyukansu: rassan al-Qaeda da ke Mali da Somaliya.

A ƙarshen watan Afrilu, reshen al-Qaeda na yankin Sahel, wanda aka fi sani da JNIM, ya nuna sassauci sosai a fannin siyasa. Ƙungiyar ta haɗa kai da 'yan awaren ƙabilar Tuareg masu kishin ƙasa, waɗanda a wasu lokuta suka taɓa yin faɗa da su, domin ƙaddamar da gagarumin hari da ya yi barazana ga shugabannin mulkin soja na Mali. Har ma ta kira 'yan Tuareg da '''yan'uwa''.

Sai dai ba ƙaruwar ƙarfin sojin JNIM kaɗai ce ke jan hankali ba. Yadda ƙungiyar ke gabatar da kanta ga al'umma ma na da muhimmanci.

A baya, farfagandarta ta fi mayar da hankali kan shugabannin al-Qaeda, taken ƙungiyar da kiraye-kirayen jihadin duniya.

Amma tun daga ƙarshen shekarar 2024, hotunan ƙungiyar ba su ƙara nuna alamomi da tambarin al-Qaeda da aka saba gani ba.

Haka kuma, maimakon magana kan matsalolin Musulmi a faɗin duniya, JNIM na ƙara mayar da hankali kan matsalolin cikin gida.

Ƙungiyar na gabatar da kanta a matsayin mai kare talakawa daga shugabanni masu cin hanci da danniya.

A lokuta da dama, ta zargi gwamnatin mulkin soja ta Mali da ƙawayenta na Rasha da kashe fararen hula da kuma ƙara tsananta rayuwarsu.

A watan Afrilu, ta yi kira ga ''dukkan masu kishin ƙasa masu aminci'' da su shiga aikin gina ''sabuwar Mali'', tare da yin alƙawarin samar da tsaro, adalci da wadata, baya ga aiwatar da shari'ar Musulunci.

Har ma ta nuna yiwuwar kulla ''dangantaka mai kyau da daidaito'' da Rasha, duk da cewa tana yaƙi da dakarun Rasha da ke taimaka wa gwamnatin Mali. Wannan furuci ya yi kama da kalaman HTS ga Rasha a lokacin da take dosar Damascus.

Akwai kamanceceniya tsakanin salon da JNIM ke bi da yadda Ahmed al-Sharaa ya gudanar da al'amuransa a Syria. Hakan ya haɗa da kulla ƙawance da ƙungiyoyin cikin gida, kwantar da hankalin waɗanda ka iya zama abokan gaba, da kuma kauce wa matakan da za su bai wa ƙasashen waje hujjar tsoma baki.

Taliban da shari'ar Musulunci

A cewar Wassim Nasr, ɗan jarida a gidan talabijin na France 24 kuma masani kan ƙungiyoyin jihadi, ana ci gaba da muhawara a cikin shugabancin JNIM kan salon da ya kamata ƙungiyar ta bi.

Ya ce wani ɓangare na shugabannin ƙungiyar na goyon bayan salon Taliban, wato ƙwace mulki da ƙarfin soja tare da yin sassauci kaɗan.

Sai dai ɗayan ɓangaren, wanda a cewarsa yanzu ya fi na farko ƙarfi, ya fi son salon ƙungiyar HTS ta Syria, na yin sassauci da kulla manyan ƙawance domin ƙwace mulki cikin sauri.

Nasr na ganin JNIM za ta iya koyon darussa daga waɗannan salo biyu, amma sauyin da take samu a fannin siyasa na iya kai ta ga yanke alaƙarta da al-Qaeda.

Kamar JNIM, ita ma al-Shabaab ta Somaliya na nuna aniyar yin yarjejeniya da tsohuwar abokiyar hamayyarta.

A cewar Abdullahi Guji, masani kan Somaliya a sashen BBC Monitoring, al-Shabaab ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da wata ƙabila mai ƙarfi a Somaliya da ake kira Macawisley a watan Oktoba.

Tun da farko, mayaƙan wannan ƙabila ne ke sahun gaba wajen yaƙi da ƙungiyar.

Guji ya ce tun daga lokacin ƙabilar ta janye dakarunta daga fagen daga, lamarin da ya zama babban koma-baya ga ƙoƙarin gwamnatin Somaliya na yaƙi da ƙungiyoyin jihadi.

Akwai kuma wani dalili da zai sa wasu ƙungiyoyin jihadi ganin damar faɗaɗa ikonsu: suna ganin cewa a halin yanzu gwamnatocin ƙasashen Yamma sun shagaltu da wasu batutuwa da suke ganin sun fi gaggawa.

Darussan da aka koya daga tarihi

Ba kamar babbar abokiyar hamayyarta IS ba, wadda ba ta taɓa yin sassauci ba, al-Qaeda ta daɗe tana nuna sassauci wajen neman cimma manufofinta. Sai dai tarihi na ɗauke da wani darasi da ya kamata a kula da shi.

Zanga-zangar juyin juya halin Larabawa ta shekarar 2011, wadda ta raunana tasirin al-Qaeda sosai, ta sa wasu ƙungiyoyin jihadi masu alaƙa da ita a Yemen, Libya da Tunisia suka fara amfani da sunan Ansar al-Sharia (Masu goyon bayan Shari'a).

Manufar hakan ita ce samun goyon bayan al'ummar yankunan da suke aiki, ba tare da amfani da sunan al-Qaeda ba.

A shekarar 2012, shugabannin al-Qaeda a Mali sun shawarci ƙungiyoyin jihadi da suka ƙwace ikon arewacin ƙasar tare da taimakon 'yan awaren Tuareg da kada su yi gaggawar aiwatar da tsauraran dokokin Musulunci.

Maimakon haka, sun bukace su da su yi aiki tare da ƙawayensu na cikin gida, su guji matakan da za su nisanta su daga al'umma, sannan su rage nuna alaƙarsu da al-Qaeda.

Saƙon da suke son isarwa ba shi ne su yi watsi da burinsu ba, sai dai su yi haƙuri da dabarun siyasa, su jira lokacin da ya dace. Wataƙila irin wannan tunani ne ake amfani da shi a yanzu.

To, shin waɗannan ƙungiyoyi da gaske sun sauya manufofinsu ne, ko kuwa dabarunsu kawai suka sauya? Ko da waɗanda ke kira da a riƙa yin sassauci, ba lallai ne sun yi watsi da burinsu na kafa ƙasa da za ta aiwatar da tsattsauran fassarar shari'ar Musulunci ba.

Colin Clarke na mamakin ko wannan sabon salon sassauci wata dabara ce ta ''dokin Trojans'', wadda za ta ba ƙungiyoyin jihadi damar ƙwace mulki ba tare da sun yi watsi da manyan manufofinsu na dogon lokaci ba.

''Babbar tambayar ita ce, idan waɗannan ƙungiyoyi suka ƙwace mulki, shin za su sauya matsayinsu da gaske, ko kuwa kawai za su sauya dabarunsu ne domin su tsira da kuma ƙarfafa ikonsu?'' in ji shi.

Sai dai ba dukkan ƙungiyoyin ne ke sauya dabarunsu ba.

IS na nan daram kan burinta na jihadin duniya, kuma tana ci gaba da ƙin yin sassauci. Haka kuma, reshen al-Qaeda na Yemen, wanda aka fi sani da AQAP, na ci gaba da kira da a kai hare-hare kan Amurka da Isra'ila, tare da ƙarfafa kai hare-haren da mutum ɗaya zai iya gudanarwa kan ƙasashen Yamma da wuraren da Yahudawa ke da alaƙa da su.

Haka kuma, lokaci bai yi ba da za a iya sanin ko ƙungiyoyi irin su JNIM da al-Shabaab za su bi sahun Taliban ko Syria, ko kuma za su amince su yi sassauci.

Wasu ƙungiyoyin jihadi na iya mayar da hankali kan siyasar cikin gida idan suka fuskanci ƙalubalen gudanar da yankunan da suka ƙwace. Wasu kuma na iya ɓoye manyan manufofinsu har sai sun sami isasshen ƙarfin da za su aiwatar da su.

Burinsu na jihadin duniya na iya kasancewa bai yi nasara ba, amma har yanzu gwagwarmayar ƙungiyoyin jihadi ba ta ƙare ba.