Amnesty ta ce a binciki harin da aka kai wa ƴar Kwankwasiyya a Kano
Ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Amnesty International ta yi kira ga hukumomi da su gaggauta yin bincike kan harin da aka kai wa Maryam Golden, wata ƴar Kwankwasiyya a jihar Kano da ke goyon bayan jam’iyyar adawa ta NDC.
Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a shafinta na Facebook ranar Laraba, ta yi Alla-wadai da harin da aka kai wa Maryam wanda ake zargin wasu ’yan daba da aikatawa.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na daren Talata 24 ga Nuwamba, a unguwar Rimin Kebe da ke Kano.
Bidiyon harin wanda ya bazu a kafofin sada zumunta, ya nuna Maryam ɗauke da munanan sara daga adda, inda jini ke zuba a jikinta.
Amnesty ta ce munanan raunukan da ta samu za su bar mata taɓo na tsawon rayuwa.
Waɗanda suka kai mata harin sun gargaɗe ta da ta daina sukar gwamnatin jihar Kano, a cewar Amnesty.
Ƙungiyar ta ce iyalanta sun alaƙanta harin da siyasa da kuma yadda take sukar gwamnati.
“Bai kamata a rasa rai ko a fuskanci tashin hankali saboda shiga harkokin siyasa cikin lumana ko sukar gwamnati ba,'' in ji Amnesty.
Amnesty ta ƙara da cewa wannan hari da makamantansa sun nuna yadda hukumomin Najeriya suka gaza dakatar da hare-haren da ake kai wa ’yan siyasar adawa da masu alaka da su.