Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Da me Amurka ke amfana da tallafin tsaron da take bai wa Najeriya?
Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce Amurka na taimaka wa sojojin ƙasar wajen bibiyar shugabannin ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da kuma daƙile hanyoyin sadarwarsu ta hanyar musayar bayanan sirri na lokaci-lokaci da hotunan tauraron ɗan'adam da kuma horas da jami'an soji.
Jaridar Guardian ta ambato ministan na cewa tallafin ya ƙara wa sojojin Najeriya ƙarfi wajen gano wuraren da ake son kai hare-hare, inda sojoji ke gudanar da ayyuka kusan kullum bisa ingantattun bayanan sirri.
Musa ya ƙara da cewa hare-haren sun yi sanadin kashe wasu shugabannin ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da kuma ƴan bindiga a arewa maso yamma da arewa maso gabashin Najeriya.
Ya ce kuma Najeriya na sa ido kan yadda masu tayar da ƙayar baya ke amfani da tsarin sadarwar tauraron ɗan'adam na Starlink, da kuɗaɗen intanet (cryptocurrencies), da kuma jiragen sama marasa matuƙa tare da haɗin gwiwa da Amurka wajen katse hanyoyin da suke samun kuɗaɗen gudanar da ayyukansu.
Ministan ya ce ƙasar na sa ran samun ƙarin jirage masu saukar ungulu daga Amurka da Italiya domin ƙarfafa ƙarfin gudanar da ayyukan soji.
Ya ce Najeriya ta kuma cimma yarjejeniya da Kamaru, Jamhuriyar Nijar da Chadi wadda ke bai wa sojoji damar bin sawun masu tayar da ƙayar baya da 'yan bindiga har zuwa kilomita biyar a cikin yankunan kan iyaka na ƙasashen, domin ci gaba da gudanar da samamen tsaro.
Wane taimakon tsaro Amurka ke bai wa Najeriya?
Dokta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security mai nazarin harkokin tsaro a yankin Sahel ya ce taimakon da Najeriya ke sama daga Amurka na da yawa.
''Na farko a kwai batun bayanan sirri, wanda Amurka ke bai wa jami'an tsaron Najeriya waɗanda ke amfani da su wajen samun nasara a ayyukanta'', in ji.
Masanin tsaron ya kuma bayyana horas da dakarun Najeriya a cikin nau'ikan tallafin tsaron da Amurkan ke bai wa Najeriya.
A farkon shekarar nan ne dai Amurka ta sanar da tura dakarunta kusana 200 zuwa Najeriya domin horas da sojojin Najeriya dabarun yaƙi, kodayake a watannin baya Amurka ta sanar da komawarsu gida.
Dokta Kabiru Adamu ya kuma ce akwai tallafin makamai da Amurka ke sayar wa Najeriya, a wasu lokutan ma kyauta take bai wa Najeriya, a cikin tallafin tsaron.
Waɗanne nasarori taimakon ya cimma?
Dokta Kabiru Adamu ya ce an samu nasarori masu yawa sakamakon tallafin tsaron da Najeriya ke samu daga Amurka.
''Taimakon ya kai ga kashe manya-manyan shugabannin ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi aƙalla huɗu, da kuma manyan kacalla-kacalla da ke addabar yankin arewa maso yammacin Najeriya'', in ji shi.
Sai dai masanin tsaron ya ce har yanzu akwai matsalolin da ke addabar mutanen yankunan da ke fama da matsalar tsaron, musamman a arewa maso gabas da maso yamma.
''Misali rashin zuwa gona ko kasuwa ko tafiya a manyan hanyoyi, har yanzu akwai waɗannan matsaloli'', in ji shi.
Me ya sa Amurka ba ta bayar da taimakon murƙushe ƴan fashin daji?
Wasu na ganin cewa Amurka ta fi mayar da hankali kan ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi da ɗaukar matakan kawar da su, fiye da ƙungiyoyin ƴanbindiga a yankin arewa maso yammacin ƙasar.
Wani abu da Kabiru Adamu ya ce na faruwa ne sakamakon muradin Amurka.
''Ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi ne suka fi damunta, idan ba za ka manta ba tun garin ranar 11 ga watan Satumba, Amurka ta ƙudiri aniyar kawar da ayyukan masu iƙirarin jihadi a duniya'', in ji shi.
To amma Dokta Kabiru Adamu ya ce a baya-bayan nan sakamakon zargin kisan Kiristoci a Najeriya da ake yi wa wasu ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, ya sa Amurka ta fara karkata kan ƴanbindigar.
Me Amurka ke amfana daga ƙawancen tsaro da Najeriya?
A duk lokacin da aka yi maganar ƙawancen tsaron Amurka da Najeriya, ƴanƙasar da dama na tambayar me Amurka ke amfana da ƙawancen.
Dokta Kabiru Adamu ya ce akwai abubuwa guda uku da Amurkan ta fitar a matsayin manyan manufofint na tsaro a Afirka.
''Na farko shi ne tattalin arzikinta, na biyu kare Kirista, wannan kam ba ta ɓoye ba, sai kuma na uku inganta ƙarfin sojojin ƙasashen Afirka'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa idan aka lura da wannan, to dole a alaƙanta batun da tattalin arziki.
''Batun ma'adinai da take nema don inganta masana'antunta da kuma batun gasar samun ma'adinan da take yi tsakaninta da China'', in ji shi.
Ya kuma ce akwai kuma muradinta na ƙarfafaf zaman lafiyar ƙasashen duniya da yawa, domin kare al'ummar Kirista da ya ce tana iƙirarin yi.