Strasbourg ta dauki Vitor Matos sabon kociyanta, Strasbourg
Strasbourg ta sanar da naɗin kociyan Swansea City, Vitor Matos a matsayin sabon wanda zai horar da ƙungiyar.
Ƙungiyar da ke buga babbar gasar tamaula ta Faransa ta sanar da hakan a daren Laraba, amma har yanzu babu wata sanarwa daga Swansea game da ficewar Matos.
Ana sa ran Strasbourg za ta biya Swansea diyya da ake ganin zai kai kusan fam miliyan biyar domin samun damar ɗaukar kocin.
Matos, mai shekara 38, ya shafe ƙasa da shekara guda a Swansea bayan ya bar aikin horar da Maritimo, domin maye gurbin Alan Sheehan a matsayin babban kocin ƙungiyar da ke buga gasar Championship a watan Nuwamban 2025.
Ana kuma sa ran mambobi huɗu na tawagar masu horar da ke aiki da Matos, wato Diogo Medeiros, Toze Mendes, Goncalo Ricca da mai horar da masu tsaron gida, Pedro Pereira, za su bar Swansea.