Real Madrid na son Calafiori, Man United ta dage kan Hall

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid na ci gaba da nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan bayan Italiya, Riccardo Calafiori, amma Arsenal ta bayyana ƙarara cewa sai an gabatar da tayi mai matuƙar tsoka kafin ta yi tunanin sayar da ɗan wasan mai shekara 24. (CaughtOffside)
Manchester United na shirin yin garambawul mai zurfi a ɗangaren tsaron bayan ƙungiyar a lokacin bazara mai zuwa, inda za su sake duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Newcastle da tawagar Ingila, Lewis Hall, mai shekara 22, wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan baya na gefen hagu kuma yake da sha'awar komawa Old Trafford.
Haka kuma, ƙungiyar na zawarcin dan wasan baya na Bournemouth da tawagar Faransa, Adrien Truffert, mai shekara 24. (i news)
Liverpool da Arsenal duk suna sha'awar ɗan wasan baya na ƙasar Spain, Xavi Espart, amma Barcelona za ta ƙi amincewa da duk wani tayin da aka yi mata kan ɗan wasan mai shekara 19, wanda kwantiraginsa ta ƙushe da sharaɗin sallama da ya haura fam miliyan 84. (Teamtalk)
Newcastle na da burin ɗaukar ɗan wasan baya na AC Milan kuma ɗan ƙasar Ingila, Fikayo Tomori, a lokacin da kwangilarsa za ta ƙare a lokacin bazara, inda zai sa ya zama ɗan wasa mai cin gashin kansa. (Football Insider)
Arsenal na shirin ɗaukar ɗan wasan gaba na Club Brugge, Nicolo Tresoldi, mai shekara 22, a watan Janairu; inda aka yi ƙiyasin darajar ɗan wasan na ƙasar Jamus kan fam miliyan 42. (Sun)
Ɗan wasan tsakiya na Argentina, Emiliano Buendia, na shirin sanya hannu kan sabuwar kwangila a Aston Villa, yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar ɗaukar ɗan ƙasar Sweden, Victor Lindelof, mai shekara 32, da kuma dan Ingila mai shekara 19, George Hemmings. (Athletic)
Manchester United na ci gaba da sa ido kan halin da ɗan wasan gefe na Crystal Palace, Ismaila Sarr, mai shekaru 28 ke ciki, yayin da Galatasaray ita ma ke nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan na Senegal. (Teamtalk)
Ɗan wasan baya na Tottenham kuma da ƙasar Spain, Pedro Porro, mai shekara 27, zai "yi nazari sosai" kan damar komawa Barcelona ko kuma Real Madrid. (Football Insider)
Ɗan wasan baya na Argentina, Lisandro Martinez, mai shekara 28, na shirin barin Manchester United a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Mail)


























